Yadda Ake Neman Aure A Musulunci

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Aslm alykm akaramakallahu may Allah reward with beautill abide in jannatul firdausi i love you for the sake of Allah for the sake of the goodness your here doing for only Allah's sake insha Allah i have good thought for akan kanayine dan Allah dan nidai ban taɓa baka ko da sisi kwabo ba, baka sanniba amma akoda yaushe kana kokarin karba tamboyoyine kuma in time duk da yawan aikin dake gareka agabanka thanks alot my habibi😍😍

    Tambayace dani dan Allah a musulunci bisa ga tsari na sunnah ya ya kamata mutum yaje neman aurin mace? afasheman komai ta yanda abin zai zama gwanin banshawa ta kuwacce fuska🤦‍♂️🤦‍♂️ jaxakallah bil khairi

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Na'am. Da farko dai Bayan ka ga Macen da kake so. Wajibi Ne Ka tsaya kare mata kallo yadda ya Kamata. Tin daga Sama Har Kasa. Har sai Zuciyarka ta Tabbatar Maka da Cewar wannan Matar ta yi Maka Ɗari Bisa Ɗari. Ma'ana ta kwanta Maka a Ranka. Sabida idan tana da wani Aibu wanda kai Baiyi maka ba. Daga baya idan zama ya yi zama. Zaka ji ta Fita a Ranka.

    Daga nan Kuma Zaka Nemi Adreshinta da na Iyayenta. Sabida ana duba cewar su Wanene Iyayen Wannan Yarinyar. Mutanen Kirki ne ko na Banza? Suna da Magana ɗaya ko kuma basu da Magana ɗaya? Sun san ya Kamata ko basu san ya Kamata ba? Suna ganin Girman Mutane ko kuma Masu Rena Mutane Ne?

    Idan ka tabbatar da babu Matsala daga wajen Iyayenta, Sai ka sami Waɗanda take tare da su a Unguwarsu, waɗanda suka Santa, Ma'ana Waɗanda Suka yi Mata Farin sani. Ba Waɗanda sai an Kwatanta Musu Ita ba. Waɗanda da kace Wance, to sun Santa. Kuma Wajibi ne waɗannan Mutanen su Zama Adalai. Ba Waɗanda ba sa Kaunar ganinta a doron kasa ba. Domin a Kowacce Society Akwai Irin Waɗannan Mutanen. Sai ka yi Bincike su halayenta da na Iyayenta da na gidansu. Ba tare da ta sani ba.

    Daga Lokacin da ka Tabbatar da Cewar babu wata matsala da zata hanaka Aurenta. Ko kuma ko da da wata Matsala a Tattare da ita. Kai ba zata Zame Maka Matsala ba. Sai ka yi kokari ka Tura Magabatanka gidansu. Wajen Iyayenta kenan. Da Niyyar za su Nema maka Izinin Mahaifinta, a Baka Dama ka je wajenta ku Tattauna. Kaga kenan idan Anyi Mata Miji ma. Iyayenta za su Gayawa Magabatanka cewar wani ya Rigayeka. Idan har Hakan ta Kasance sai ka yi mata Addu'a. Sai ka jira Wadda Allah ya Kaddara cewar ita ce Matarka. Domin wani baya Auren Matar Wani.

    Idan kuma ba a yi Mata Miji ba. Ba Mamaki idan iyayenta Masu Zurfin Tunani ne. Za su Nemi ka Basu Lokaci, za su Yimaka Magana. Sabida a Daidai wannan Lokacin ne Kaima za suyi Bincike Akan halayenka da Dabi'unka. Idan Sun tabbatar da cewar Akwai Matsala, Za su zo Maka da wata Magana. Saɓanin Abinda kake Tunani. Idan kuma babu wata Matsala. Ma'ana idan har ka chanchanta a Baka Aure. Za su Baka Izini kazo har gidansu ka sameta ku Tattauna. Idan ka ga babu wata Matsala Shikenan. Sai ka sake Samun dama ta biyu ka tura magabantaka. Su Nema maka Aurenta. Ma'ana Su Baka Ranar Aure. Sabida ba a son yawan zuwan hira nan. Ana son Haduwarka da wadda Zaka aura ya zamana bata Wuce haduwa Ukku ba.

    Zuwa na farko, da ka je Kuka ga juna ka Gabatar da Kanka da kuma Kudurinka na Aure A kanta. Na biyu shi ne ZaKa je ku Tattauna Akan yadda Bikinku zai Kasance. Na Ukku shi ne. Zuwanka Kofar Gidansu Wajen Daurin Aurenka da Ita. Daga Nan Kuma za a kawo Maka Matarka.

    Sabida Doguwar Soyayya tana kawo Reni da yawan Saɓani a Tsakanin Masoya. Sabida Mata Suna Samun Damar Sauraron wani Namijin bayan Kuma an sanya Mata Ranar Aure da wani. Ko kuma ka je ba ka sameta ba. Ko ka kira wayarta bata Kusa da wayar. Sai kaga nan da nan an sami matsala. Ko kuma Wasu Matsalolin na daban. Kaga Kenan ana yawan Fada. Ko kuma ita tana Ganin Kamar Zaka Tauye Mata Wani Hakki nata. A haka sai kuna yawan Samun Saɓani. Kafin a Kaita Gidanka ta Rena ka.

    Sabida Haka Idan har Baku Dauki Doguwsr Soyayya ba. za a kawo Maka Matarka, kana jin Kunyar ta, tana jin Kunyar ka. Kana ganin Girmanta, Itama tana ganin Girmanka. Sabida haka kenan Anan ne zakuyi Rayuwar Aure mai tsafta. Kowa yana ganin Mahimmancin kowa.

    Allah Shi ne Masani.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.