Wannan bincike mai taken "Yanayin Tsaro A Garin Gusau" ya zo da babuka biyar. A babi na ɗaya an yi gabatarwa ne a cikin wannan bincike da manufar bincike da hasashen bincike da farfajiyar bincike tare da kawo matsalolin da aka fuskanta a wannan bincike da muhimmancin da kuma hanyoyin da aka bi wajan gudanar da wannan bincike daga ƙarshe aka zo da naɗewa. Babi na biyu kuwa yana ƙunshe da bitar ayyukan da suka gabata da hujjar cigaba da bincike daga ƙarshe aka zo da naɗewa. A bani NA uku an kawo fashin baƙi a kan ma'anonin kalmomin da suka haɗu suka gina taken bincike waɗanda suka haɗa da ma'anar yanayi da ma'anar tsaro da ire-iren tsaro da ma'anar gari da kuma ma'anar kalmar Gusau daga ƙarshe aka zo da naɗewa. A cikin babi na huɗu kuwa an zo da bayanai a kan gundarin taken bincike, a inda aka kawo bayani game da yanayin Tsaro na gargajiya da tsokaci a kan ganuwar Gusau da ƙofofinta da kuma makaman da ake amfani da su na gargajiya da yanayin tsaro na zamani da irin kayan da ake amfani da su domin, kula da da yanayin tsaro na Gusau da bayani a kan su wa ye 'yanta'adda da ire-iren 'yanta'adda da ayyukan 'yanta'adda an zo da bayani a kan abubuwan da ke haifar da ta'addanci da kalmomin 'yanta'adda da illoli da ayyukan ta'addanci ya haifar a garin Gusau da matsalolin da tsaro yake fuskanta wajen al'umma da jami'an tsaro da rawa da jama'a da hukuma ke takawa wajen kawar da ayyukan ta'addanci daga ƙarshe wannan babi ya zo da muhimmancin tsaro a garin Gusau da naɗewa. Babi na biyar ya ƙunshi sakamakon bincike da ta'arifin wasu kalmomi daga ƙarshe aka zo da da shawarwari da naɗewa. Wannan bincike ya ta'allaƙa ne a kan yadda aka gudanar da "Yanayin Tsaro A Cikin Garin Gusau.
Yana
Yin Tsaro A Garin Gusau
NA
MAHADI
MUSTAPHA
SADAUKARWA
Na
sadaukar da wannan aiki mai taken “Yanayin tsaro a garin Gusau” ga
Mahaifana, MalamAlmustapha
Abdullahi Ajiya Sallau da Mahaifiyata, Hajiya
Zara'u Muhammad Nalado, da
Malama Lauratu Usman, waɗanda suka haife ni,
sannan suka ba ni tarbiyya da
cikakkiyar kulawa domin ganin na zama mutumin ƙwarai dangane da
harkokin rayuwata a kodayaushe.
Haka
kuma, na sadaukar da shi ga dukkan malamaina, na makarantar Firamare da Sakandare da Difiloma da kumaJami’a.
GODIYA
Ina mai godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki Mai kowa Mai komai Mai rahama Mai
jin ƙai zuwa ga bayinSa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad
(S.A.W.) da sahabbansa da zuri’arsa da dukkan waɗanda suka bi shi har zuwa
ranar sakamako.
Bayan haka, ina miƙa godiyata da jinjina zuwa ga mahaifina Malam
Almustapha Abdullahi Ajiya Sallau, bisa irin
jajircewar da ya yi na ganin cewa na samu ilimin addini da kuma na zamani a
rayuwata. Kuma ina ƙara gode masa a kan irin addu’o’in da yakan yi mani dare da
rana. Ina mai addu’ar Allah (SWT), ya saka masa da mafificiyar aljanna (maɗaukakiya), amin. Haka kuma, ina mai
miƙa godiya da jinjina zuwa ga mahaifiyata dangane da irin namijin ƙoƙarin da
takan nuna a kaina na ganin cigaban rayuwata har zuwa ranar da rai zai yi
halinsa.
Haka kuma, ina miƙa godiya da jinjina ga Malamina, wanda kuma shi ne ya
duba wannan aiki nawa, watau Dr. Rabi'u Adamu Bakura, bisa jajircewa da ƙoƙarin ganin ya ɗora ni a kan hanya don samun nasarar
kammaluwar wannan aiki nawa. Godiya ta musamman ga Dr. Bakura, Allah Ya biya shi kuma Ya saka masa da Aljanna a ranar gobe ƙiyama, amin.
Bugu da ƙari, ina farin cikin miƙa godiyata ta musamman ga Malamaina waɗanda
suka yi mini riƙo na amana da mutuntawa tare da ba ni shawarwari a kan harkokin
karatuna domin ganin na samu nasara. Waɗannan malamai sun haɗa da: Farfesa A.M. Bunza, Farfesa M. Tsoho Yakawada,
Farfesa Aliyu Musa, Farfesa Balarabe A., Farfesa M. L. Amin, Dr. Malumfashi, Dr. R.M. Tahir, Dr. Nazir I. Abbas, Dr. Musa
Fadama, Malam Isa S. Fada, Malam Musa Zaria, Malam Aliyu Rabi’u Ɗangulbi, Malama Halima Kurawa, Malam Abu-Ubaida Sani, Malam M. Arabi da
sauransu. Ina roƙon Allah ya saka masu
da mafificin alkhairi, amin.
Har ila yau, ina miƙa godiyata ta musamman zuwa ga yayyena da ƙannena da
kuma abokaina, bisa ga irin gudummuwar da sukan ba ni da kuma addu’o’in da
sukan yi mani, kamar su; yaya Anas Almustapha Ajiya, Abdul'aziz
Almustapha Ajiya, Anty Hafsat Almustapha Ajiya, Anty
Nafisa Almustapha, Anty Kafiya Almustapha Ajiya, Anty Samira
Almustapha Ajiya, da ma waɗanda
ban samu damar ambaton sunayensu ba, kuma da fatan za su yi haƙuri da ni.
Sannan kuma, ina miƙa godiya zuwa ga ƙannena da abokan karatuna kamar su; Saddam Almustapha Ajiya, Gaddafi Almustapha
Ajiya, Ibrahim Almustapha Ajiya Usama Almustapha Ajiya, Aliyu Almustapha Ajiya,
Abbas Muhammad Hussaini, Sadam Yusuf, Ibrahim Garba Total, Amir Tijjani, Umar Muhammad, Yusuf
Muhammad Kwalli, Abdulrashi Bala, Abdulrashid Isma'il, Makiyu Balarabe, Jamilu
Officer, Munnir Sani Mai Fulla, Abdulmalik Mai Biredi da sauransu. Haka kuma, ina mai godiya ga abokan zamana Yahaya
Sani Deemama, Yasir Sani Moyi, Aminu Aliyu Ɗanmaituwo, Zaidu Tukur Sarkin Rafi
Mubarak Hamisu Pepe, Bilyaminu Rabi'u Buzu, da sauransu. Allah ya saka masu
da alkhairi kuma Allah ya albarkaci karatu, amin.
BABI NA ƊAYA
1.0 GABATARWA
A
cikin wannan bincike za mu yi nazari ne
a kan yanayin tsaro da ma'anar tsaro a garin Gusau da kuma rabe-raben tsaro, da
irin rawar da jami'an tsaro da al'umma suke takawa a kan sha'anin tsaro. Haka
kuma wannan bincike zai yi ƙoƙarin kawo ma'anar ta'addanci, da kuma illoli da
matakan kawar da su a garin Gusau.
A
cikin wannan bincike za a yi nazari ne a kan yanayin tsaro a cikin garin garin
Gusau.
Haka
kuma za a tsara wannan aiki a kan babi-babi, a babi na ɗaya za a yi bayani a
kan manufar bincike da, hasashen bincike da, farfajiyar bincike da matsalolin
bincike da, muhimmancin bincike da, hanyoyin gudanar da bincike, daga ƙarshe
kuma ya zo da naɗewa.
1.1
MANUFAR BINCIKE
Duk
wani abin da ɗan Adam ya ƙuduri ya aiwatar a rayuwarsa, za a tarar cewa,
lallai, akwai wata manufa ta musamman da ta wajabta masa aiwatar da wannan abu.
Masu iya magana kan ce 'kowane allazi da nasa amanu, idan muka lura da wannan
zance za mu fahimci cewa babu wani bincike da za a aiwatar ba tare da manufar gudanar
da shi ba. Don haka manufofin gudanar da wannan bincike shi ne domin samun
takardar shaidar kammala karatun digirin farko. Haka kuma fito da yadda yanayin
tsaro yake a garin Gusau, tare da nuna muhimmancin tsaro musamman a wajen
al'umma da kuma wanzar da zaman lafiya a cikin al'ummar garin Gusau, domin su
fahimci muhimmancin tsaro, tare da gano irin hikima da fasaha da dabaru da ke
ƙunshe a cikin lamurran tsaro.
1.2
HASASHEN BINCIKE
Hasashen
da ake yi a cikin wannan bincike sun haɗa da:
1.
Tsaro na ɗaya daga cikin abubuwa mafi muhimmanci ga rayuwar al'umma.
2.
Tsaro na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatuwar samun zaman lafiya mai ɗorewa a
tsakanin al'umma.
1.3
FARFAJIYAR BINCIKE
Kafin
a shiga bayanin farfajiyar bincike, yana daga cikin ƙa'ida ta bincike, ɗalibin
bincike ya yi nazari a kan abin da yake kusa da shi, wato muhalli ko farfajiyar
da yake zaune, domin samun ingantattun bayanai game da abin da yake bincike.
Bari
mu ga ma'anar farfajiyar bincike da muhalli:
Wikepedia
(2019) an bayyana muhallin bincike da cewa, shi ne wuri na musamman wanda aka
gudanar da bincike a kan wani abu da ke da mazauni a wurin, kamar al'umma,
abubuwa da sauransu, ta hanyar littattafai, da mukalu, da kuma tarukan kara wa
juna sani, domin samun wani sakamako.
Wannan
bincike an gudanar da shi ne a garin Gusau babban birnin jihar Zamfara, za a yi
nazari a kan yanayin tsaro a cikin garin Gusau, inda za a gana da jami'an
tsaron domin jin yadda suke gudanar da aikin su.
1.4
MATSALOLIN BINCIKE
Kamar
kowane irin al'amari na rayuwa, a kan iya haɗuwa da wata mastala ko cikas,
wannan aiki ya haɗu da barazana ta hanyoyi da dama, kamar haka.
1.
Rashin samun wadatattun littafai waɗanda suka yi magana a kan lamarin tsaro,
wanda hakan ya tilasta aka shiga neman kundaye, da muƙalu, da kuma hira da ɗaiɗaikun
mutane.
2.
Bayan haka kuma, akwai matsalar rashin samun haɗin kan wasu al'ummomi da
lamarin ya shafa.
3.
Daga ƙarshe kuma akwai matsalar da aka fuskanta, ta rashin kuɗi masu gidan
rana, domin gudanar da aiki a cikin lokaci.
1.5
MUHIMMANCIN BINCIKE
Bincike
shi ne gano wani abu wanda, da ba a sani ba, ko ƙari ga wani abu wanda aka sani
domin bayar da gudummuwa ko warware wata matsala da ta zama damuwa ga wata
al'umma (Bunza 2017).
Daga
wannan za a iya cewa muhimmanci wannan bincike ga rayuwar al'umma baki ɗaya, ya
haɗa da abubuwa kamar haka:
1.
Kasancewarsa bincike na farko da aka gudunar a kan sha'anin tsaro a garin Gusau
wanda zai taimaka wa al'umma da 'yan uwana ɗalibai manazarta domin samun sauƙin
fahimtar yadda sha'anin tsaro yake ba tare da shan wata wahala ba.
Wannan
zai sa su san irin rawar da za su taka wajen bayar da tasu gudummawa don
tabbatar da nasarar samun ingantaccen tsaro a tsakanin al'umma.
2.
Wani muhimmanci kuma da wannan bincike zai kawo shi ne ƙara samun haɗin kai ga
al'umma, domin samun zaman lafiya a tsakanin al'umma. Domin Hausawa na cewa:
Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka. Shi kuwa lamarin tsaro abu ne da ke buƙatar haɗin
kan kowa da kowa.
3.
Wannan aiki zai taimaka wa ɗalibai da manazarta, domin samun damar ɗora nasu
bincike a daidai inda na tsaya.
1.6
HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE
Da
yake ana nazari ne a kan abin da ya shafi yanayin tsaro, hanyoyin da ake
tsammanin sun fi dacewa a bi don cimma ƙudurin wannan bincike sun haɗa da:
1.
Da farko an fara tattara bayanai daga littatafan da aka wallafa da waɗanda aka
samu a ɗakunan karatu daban-daban.
2.
Nazarin kundayen binciken da aka gudanar a makarantu da Jami'o'i daban-daban da
kuma muƙalu da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani daban-daban da suka
danganci duk wani nazari da aka aiwatar game da yanayin tsaro.
Haka
kuma, an yi amfani da babban ɗakin karatu na Jama'ar Tarayya Gusau.
Da
kuma ɗakin karatu na Kwalejin horas da malamai na Gwamnatin Tarayya da ke Gusau
Jihar Zamfara (F.C.E.T Gusau).
Haka
kuma akwai ɗakin karatu na Kwalejin Ilimi da Fasaha (Zacas Gusau). Domin samun
nasarar wannan bincike.
Haka
kuma za a tattauna da dangogin masu sana'o'i daban-daban da suka haɗa da:
1.
Dillalai kamar na: Dabbobi, babura, kekuna, motoci, filaye
2.
Kungiyar 'yan kasuwa
3.
Kungiyar direbobi
4.
Kungiyar maƙera
5.
Hukumar jami'an tsaro
6.
Kungiyar 'yansakai
7.
Kungiyar 'yan banga
8.
Kungiyar mahauta
9.
Daga ƙarshe kuma za a tattauna da tsofaffin da suka san jiya da yau, da
sarakuna, da hakinmai da masu unguwanni, da sauransu.
Haka
kuma an tsara zantawa da jami'an tsaro da ke zaune a garin Gusau, domin
fahimtar yadda ake aiwatar da aikin tsaro jiya da yau da kuma dalilin da ke
haifar da haka.
Bayan
wannan za a zanta da 'yan jarida da ke zaune a cikin garin Gusau, da kuma
manyan malamai, musamman na cikin wannan gari, domin samun sakamakon bincike
mai armashi da gamsarwa.
Bugu
da ƙari, an shirya ziyartar wasu manyan jami'an tsaro da ke a cikin garin
Gusau, domin samun bayanai yadda suke gudanar da aikin nasu.
Tare
da matsalolin da ke addabar su da hanyoyin magance matsalolin, domin samun
nasarar tabbatar da tsaro a cikin garin Gusau da jihar mu da ƙasarmu Najeriya
baki ɗaya.
1.7
NAƊEWA
Daga
ƙarshe kuma wannan babin gabatarwa ce game da wannan aikin binciki, domin
haskakawa mai karatu, wanda ya zo da gabatarwa, da manufar bincike, da hasashen
bincike, da farfajiyar bincike, da matsalolin da suka kawo tarnaƙi game da
bincike, da muhimmancin bincike, da hanyoyin gudanar da bincike, daga ƙarshe
kuma wannan babin ya zo da naɗewa.
BABI NA BIYU
BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
2.0 GABATARWA
Duk da
irin yadda ake ganin cewa ba a yi wani abin da ya taka kara ya karya dangane da
irin wannan bincike na yanayin tsaro, ba za a rasa wasu abubuwa da suka yi kama
da hakan ba, musamman idan aka yi la'akari da irin binciken da masana da ɗalibai
suka gabatar a kan lamarin tsaro. Wannan fasali zai waiwayi ɗan abin da ya
samu, domin mu ga yadda yanayin ya kasance.
Wannan
babi zai yi bayani ne a kan bitar ayyukan da suka gabata, waɗanda suka haɗa da
bitar littattafan da aka wallafa, da kundayen bincike, da kuma muƙalu da
mujallu, da aka gabatar a wurare daban-daban masu alaƙa da wannan aiki.
2.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
Masu
azancin magana kan ce "Waiwaye adon tafiya." Haka yake, domin masana
da dama sun gudanar da bincike mabambanta dangane da sha'anin tsaro, amma ba a
taɓa aiwatar da wani bincike mai take irin wannan ba.
Babu
shakka ya zama wajibi ga duk wanda zai aiwatar da bincike, ya tsaya ya dubi
ayyukan magabata domin samun haske game da yadda suka gabatar da nasu ayyukan.
Domin ta yin haka ne za a fahimci inda aka kwana da kuma inda za a tashi.
Wannan
ne ya tilasta a waiwayi aikace-aikacen ayyukan da masana suka aiwatar domin
samun ƙarin haske. Daga cikin aikace-aikacen da aka gudanar waɗanda aka yi
bitar su, sun haɗa da: Bugaggun littattafai, da kuma muƙalu, tare da kundayen
bincike, kamar yadda za mu gani ɗaya bayan ɗaya.
2.1.1 WALLAFAFFUN LITTATTAFAI
Masana
da dama sun yi rubuce-rubuce, musamman akan harkar tsaro, inda suka tofa
albarkacin bakinsu, musamman a kan ma'anar tsaro da rabe-raben tsaro da
muhimmancin tsaro ga al'umma, da kuma gudummuwar da al'umma ke bayarwa a kan
harkar tsaro, daga cikin waɗannan masana akwai.
Nalado
A.M. (Babu shekara). Daga cikin wannan littafi mai suna Kano state jiya da yau
an yi (1864-1968) an yi bayanin yadda yaƙin Damagaram ya gudana da dabaru
iri-iri domin tabbatar da tsaron al'ummarsa tare da kariyar mutuncinsu.
Haka
kuma daga cikin wannan littafi an nuna yadda sarakuna suke shirya dubarun zuwa
yaƙi, da yadda suke ƙoƙarin bayar da kariya ga jama'arsu.
Gusau
M.B. Da Gusau M.S (2012). A cikin littafinsu mai take: Gusau ta malam Sambo sun
kawo bayanin sunan Gusau da kirarinta, da kuma asali da ma'anar kalmar Gusau.
Haka kuma an yi bayanin kafuwar Gusau da haɓakar ta wanda ya ƙunshi tarihin
garin Gusau da mutanenta na farko da bunƙasarta da tsarin sarauta da mulki, da
kuma tarihin rayuwar sarakuna tun daga jiya har zuwa yau. Haka an kawo bayanai
game da ganuwar garin Gusau wadda ta kasance wani ginshiƙi na samar da tsaro a
da.
Shi kuwa
Muhammad Isa Talata Mafara (1999).A cikin littafinsa mai taken: "Daular
Usmaniyya" ya bayyana irin hanyoyin da sarakuna ke bi domin kare kansu
daga abokan gaba, da yadda suke samar da kayan zuwa yaƙi da kuma na kariyar
mutuncinsu; Wannan littafi yana ɗauke da bayani a kan yaƙe-yaƙen da Shehu
Usmanu danfodiyo ya yi.
Shi
kuwa Aliyu M.Bunza (2006). A cikin littafinsa mai suna "Gadon feɗe
al'ada" Ya kawo bayani akan "Tsaro da siyasa" Ya ce daga cikin
manufar al'ada a rayuwar masu ita akwai samun tsaron kai da kaya, da gudanar da
siyasar rayuwa ba cikin takurawa ba.
Ya kuma
bayyana cewa, a can da ƙasar Hausa na fuskantar barazanar maƙiya na ciki da na
waje, don haka ne Bahaushe ya ƙirƙiro tsaro ta hanyar tsafe-tsafen tsare kansa,
da garinsa, da lafiyarsa, da kuma dukiyarsa.
Shi
kuma, Gusau A.R (2014) A cikin littafinsa mai taken "Mai dubun
nasara". Ya kawo bayani a kan tarihin Gusau a taƙaice, haka kuma ya kawo
bayanin jerin sarakunan Gusau, da kuma bayani a kan rabe-raben tsaro inda ya
nuna akwai tsaro irin daban-daban kamar haka:
1.
Tsaro na dukiya
2.
Tsaro na addini
3.
Tsaro na rayuka
4.
Tsaro na shuwagabanni
Masanin
ya ƙara da cewa, tsaro abu ne da sarakuna ya kamata su kula da shi, su ma
talakawa ba za a barsu a baya ba, domin suna taka rawa wajen ba da gudunmawa ga
tsaro.
Maryam,
M. Na Inna. (Babu shekara). A cikin littafinta mai suna "Tarbiyyar matasa
a Musulunci" daga cikin wannan littafi ta yi bayanin abubuwan da ke kawo taɓarɓarewar
tarbiyya da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya, daga cikin wannan littafi ta
kawo wane ne ɗan ta'adda da kuma bayani a kan hanyoyin magance wannan matsala.
Haka
kuma. Waya (2000). A cikin littafinta mai suna "Kano da Masarautarta Jiya
Da Yau", ta yi bayani akan asalin masarautar Kano da kuma hasashe akan
mazaunan farko, da wanzuwar mutane da kafuwar mazauni a Kano, haka kuma ta kawo
bayani akan hanyoyin kariyar kai.
2.1.2 KUNDAYEN BINCIKE
Hibbatullahi
M. Da wasu (2014). Sun yi nazari ne akan matsalolin da ke haifar da ta'addanci
a unguwar Sabon Fegi Gusau wanda suka gabatar a Sashen Hausa Tsangayar Harsuna
Kwalejin Ilimi da Ƙere-Ƙere ta Gwamnatin Tarayya da ke Gusau Jihar Zamfara. Sun
kawo ma'anar kalmar ta'addanci da kuma waɗanda ke yin ta'addanci da abubuwan da
ke haifar da ta'addanci, da matsalolin da ta'addanci yake haifarwa. Haka kuma
sun kawo hanyoyin yaƙi da ta'addanci, daga ƙarshe kuma sun zo da bayanin
hanyoyin da ya kamata abi a samar da jami'an tsaro donmagance matsalar
ta'addanci.
Yusuf
Wada Da wasu (2014) a kundin bincikensu mai taken "Yanayin Tsaro A jiya Da
Yau A Garin Dandume" Da suka gabatar a sashen Turanci, da Hausa da Islama
kwalejin kimiyya da fasaha "Zacas Gusau jihar Zamfara" Domin cike
sharaɗin samun Takardar "Diploma" Sun yi bayani akan ma'anar tsaro,
ire-iren tsaro da kuma yanayin tsaro a garin Ɗandume, da kayayyakin da ake
gudanar da tsaro a garin Dandume, da kuma bayani a kan matsalolin tsaro, da
ƙarshe kuma sun kawo bayani akan muhimmancin tsaro a garin Ɗandume.
2.1.3 MUƘALU DA MUJALLU
Muƙalu
da mujallu su ne takardu masu ɗauke da bincike na ilimi, mafi akasarin waɗannan
ana gabatar da su ne a lokuttan tarurrukan ƙara wa juna sani. Game da harkar
tsaro, a matakai daban-daban an gabatar da muƙalun da dama da suka haɗa da:
Shekarau
M.I (2007). A cikin wata muƙalarsa da ya gabatar mai taken "Role of Government
In Security of Life and Property" a cikin wannan muƙala an yi bayanin cewa
a ƙalla akwai dubban mutane da suke yaƙi a tsakanin 'yan ta'adda, haka kuma
daga cikin wannan muƙala an kawo bayanin inda Alh. Yusuf Maitama Sule: Ya ce a
cikin harkar tsaro akwai rashin ma'ana, ita kuma siyasa an gurɓata ta da cece
kuce, shi kuma tattalin arziki an gurɓata shi da cin hanci, haka kuma al'umma
an gurɓata su da rashin kyakkyawan ɗabi'u, haka kuma an yi bayanin ta'addanci a
cikin lokaci, daga ƙarshe kuma an yi bayanin tsaro a ɓangaren musulunci.
Kadaura
journal of Hausa multi disciplinary studies. Vol 1. No 5 September(2019).
Department of Nigerian Languages and Linguistics Kaduna State University,
Kaduna. A cikin wannan mujallar sun kawo bayani akan ma'anar tsaro da kuma
bayani a kan kafuwar tsarin shugabanci na gari-gari, haka kuma sun kawo bayanin
yadda za a kare al'umma daga miyagun mutane, da yadda suke samar da kayayyakin
yaƙe-yaƙe, da kuma cusa tarbiyya ta hanyar tsaro ga yara, haka kuma daga ƙarshe
sun nuna yadda ake samar da jami'an tsaro.
Farfesa
M.L. Mayanci (2019) a cikin wata muƙalarsa mai taken: "Converting the
Menace of Insecurity in Zamfara State Within 100 days Governor Matawalle".
Daga cikin wannan muƙala an yi bayanin mene ne tsaro, inda ya ce tsaro wani
babban haƙƙine ga kowace ƙasa baki ɗaya. Ya kuma yi bayanin cewa shi tsaro ya
ƙunshi tsaro na mutane da tsaro na dukiya, da tsaro na muhalli, da kuma tsaro
na jindaɗin rayuwa. Haka kuma ya bayyana cewa, a cikin kundin tsarin mulki na
ƙasa, na shekarar (1999) ya nuna tsaro da walwala ta mutane ya kamata ya zamo
mataki na farko da gwamnati za ta yi aiki akai, wato kulawa da shi, domin yawan
matsaloli na rashin tsaro da suke faruwa a cikin sassa daban-daban na Najeriya
shi ya sa aka kirata da ƙasa marar tsaro, haka kuma an yi yinƙuri daga sassa
daban-daban na gwamnati, don a samu a kawar da matsalar rashin tsaro.
1.
Tsaron kai
2.
Tsaron kaya
3.
Tsaron kare martabar gari
4.
Tsaro na "Kura rame"
5.
Tsaro na ganuwa.
2.2 HUJJAR CIGABA DA BINCIKE
Idan
muka yi la'akari da bayanan da suka gabata, a inda muka yi tankaɗe da rairaye a
kan nazarce-nazarcen da aka aiwatar a ƙoƙarin muna kwatanta ƙudurin wannan
nazari da abin da magabata a fagen nazari suka aiwatar, za a luracewa har zuwa
yanzu ba a ci karo dawani bincike da aka gudanar dangane da yanayin tsaro. A
garin Gusau ba. Wanda ke da alaƙa da nawa shi ne na Wada (2014). Shima ya
karkatane a garin Ɗandume. Kowa ne al'amari a rayuwa yana buƙatar hujja a wajen
cigaba da aiwatardashi, wannan binciken da ake kan gudanarwa yana da matukar
muhimmanci, domin a iya bincikena ban yi karo da wani bincike ba mai irin
wannan taken aikin da nake gudanarwa sai dai mai alaƙa da shi, saboda haka
cigaba da wannan binciken zai taimakawa masu sha'awar bincike irin wannan,
wajen sauƙin fahimtar yanayin tsaro a garin Gusau.
2.3 NAƊEWA
Wannan
babin ya fara ne da gabatarwa tare da bayyana irin ayyukan da aka yi bita a binciken
da ya gabata, domin waiwaye kan ayyuka masu ƙarin haske, ko kuma masu shige da
irin wannan aiki da suka haɗa da bugaggun littattafai masu alaƙa da wannan
aiki, da kuma muƙalu, da mujallu, da kuma kundayen bincike, duk waɗannan ayyuka
babu mai take guda da wannan aiki, sai dai alaƙa.
FASHIN
BAƘI A KAN MA'ANONI DA SUKA SHAFI TAKEN BINCIKE
GABATARWA
Wannan
babi zai yi bayani a kan ma'anar yanayi, da kuma ma'anar tsaro da ire-iren
tsaro, da ma'anar gari, haka kuma wannan babi zai kawo ma'anar kalmar Gusau da
ƙarshe kuma wannan babin ya zo da naɗewa.
MA'ANAR
YANAYI
Bayaro
(2006 : 478) ya bayyana yanayi da cewa hali irin wanda ake ciki, kamar na
damina ko sanyi, ko zafi. Haka kuma ya ƙara fassara yanayi da cewa hali irin
wanda mutum ke ciki, ko a ce yana fushi, ko farin ciki, misali kamar yadda
fuskarsa ya nuna wanda ake iya gani a wannan lokaci.
Kamar
yadda shi ma Ayuba T Abubakar (2015 : 496) ya bayyana yanayi da cewa, hukuncin
iska, ko sanyi, ko ɗumi, ko damina, ko rani, ko da fannin duniya ya shiga ko ya
canza daga wani zamani zuwa wani.
MA'ANAR TSARO
Ayuba T
Abubakar (2015: 472) ya bayyana kalmar tsaro da cewa, suna, namiji, wato kare
jama'a daga abin da zai cuce su. Ma'aikatan tsaro masu aikin tsare lafiya da
dukiyar mutane, haka kuma akwai tsaron ƙasa, kare ƙasa daga illa ko abokan
gaba, ko kuma kare kai ko, ƙaddara.
Bunza A
M (2006 : 99) ya bayyana tsaro da siyasa na daga cikin manufar al'adar rayuwar
masu ita, akwai samun tsaron kai da kaya da gudanar da siyasar rayuwa, ba cikin
takurawa ba. A can da, ƙasar Hausa na fuskantar barazanar maƙiya na ciki da
waje. Dalili da haka ne Bahaushe ya ƙirƙiro tsafe-tsafen tsare kansa, da
garinsa, da lafiyarsa, da dukiyarsa.
Binta
Musa Hassan (2019 : 176) ta ce, Kalmar tsaro na nufin yin gadi ko kare ko kula
ko kiyaye wani ko wasu muhimman abubuwa daga taɓuwa da za ta kawo illa ga abin.
Ko kuma ajiye ko riƙe ko kange ko kulle
wani abu wato dai kariya "CNHN", (2006). Haka kuma kalmar na
iya ɗaukar ma'anar kula ko kare duk farfajiyar ƙasa da iyakokinta da arzikinta
da kuma kula da lafiyar 'yan ƙasa da iyalinsu da tarbiyyarsu da kuma samar masu
da ayyukan yi "kamar sana'o'i" da yi masu jagoranci na gari da
tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu . Waɗannan su ne ginshiƙai kuma muhimman
abubuwa da tsaro ya ƙunsa. Yayin da rashin jagoranci na gari da rashin ayyukan
yi ga jama'a da aikata manyan laifuka da rigingimu a tsakanin al'umma kan
haddasa rashin tsaro da rarrabuwar kawunan al'umma.
Gusau da Gusau (2012 : 188), sun bayyana cewa,
tsaro abu ne da kowace al'umma take da buƙata da shi ; Da zarar aka wayi gari
rayuka da dukiyoyin mutane suna fuskantar barazana, to abu ne mawuyaci, ko
addini su iya gudanarwa yadda ya kamata. Tabbatar da tsaro ga dukiya da addini,
da rayuka, da hankali, da zuri'ar mutane, abu ne da alhakinsa ya ɗora a kan
shugabanni. Amma kuma, tattare da haka, su ma talakawa akwai rawar da ya kamata
su taka a matsayin tasu gudunmawa. Bisa wannan manufa ne sarakuna a kowane
lokaci, suke ƙoƙarin faɗakar da talakawansu akan muhimmancin kula da wannan
lamari.
IRE-IREN TSARO
Ana iya
kallon lamarin tsaro ta mabanbantan fuskoki da masana suka karkasa shi, ta
la'akari da nau'in da.
1. TSARO NA GANUWA
Bunza
A.M (2018 : Lecture) ya bayyana cewa, tsaro na ganuwa shi ne tsaron da ake
zagaye gari da gina ta laka, haka kuma a kan yi mata ƙofofi domin shige da
ficen mutane, a kan yi wannan ganuwa ne domin kare martabar gari, da kuma
mutanen gari, da dukiyoyinsu, da lafiyarsu, a kan yi wannan ganuwa ne domin
tabbatar da tsaro.
2. TSARON KURA RAMI
Bunza
A. M (2018: lecture) ya ƙara da cewa, tsaron kura rami, tsaro ne wanda mutanen
gari ke taruwa a bakin gari, suyi rami babba musamman don hana miyagun namun
daji shigowa cikin gari.
3.
TSARON KAI
Bunza
A. M (2006:99) ya bayyana cewa tsaron kai shi ne dukkanin wani tsaro da zaka
samarwa kanka, domin kariya daga wani haɗari ko farmaki wanda zai iya samun
rayuwarka a tafiya, ta yau da kullum. Haka kuma tsaron kai na iya ɗaukar
dukkanin abin da za ka yi domin samarwa kanka kyakkyawar kulawa da kariya ga
duk wani abu da zai cutar da kai.
4.
TSARON ƘASA
Bunza
A. M (2018: lecture) ya bayyana mana da cewa, wannan shi ne tsaron da ake bayar
da cikakkiyar kulawa da shuwagabanni kan yi wajen kare ƙasarsu ko garurukansu
daga masu tayar da zaune tsaye, ko kuma domin hana kwace wani ɓamgare na
ƙasarsu. Haka kuma tsaro ƙasa shi ne duk wata gudummuwa da shugaba zai bayar
domin tabbatar da kariya da bayar da kulawa ga ƙasa domin gujewa farmaki ga
abokan gaba da mahawara da kan iya kawowa daga wani ɓamgare.
5. TSARON DUKIYA
Bunza
A. M (2018: lecture) ya bayyana tsaron dukiya da cewa, wannan tsaro shi ne
wanda ake yi domin ba da kulawa da kariya ga dukiyoyin al'umma, domin kare
dukiya daga 'yan fashi ko ɓarayi, ko kuma masu yiwa dukiyoyin al'umma, ko
gwamnati ɓarna. Haka kuma tsaro ne da aka bayar da kulawa mai muhimmanci, domin
dukiya ita ce ƙashin bayan duk wata rayuwar al'umma. Bugu da ƙari, tsaron
dukiya tsaro ne wanda ke da matuƙar muhimmanci, domin kare al'umma daga
rikice-rikice ko faɗace-faɗace.
6. TSARON JAMA'A
Yusuf
Wada da wasu (2014) a cikin kundin bincikensu mai taken yanayin tsaro a garin
Ɗandume, inda suka bayyana cewa tsaron jama'a shi ne, kasancewar gwamnati ita
ce uwar al'umma ta kanyi iya ƙoƙarinta domin ganin ta bayar da kariya da kulawa
mai inganci ga jama'a, domin kaucewa rikici ko faɗace-faɗace a cikin gari. Bugu
da ƙari, tsaron jama'a shi ne irin kulawar da masu mulki wato shuwagabanni ke
bayarwa a kan talakkawansu tare da ƙudurin kawo zaman lafiya a tsakanin
al'umma.
7. TSARON SHUWAGABANNI
Yusuf
Wada da wasu (2014) a cikin kundin bincikensu mai taken yanayin tsaro a garin
Ɗandume, inda suka bayyana cewa tsaron shuwagabanni shi ne tushiya mafarin duk
wani tsaro. Wannan shi ne irin tsaron da ake baiwa shuwagabanni tare da
cikakkiyar kulawa, da kuma karesu daga mahara. Haka kuma wannan shi ne tsaron
da ake ba muhimmanci domin nuna kulawa da bayar da cikkakkiyar kariya ga shuwagabanni
domin karesu daga duk wani abu da ke iya cutar da su.
MA'ANAR GARI
Bayaro
(2006: 159) ya nuna cewa kalmar "gari" na cikin jerin sunaye na maza,
jam'i kuwa garuruwa a wani karin harshen a kan ce garuruka ko garurra. Kalmar
na nufin wurin da mutane suka zauna suka yi gidaje.
MA'ANAR KALMAR GUSAU
Bayaro
(2006 : 177) ya bayyana cewa, kalmar na cikin jerin kalmomin suna jinsin mace.
Ya kuma nuna kalmar na ɗauke da ma'anar : "sunan babban birnin jihar
Zamfara.
Gusau
da Gusau (2012 : 1) sun bayyana asali da ma'anar kalmar "Gusau" an
samo ta ne daga kalmar "gusa" ko "matsa" waɗanda ke nuna
gurgusawa ko matsawa daga bagire zuwa wani bagire da ke kusa.
NAƊEWA
Kamar
yadda muka kammala wannan babin, mun yi bayani a kan ma'anar yanayi, da kuma
ma'anar tsaro da ire-iren tsaro, da kuma ma'anar gari, haka kuma mun yi bayani
a kan ma'anar kalmar Gusau.
BABI NA HUƊU
YANAYIN TSARO A GARIN GUSAU
4.0 GABATARWA
Wannan
babin zai yi bayani a kan taƙaitaccen tarihin Gusau, da bayani a kan yanayin
tsaro na gargajiya da na zamani kamar yadda za mu gani a ciki. Haka kuma an
kawo bayani a kan 'yan ta'adda da ire-iren 'yan ta'adda, da kuma abubuwan da ke
haifar da ta'addanci a garin Gusau, da illolin da ta'addanci ke haifarwa, tare
da kawo bayani game da matsalolin da hukuma ke fuskanta. Babin ba zai kammala
ba, sai an zo da irin rawar da al'umma da hukuma ke takawa wajen ganin an
magance matsalar ta'addanci a cikin garin Gusau, an kawo muhimmancin tsaro a
cikin wannan babi, daga ƙarshe kuma ya zo da naɗewa.
Garin
Gusau gari ne mai faɗi sosai, da kuma albarkatun ƙasa, da sana'o'i kamar noma
da kiwo, da kuma sauran hanyoyin bunƙasa tattalin arziki kamar kasuwanci. Haka
kuma gari ne wanda yake da yawan al'umma, sannan ga ingantaccen tsarin mulki na
gargajiya da na zamani, hakan ya sanya aka bai wa tsaro muhimmanci jiya da yau.
A wannan babin za a yi ƙoƙarin gano ko fito da
ma'anar tsaro da rabe-raben tsaro da kuma ma'anar ta'addanci da ire-iren daga
ƙarshe kuma ya zo da naɗewa.
4.1 TAƘAITACCEN TARIHIN GARIN GUSAU
Gusau
(2014: 96) an kafa garin Gusau ne a shekara ta 1811 bayan tasowa daga 'Yandoto
a shekara ta 1806.
Garin
Gusau yana ɗaya daga cikin manyan garuruwan tsohuwar jahar Sakkwato, kafin daga
bisani ya zama babban birnin Jahar Zamfara a shekarar 1996. Kundin bayanin
tarihin ƙasa na 1920 ya nuna, garin yana bisa kan titin Sakkwato zuwa Zariya
ne; kilomita 179 tsakaninsa da Zariya, 210 kuma tsakaninsa da Sakkwato. Daga
Gabas, ya yi iyaka da ƙasar Katsina daga Kwatarkwashi. Daga Arewa kuma ya yi da
ƙasar Ƙaura. A yayin da ya yi wata iyakar daga Yamma, da Bunguɗu. Ta ɓangaren
Kudu kuma ya yi da ƙasar Ɗansadau da Tsafe. (Gusau, 1912:7).
Gusau
(2014: 96) ya ƙara cewa, kasancewar almajirin Shehu Usmanu dan Fodiyo, Malam
Sambo ɗan Ashafa ya kafa Gusau a shekara ta 1811, wanda yake shi da jama'arsa
ba ruwansu da duk harkokin da suka shafi bautar iskoki ko tsafi irin wanda
Hausawa ke yi kafin zuwan addinin musulunci. Watau, garin Gusau ba ya da
tarihin Jahiliyya. Hakan ta sa duk al'adun Gusawa, al'adu ne irin na Musulunci.
Kuma shigowar wasu mutane, wato baƙi a Gusau, ba ta gurɓata waɗannan kyawawan
al'adu ba, don kuwa mafi yawan baƙin da ke tahowar Malamai ne na Musulunci da almajirai,
Fulani da wasunsu, da kan taho garin don tsira da addininsu, da mutuncinsu, da
kuma dukiyarsu.
Gusau (2014
: 97), haka kuma ya nuna cewa, ta ɓangaren fada kuma, duk umarnin da zai fito
daga can, zai kasance ne dabara da abin da Musulunci ya yarda da shi na
kyawawan ɗabi'u da al'adu. Musamman kuma da yake, kusan duk Sarakunan da aka yi
a garin Malamai ne na addinin Muslunci masu taƙawa da tawali'u. Da wannan
shimfiɗa ne, al'adun Gusawa ke gudana dabara da koyarwar addinin Musulunci da
kyawawan al'adu irin na Fulani da na Hausa, waɗanda ba su ci karo da Shari'a
ba. Irin wancan yanayi na kwararowar baƙi da ƙungiyoyin mutane daban-daban
musamman a zamanin Sarkin Katsina Gusau Malam Muhammadu Modibbo "1867 M /
1282 H - 1877 M / 1291 H" Ya sa garin ya sami bunƙasa a cikin ɗan ƙanƙanin
lokaci.
Gusau
(2014: 97), ya nuna cewa, samun sukunin gudanar da harkokin addinin Musulunci,
waɗanda suka shafi karatu, da karantarwa da kuma ibada ba tare da wata
tsangwama ba. Samun cikakken tsaron rayuka da dukiya sakamakon ganuwa da garin
yake da ita. A haka sai aka wayi gari, babu abin da ya sha wa mutanen garin
kai, sai harkokin karatu da noma da kuma kasuwanci. Nan take kuwa sai haɗuwar
waɗannan ginshiƙai, ya samar da wani kyakkyawan yanayi a garin, kuma ga
kyakkyawar nagartattar aƙida, da yalwar arziki da kwanciyar hankali, da suka
taimaka wajen bunƙasa wannan gari.
Gusau
(2014: 98), ya nuna cewa zuwan Bature da cin ƙasar Hausa da shimfiɗa tsarin
ilimin Boko, ya sa wasu al'adu tsiruwa. Ana cikin haka kuma sai ga Shari'ar
Muslunci ta sake kunno kai, ta godaben Mujaddadi. Wannan sabon lamari a wannan
ƙarni, shi ma ya kawo canje-canje na alhairi a al'dun mutanen garin Gusau a
matsayinsa na babban birnin Jiha. Mutane da yawa na halartar masallatai don
tafsiri da itikafi fiye da ɗari. Kawo wa yau akwai malamai da dama da suka
shahara da gudanar da tafsiri a masallatan Juma'a da wasunsu a garin Gusau.
Gusau
(2014:98) A bisa ƙididdiga da taƙaitawa, garin Gusau a daidai lokacin da ake
gudanar da wannan aiki, yana da masarauta ɗaya (1); babban sarki ɗaya, uwayen
ƙasa goma sha uku (13); 'yan majalisa goma sha takwas (18). Masallatan Juma'a ashirin
da uku (23); ƙananan makarantun boko sittin da huɗu (64); matsakaita kuma
Arba'in da uku (43). A yayin da ake da manyan makarantu guda huɗu (4).
Gusau
(2014:99). Haka kuma akwai manyan kasuwanni guda uku (3); kamfunnan kasuwanci
kuma ashirin da bakwai (27). A yayin da ake da manyan Malaman addinin Musulunci
tsakanin rayayyu da waɗanda suka riga mu gidan gaskiya. Bankunan kasuwanci kuma
da na noma akwai guda ashirin da uku (23), a yayin da ake da attajirai, manya
da matsakaita, da ƙanana, da masu tasowa kimanin ɗari da talatin da biyar
(135), da sauran abubuwa da dama.
Daga
kuma lokacin da aka kafa wannan gari na Gusau, an yi Sarakuna kamar haka:
Malam
Muhammadu Sambo (1806-1827)
Malam
Abdulƙadir (1827-1867)
Malam
Muhammadu Modibbo (1867-1876)
Malam
Muhammadu Tuburi (1876-1887)
Malam
Muhammadu Giɗe (1887-1900)
Malam
Muhammadu Murtala (1900-1916)
Malam
Muhammadu Ɗangidan (1916-1917)
Waɗanda
suka yi sarautar Gusau ba daga gidan Malam Sambo ba.
Malam
Ummaru Malam (1917-1929)
Muhammadu
Mai akwai (1929-1943)
Usman ɗan
Sama'ila (1943-1945)
Ibrahim
Marafa (1945-1948)
Muhammadu
Sarkin Kudu (1948-1951)
Alhaji
Sulaimanu Isah (1951-1984)
Dawowar sarauta gida:
Alh.
Muhammadu Kabir Danbaba (1984-2015)
Alh.
Ibrahim Bello (2015-?)
4.1.1 KAFUWAR GUSAU DA BUNƘASARTA
Gusau
da Gusau (2012: 26: 27: 28), sun bayyana cewa, Gusau a zama na biyu, duk da
matsalolin da suka kewaye Wonaka, sai da Sarkin Katsina Malam Abdulƙadir ya
shekara talatin da uku (33) a Wonaka daga 1827 zuwa 1860.
A
shekarar 1860, Magajin Korau wato Sarkin Katsina na Maraɗi da Magajin Baciri
wato Sarkin Gobir na Tsibiri suka yi niyyar su yi wa garin Wonaka zobe tun da
safe, daga nan sai Sarki Abdulƙadir suka sami labari, don haka, suka fita zuwa
Birnin Rawayya, Sarkin Katsina Abdulƙadir ya shekara biyu, daga 1860 zuwa 1862
da jama'arsa a Birnin Rawayya kafin su koma tsohon wurin zamansu na Gusau.
Gusau
da Gusau (2012: 27:28), sun nuna cewa, a yayin da mutanen Gusau suka sami zama
a Rawayya, suka ga sun yi ƙarfi, sai suka shiga tsananta wa mutanen Rawayya,
suka hana su shaƙaƙat, har ta kai idan Rashi, hakimin Rawayya, ya sa aka yi
shela, sai su koma su yi tasu shelar, su warware abin da Rashin ya umarta. Daga
nan, sai mutanen Rawayya suka yi shawarar hanyar da za su bi don su fitar da
mutanen Gusau daga garinsu. An wani daga cikinsu ya ce, tun da bamu iya cin su
da yaƙi, ba abin da zai sa su bar garin nan sai gori. A bari sai Sarkin yaƙinsu
ya fita ƙilisa bayan gari a rufe ƙofofi, in ya yi magana a mayar masa da baƙar magana. Suka
shiryar da haka, kowa ya yarda da wannan shawarar.
Gusau
da Gusau (2012:27:28), haka sun ƙara da cewa, bayan wannan shawara, ran nan sai
Sarkin Yaƙi Salihu Ɗankambo cikin mutanen Wonaka ya fita ƙilisa da marece. Ko
da ya dawo, sai ya tarar an rufe dukkan ƙofofi, ko'ina ya zagaya, sai ya tarar
da ita a kulle. Daga nan ya koma ƙofar da Sarkin ƙofa yake a zaune, ya nemi ya
buɗe masa ya ƙi, sai Sarkin ƙofa ya ce masa, "Kai gusa ka ba mu wuri na ƙi
buɗe maka. Bayan haka ana nan, sai
Sarkin Katsina Abdulƙadir suka fita zuwa idi, sai mutanen Rawayya suka rufe
ƙofofinsu. Mutanen Gusau suka nemi a buɗe masu, aka ƙiya, har ma dai suka yi
masu gori da su zarce zuwa garinsu na farko. Daga nan Sarkin Yaƙi Salihu
Ɗankambo ya ɗaura ƙaya a sirdin dokinsa, ya jawo ta har zuwa tsohon wurinsu,
wato 'Yar Gusau, ya buɗe hanya ga mutane, amma sai Ya gurguso gabas kaɗan da
'Yargusau ya zaɓi wuri. Da mutane suka iso aka ci gaba da gyara wuri, aka kafa
wa Sarkin Katsina Abdulƙadir bukkokinsa, sai kuma na Malam Muhammadu Modibbo da
Ɗangaladima Usamatu da shi kansa Salihu Ɗankambo da Liman Muhammadu Babba da
sauransu. Haka dai mutanen Gusau suka dinga tasowa daga Rawayya suna zuwa suna
gyara wuraren zama har suka bar Rawayya kwata-kwata. Da suka dawo wannan wuri
sai suka kira shi Gusau.
4.2
YANAYIN TSARO NA GARGAJIYA
Tukur
Ibrahim S/Rafi (2021), ya nuna cewa, a lokacin da, yadda ake gudanar da tsaro
ya sha bamban da yadda ake gudanar da shi a wannan lokacin, saboda a can da
garin Gusau duk wani mulki da cikakken iko da bayar da kariya ga al'ummar garin
Gusau duk suna a hannun sarakunan gargajiya ne. Kasancewar akwai ƙauyuka da
dama da ke ƙarƙashin kulawar garin Gusau kamar Abarma da Tungar Fulani, da
Mareri, da Damba da sauransu. A kowane ƙauye akwai mai Unguwa wanda shi ke da
alhakin kula da al'ummar wannan yanki, ta ɓangaren tsaron lafiya da dukiyoyinsu
baki ɗaya.
4.2.1 GANUWA DA ƘOFOFIN GUSAU
Abdulmalik
A da Murtala I Gusau (2019: 100) Kamar yadda muka samu tarihi an samar da
ganuwa ne sanadiyyar yaƙe-yaƙe da hare-haren da ake fuskanta na wancan zamani.
An gina wannan ganuwa da ƙofofinta a lokacin Sarkin Katsinan Gusau Malam
Abdulƙadir a shekarar 1863 bayan dawowa Gusau a zama na biyu.
Bayan
mutanen Gusau sun baro Rawayya a shekarar 1862, sai suka dawo Gusau a karo na
biyu kamar yadda masana suka bayyana, haka kuma a wani lokaci cikin shekarar
1863 Malam Abdulƙadir ya kai ziyara ga Sarkin Musulmi Amadu ɗan Atiku kuma suka
tattauna matsalolin da Gusau ke fuskanta na rashin tsaro, Sarkin Musulmi ya yi
umarni ga Sarkin Fulanin Bunguɗu da Sarkin Ƙauran Namoda da mutanen Rawayya da
mutanen Kwatarkwashi, cewa su taimaki Malam Abdulƙadir a kewaye garin Gusau da
ganuwa. Wannan aiki shi ya tabbatar da dawowar cibiyar masarautar Gusau da zuwa
garin Gusau tare da ba da kariya ga mutanen garin, don tabbatar da tsaro.
Bayan
haka kuma a kowace ƙofa da ke a cikin garin Gusau tana da ƙyaure na ƙarfe wanda
maƙera na gargajiya suka ƙera a matsayin gambun wannan ƙofa, haka kuma akwai
Sarkin ƙofa wato wani mutum da a kan sanya domin kula da wannan ƙofa domin masu
shiga da ficen wannan ƙofa.
Abdulmalik
A da Murtala I (2019: 101), sun nuna cewa, a kan gina ganuwa a gari ne, domin
kare garin da jama'arsa daga hare-hare da suka yi yawa a wancan lokaci, dalili
da haka shi ya sa bayan an gina ganuwa a kan ƙarfafa tsaronta ta hanyar gina
rami a bayanta. Wannan rami a kan haƙa shi daga bayan gari kimanin ƙafa goma
daga jikin ganuwar, kuma ana cika shi da duwatsu da ƙayoyi ta yadda mutum ko
doki na zai iya bi ta cikinsa ba. Bayan an kammala ginin ganuwa a gari, an
samar da ƙofofi waɗanda ta cikinsu ne kawai ake shigowa cikin gari, dan haka
kowace ƙofa da sunan da aka raɗa mata bisa wani dalili ko munasaba. Kusan
dukkan tsofaffin birane a ƙasar Hausa waɗanda aka kafa kafin jihadi ko bayan
jihadi suna da ganuwa, misalin irin waɗannan garuruwa sun haɗa; garin 'Yan
doto, Kano, Katsina, Alkalawa, Bauchi, Birnin Kebbi, Zariya da Daura duk suna
da ganuwa.
Abdulmalik
A da Murtala I Gusau (2019: 101), sun nuna cewa, ganuwar garin Gusau an yi ta
ne bayan jihadi, an gina wannan ganuwa sanadiyyar hare-haren da mayaƙan ƙasar
Katsina ke kawowa mutanen Gusau. Ginin ganuwar ya faru ne a lokacin Sarkin
Katsinan Gusau Malam Abdulƙadir a zamanin Sarkin Musulmi Amadu ɗan Atiku.
1. ƘOFAR KWATARKWASHI
A
binciken da muka yi a kan ƙofar Kwatarkwashi mun samu bayanai daga masana sun
tabbatar mana da samuwar wannan ƙofa kuma sun faɗi daidai inda ƙofar take, tana
nan wurin tsohuwar MTD kusa da tankin ruwa da ke sabon gari. Ita wannan ƙofa
babba ƙofa ce, wadda mutanen Kwatarkwashi ke shigowa zuwa cikin tsakkiyar garin
Gusau. A lokacin da aka gina ganuwa, an buɗe wannan ƙofa ne saboda mutanen
Kwatarkwashi da ke shigowa Gusau domin, hulɗoɗin kasuwanci da cinikayya da
sauran mu'amaloli yau da kullum, haka ya sa aka saka mata suna ƙofar
Kwatarkwashi, Bello Aliyu Ɗanmaituwo (2020).
Taswirar Ƙofar Kwatarkwashi
2.
Ƙofar Katsaura
Ƙofar
Katsaura ɗaya ce daga cikin ƙofofin Gusau, mazaunin wannan ƙofa yana nan cikin
Unguwar Toka a yanzu. Mun tuntubi mutane mazauna wurin da dama game da wannan
ƙofa, a inda muka samu ra'ayoyi mabanbanta a kan asalin sunan wannan ƙofar. Da
farko mun yi hira da Alhaji Shehu Ɗan Moriki mai shekaru saba'in da huɗu (74)
ya tabbatar mana da cewa ƙofar tana nan a Unguwar Toka daidai kusa da gidan
Baba Ɗan kantoma. Ya bayyana mana cewa asalin kalmar Katsaura sunan wani bawan
Allah ne mai suna Katsaura mutumin Nahuce ne. Shehu Ɗan Moriki (2020).
Taswirar Ƙofar Katsaura
3.
ƘOFAR RAWAYYA
Ƙofar
Rawayya kamar ƙofar Kwatarkwashi take an kafa ta ne saboda mutanen Rawayya, su
ke shigowa ta wannan ƙofa idan sun zo kasuwanci Gusau, haka mutanen Gusau idan
zasu tafi Rawayya ta wannan ƙofa suke bi. Bisa ga abin da muka ji daga bakin
Garba mai gudu: Ya ce wannan ƙofa tana nan a bakin tsohuwar kasuwa wurin gidan
Alhaji Goga kusa da gidan maƙera a hanyar zuwa gidan Sarki kanwuri Gusau. Malam
Hassan Mai keke (2021)
Taswirar
Ƙofar Rawayya
4. ƘOFAR JANGE
Ƙofar
Jange asalin muhallin da ƙofar take mashaya ce wato wuri ne da yake magudanar
ruwa mutane na ɗibar ruwa a wurin kuma suna shayar da dabbobinsu. Jange sunan
wani mutum ne mayaƙi, Jarumi, maharbi da ke zaune a wurin yana farautar namun
daji. Kamar yadda muka samu bayani daga bakin Abdulmalik Aminu marubucin
littafin (Hasken masarautar Gusau 2019) mai shekaru alba'in da ɗaya (41).
Taswirar Ƙofar Jange
5. ƘOFA MATSATTSA
Ƙofa
Matsattsa mazauninta yana nan a Marnar Talikai gaba da injinin niƙa kusa da
makarantar Allo ta Malam Sanda. An yi wannan ƙofa ne a sanadiyyar wani mutum da
ake kira "Kako" (Kakan su Sanata Hassan Nasiha da Muhammadu Buwai)
mutumin Katsina ne ya fito daga 'Yan Tumaki. Mun yi hira da wani mutum mai suna
Muhammadu Nakungun mai shekaru ɗari da 'yan kai yana nan zaune a Marnar
Talikai, sunan kakansa Muhammadu Ɗan mairi shi ne wanda ya yi tsaron wannan
ƙofa ta Matsattsa. Hassan Muhammadu Ɗanmairi (2020).
Taswirar Ƙofar Matsattsa
6. ƘOFAR MANI
Abdulmalik
A da Murtala I Gusau (2019 : 109) Ƙofar Mani na ɗaya daga cikin ƙofofin Gusau,
ta samu sunanta ne daga wani mutum da ake kira Mani, haka kuma an sakawa sunan
unguwar ƙofar Mani. Kamar yadda bincike ya nuna, ƙofar Mani tana nan a hanyar
zuwa Kanwurin Sarki, idan ka matsa kaɗan zaka cimma Ƙofar Mani daidai wata kasuwa, a gefe kuma akwai tsohon gidan
Mani inda ake sayar da hatsi.
Taswirar Ƙofar Mani
7. ƘOFAR TUBANI
Ƙofar
Tubani tana dab da gidan Malam Muhammad Noma kusa da injinin niƙa dab da wata
ƙaramar gada da kuma makarantar Islamiyya da
Gangaren Na Dumau. Haka kuma akwai tsohon gidan Dumau yana nan kusa da
ƙofar, amma a wancan lokacin gidan yana cikin baici ne. Asalin sunan ƙofar an
samo shi ne daga wani mutum da ake kira da suna Tubani, shi manomi ne, sai dai
zuwa wannan lokaci babu sauran birbishin zuri'arsa. A halin yanzu, mun samu waɗansu
bayanai ne daga wani dattijo mai suna Sani Madugu mai shekaru tamanin da biyar
(85), da kuma wani mutum mai suna Sani Ɗankwamma mai kimanin shekaru saba'in da
biyar (75).
Taswirar Ƙofar Tubani
8. ƘOFAR DOKAU
Abdulmalik
A da Murtala I Gusau (2019 : 111) Ƙofar Dokau ko Dogo? An sami saɓani dangane
da sunan wannan ƙofa. A ruwayar wasu marubuta da suka wallafa littatafai da ke ɗauke
da tarihin Gusau sun kawo cewa sunan ƙofar ita ce, ƙofar Dogo ba Dokau ba. Kamar
yadda muka ba da bayanai ana raɗa wa ƙofa suna ne a sanadiyyar wata a salsala
ko munasaba, idan muka duba tsofaffin garuruwa dukkan ƙofofinsu suna da wata
munasaba da ta sa aka raɗa masu suna. Haka abun yake anan garin Gusau ƙofofin
namu sun samu ne sanadiyyar wasu dalilai. Dalilin da yasa ake kiranta da wannan
suna Ƙofar Dokau saboda samun wani gari da ake kira Dokau shiyasa ake kiranta
da wannan suna Ƙofar Dokau.
Taswirar
Ƙofar Dokau
9. ƘOFAR GOJE
Abdulmalik
da Gusau (2019: 113), kamar yadda muka yi wannan bincike akwai wannan ƙofa ta
Goje, amma cikin binciken da muka yi ba mu samu tabbacin inda wannan ƙofa take
ba. Bayan haka kuma duk mutanen da muka tuntuɓa suna faɗa mana cewa Gusau tana
da ƙofofi har guda tara (9) amma ba su san inda muhallin wannan ƙofa take ba,
saboda haka wannan ƙofa mutanen mu saboda sakaci da riƙon sakainar kashi
tarihin wannan ƙofa ya kucce masu. Dan haka a iya binciken da muka yi bamu samu
tabbacin inda wannan ƙofa take.
Dukkan
waɗannan ƙofofi an yi su ne domin tabbatar da tsaro a garin Gusau. Haka kuma
dangane da kulawa da ake yi daga mahara akwai wata hasumiya da ake amfani da
ita domin hango mahara, wasu kuwa suna tsaron ƙofofin idan na saman hasumiyar
suka hango ayari ko runduna tafe, musamman mayaƙa, sai su buga ƙugen yaƙi domin
sanar da sauran jama'a, su kuwa 'yan dakon da suke a bakin ƙofa suke da alhakin
buɗewa ko rufewa ga duk wani baƙo da zai shigo a cikin garin, domin kare
barazanar 'yan samame da mahara. Haka kuma duk wanda almuru ta yi masa a wajen
bakin ƙofa to ba zai shiga garin ba sai gari ya waye.
Kafin
zuwan Turawan mulkin mallaka sarakuna sune gaba wajen yin ayuka, kai tsaye a
matsayin shuwagabanni a masarautunsu. Don haka suke da hakkin tabbatar da
tsaro, ke nan su ne wuƙa su ne nama a wannan ɓamgaren. Haka su ke ba da muƙamai
kamar Dakarai ko Jarumai da ke ƙarƙashinsu domin su ba da kulawa da kuma kariya
ga al'umma, da dukiyoyinsu, dama gari baki ɗaya.
Irin waɗannan
mutane da ke aiwatar da tsaro su ne kamar haka:
1- Mayaƙa
/ Dakarai
2-
Sarkin Dogarai
3-
Sarkin Yaƙin Dogarai
4-
Galadiman Dogarai
5-
Madawakin Dogarai
6-
Ciroman Dogarai
Yusuf
Wada da wasu (2014 : 17), sun bayyana cewa, duk waɗannan dogarai da aka zayyana
babban aikin su, shi ne bayar da cikakkiyar kariya da tsaron lafiyar sarki, da
wani abu ya samu sarki gara su rasa rayuwarsu, haka kuma waɗannan mutane suna
da asiri iri daban-daban saboda ƙoƙarin kulawa da sarki, sannan sauran dogarai
sukan zagaya a cikin gari domin kula da irin abubuwan da ke faruwa a cikin
gari, ma'ana suna kwantar da duk wata hayaniya, da sasanta tsakanin talakawa,
da kuma kawo rahoto ga sarki, a kan irin abubuwan da su ke faruwa a cikin gari.
4.2.2 MAKAMAN DA AKE AMFANI DA SU
Dangane
da kayayyakin da ake amfani da su a garin Gusau, a wancan lokaci, akwai
kayayyaki da dama da ake amfani da su, domin tabbatar da samun zaman lafiya a
cikin al'umma da dukiyoyinsu, da kuma kare martabar gari.
Daga
cikin irin waɗannan kaya sun haɗa da:
1-
Mashi
2-
Gariyo
3-
Tsikata
4-
Majaujawa
5-
Kibiya
6- Baka
7-
Kwari
8- Adda
9-
Takobi
10-
Gora
11-
Sanda
12-
Kulki
13-
Garkuwa
14-
Sulke
15-
Kwalkwali
Waɗannan
su ne kayan da ake amfani da su domin kare martabar gari, haka kuma dogarai kan
yi amfani da bulala a wajen ayukansu na yau da kullum a cikin garin Gusau.
Adda
Takobi
Gora
Tsikata
Kwari
Baka
Kibiya
Mashi
4.3 YANAYIN TSARO NA ZAMANI
Yusuf
Wada da wasu (2014:19), a cikin kundin bincikensu mai taken "yanayin tsaro
jiya da yau a garin Ɗandume. Sun bayyana cewa, a yau (wato wannan zamani) yadda
ake gudanar da tsaro ya sha bamban da yadda ake gudanar da shi a da, saboda
tsaro a yau ya ta'allaƙa ne kacokan a hannun gwamnati (ma'ana a irin mulki na
zamani) domin a yau gwamnati ita ce ke da wuƙa da nama a wajen gudanar da aikin
tsaro.
Kamar
yadda muka sani cewa ana gudanar da tsaro ta amfani da ma'aikatan tsaro da
gwamnati kan ɗaukar aiki, musamman don haka. Irin waɗannan ma'aikata sun haɗa
da 'yan sanda da sojoji da sauran ma'aikatan tsaro. Su ne waɗanda gwamnati kan ɗauka
kuma take biyansu albashi, domin su tabbatar da bin doka da kuma tabbatar da
tsaro a garin Gusau.
Haka
kuma ana gudanar da tsaro ta hanyar amfani da sarakunan gargajiya. Haka kuma
dogarai amfaninsu ya tsaya ne ga tsaron sarakunan gargajiya. Su kansu sarakunan
ana amfani da su domin tsawata wa mutanensu idan buƙatar hakan ta taso domin
kuwa har yanzu ana girmama sarakuna a garin Gusau. Haka kuma ƙungiyoyin
'yansakai suna taka muhimmiyar rawa ta fuskar tsaro a yau. Irin waɗannan
ƙungiyoyin sun haɗa da 'yanbanga (Vigilante) da masu gadi. Haka kuma masu kuɗi
kan taimaka, wa irin waɗannan ƙungiyoyin na 'yansakai da kayan aiki kamar su
takalma da fitilu da kayan saƙi (Uniform) da sauran abubuwan da suke buƙata.
Kasancewar
gwamnati ke da wuƙa da nama a harkar tsaro a yau, takan yi ƙoƙarin samar da kayan
aiki irin na zamani tare da kulawa da jami'an tsaro don tabbatar da cikakken
tsaro ga al'umma da dukiyoyinsu, ta kuma samar da duk wani abin da jami'an
tsaro ke buƙata ta fuskar aikinsu tare da kulawa da jindaɗinsu domin su samar
da cikakkiyar kariya ga al'umma daga duk wata barazana da ka iya tusgowa ta
fuskar tsaron lafiya da dukiyoyi.
A yanzu
akwai tsaron iyakar garin Gusau wanda wasu nau'o'in jami'an tsaro ke gudanarwa.
Aikinsu shi ne kula da masu shiga da fice (Immigration Service), kamar yadda
aikin Sarkin ƙofa yake a da. Sannan akwai kuma masu kula da shige da ficen kaya
(Custom) domin hana miyagun kaya shigowa kamar ƙwayoyi a cikin garin Gusau.
Bayan haka kuma gwamnati kan raba ayyukan tsaro zuwa sassa daban daban don
sauƙaƙa aikin tsaro, kamar turasu a Unguwanni daban-daban da ke a cikin garin
Gusau.
A garin
Gusau a wannan zamani akwai masu gudanar da aikin tabbatar da zaman lafiya iri
daban-daban da suka haɗa da jami'an tsaro na gwamnati, da kuma na 'yansakai, da
suke aikin tabbatar da tsaro ga rayuka, da dukiyoyin al'umma, da shuwagabanni
baki ɗaya.
Misalin
irin waɗannan jami'an tsaro sun haɗa da:
1-
Yansanda
2-
Yanbanga
3- Masu
gadi
4-
Sojoji
5-
Hukumar kula da haɗura
6-
Dogarai
7-
Hukumar hana shigowa da miyagin ƙwayoyi da fataucinsu
8- Masu
kula da shige da ficen kaya
9- Masu
kula da shige da ficen mutane
10.
Hukumar (Civil defence)
11.
'Yan ƙato da gora.
Da
sauransu.
4.3.1 KAYAN DA AKE AMFANI DA SU.
A yau kayan aikin da ake amfani da su, a
sha'anin tsaro sun sha bamban da waɗanda ake amfani da su a lokacin da, wannan
kuwa ya faru ne saboda irin cigaban da ake samu a Duniya ta fuskar kimiya da
fasaha. Kayan da ake amfani da su a yau suna da yawa, amma ga kaɗan daga cikin
su.
1-
Motoci
2-
Babura
3-
Bindigoge
4-
Barkonon tsohuwa
5-
Ankwa
6- Wayar
tangaraho
7-
Dabbobi (Irin su karnuka da dawaki)
8-
Makami mai linzami.
Da
sauransu.
4.4 SU WA YE 'YAN TA'ADDA?
Hibbatullahi
da wasu (2014 : 27), a cikin kundin bincikensu mai taken "Nazari a kan
matsalolin da ke haifar da ta'addanci a unguwar Sabon Fegi Gusau. Sun yi
bayanin cewa 'yan ta'adda su ne waɗanda ke tayar da zaune tsaye, ta hanyar
tashe-tashen hankulla a cikin al'umma, wato ta hanyar yin faɗace-faɗace ko kawo
rikici a cikin al'umma. Su waɗannan 'yan 'ta'adda, sukan iya tayar da tashin
hankali ne haka kawai ko kuma kawo rikici na siyasa a cikin al'umma da
sauransu.
4.4.1 IRE-IREN 'YAN TA'ADDA
1.
Akwai 'yan sara suka
2.
Akwai 'yan bindiga daɗi
3.
Akwai 'yan fashi da makami
4.
Akwai masu yaɗa kayan shaye-shaye
5.
Akwai ɓarayi masu ƙwace
6.
Akwai masu garkuwa da mutane
Da
sauransu.
4.4.2 AYYUKAN 'YAN TA'ADDA
Ba za a
rasa wasu ayyuka da 'yan ta'adda ke yi ba, musamman ayyuka marassa kan gado
wato ayyuka marassa kyau a harkokinsu na yau da kullum a cikin al'umma. Misali:
idan 'yanta'adda suna jin yunwa sukan fito farauta a cikin gari lungu da saƙo,
haka kuma, duk wanda suka samu yaro ko babba za su ƙwace abin da ke hannunsa,
misali abinci ne ko kuɗi ko kuma wayar hannu.
Misalin
ayyukansu sun haɗa da:
1.
Sace-sace
2.
Sare-sare
3.
Buge-buge
4.
Shaye-shaye
5. Da
kuma aikata fyaɗe ga mata.
Da
sauransu.
4.4.3 ABUBUWAN DA KE HAIFAR DA TA'ADDANCI
1. Rashin kyakkyawar tarbiyya
Yusuf
Umar Auta (2021). Wannan kusan ana iya cewa yana ɗaya daga cikin dalilan da
suka hardasa wannan baƙar ɗabi'a shi ne babban dalili da ke saka matasa a cikin
sha'anin harkar ta'addanci. Sau da yawa yaro zai taso a gaban iyayensa sai su
saka masa ido ba su kula da tarbiyyarsa ko don gudun ɓacin ransa ko don nuna
soyayya ga yaran. Wannan lamari na rashin kula da tarbiyya yara shi ke sa idan
yara suka girma suka zama matasa ba su tsoro ko shakkun kowa, kuma sai su
aikata abin da suka ga dama.
Irin
wannan lamari iyaye ne suke yin ko - oho ga lamarin kula da yaransu, wato ba su
kai su makarantu kamar na addini da na zamani kuma ba su tsawatawa idan yaran
suka aikata abin da ba daidai ba. Idan kuwa iyaye ba su tsawata na yaro ba,
saboda lalacewar tarbiyyar yaro zaka tarar baya ganin girman iyayensa ban
lantana yaga girman kowa idan suka tashi aikata wani abu ko da ba mai kyau ba
ne. Saboda haka da wannan lamari na rashin tarbiyya yana daga cikin dalilan da
suke hardasa wannan lamari na ta'addanci.
2.
Jahilci
Hussaini
Muhammad (2020). Dalilin da yasa nace jahilci shi ke kawo ta'addanci a cikin
al'umma, saboda duk inda aka ce al'umma ta rasa ilimi to tabbas wannan al'ummar
ta gurɓata. Ba wani jindaɗi da zai wanzu a cikin wannan al'ummar saboda bata da
ilimin da zata yi amfani da shi don gyara al'umma a kan tafarki mai kyau,
jahilci yana da illolin da dama da suke zama barazana a wajen al'umma baki ɗaya
tun daga matasa dattawa da sauran al'umma baki ɗaya.
3.
Shaye - shayen miyagun ƙwayoyi
Alkali
Bashir Mahe (2020). Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi yana daga cikin dalilan da
suke hardasa ta'addanci. Saboda idan muka lura za mu ga cewa, ba kowa ne zai iya
aikata wani aiki na ta'addanci a bainar jama'a ba, ba tare da ya kawar da
hankalinsa ba. Sheye - shaye wani lamari ne na shan kayan barasa (maye) don
kawar da hankalin wanda yasha. Haka kuma shaye-shaye yana iya zama wani yanayi
na shan ƙwayoyi ko sinadari da zai kawar da hankalinsa ɗan wani lokaci, wannan
yanayi na shan kayan maye domin kawar da hankali da aikata wani abu mararsa
kyau galibi matasa ne ke yinsa, kuma sukan sha kayan mayen ne idan za su aikata
wani lamari na ta'addanci kamar sare - sare ko zage - zage ko tashin hankalin
jama'a. Matasa kan sha kayan maye da suka haɗa da:
Giya
Sholisho
Ƙwaya
Babba
juji
Tabar
wiwi
Bidar
ibilis
Roci
4.
Rashin adalci
Hamisu
Halliru (2021). Rashin adalci, idan muka diba za mu ga cewa, hukuma ita kanta
tana daga cikin manyan dalilan da suka sanya matasa cikin lamarin ta'addanci.
Hukuma ta bayar da gagarumar gudummawa wajen samar wa ta'addanci gindin zama a
cikin al'umma, saboda gazawa wajen samar wa matasa aikin yi da kuma yi masu
hukuncin da ya dace a lokacin da suka aikata aikin ta'addanci. Rashin adalcin
da hukuma ke yi wajen hukunta wanda ya aikata ta'addanci sai a sake shi da
zaran aka ba su kuɗi. Wani lokaci kuma sai a gaya ma jami'an tsaro cewa yaron
manya ne, su sa ke shi ko a raba su da aikinsu. Wannan duk sakacin hukuma ne da
take da shi wajen hukunta mai laifi, kuma wannan yana ƙara wa yaran ƙwarin
guiwar sake aikata mummunan ta'addanci.
4.4.4 KALMOMIN ‘YAN TA'ADDA
'Yanta'adda
Kamar yadda muka sani cewa ba za a rasa wasu kalmomi da suke amfani da su ba, a
matsayin ɓad da sau. Su na amfani da salon magana ko, karin magana ko, kuma
zaurance haka kuma idan muka duba yadda ilimin ma'ana ya ke zuwa da kalmomi
masu sarƙaƙƙiya ta yadda dole sai an walwala ma'anar wannan kalma.
Misalin
irin wannan kalmomin da suke amfani da su, sun haɗa da:
1- (An
kar - an kar) ana nufin a kiyaye.
2- (Ga
lakwaye na tafe) idan aka ga jami'an tsaro tafe.
3-
(Ayya dai - ayya dai) idan aka ga wayar hannu ko kuɗi ga wani.
4-
(Hanya ba kyau) idan an fita nema ba a samo ba.
5- (Tir
- tir) idan an fizge abun wanda aka
sani.
6-
(Hanya dai kaɗo) idan an hango wani baƙo tafe.
7- (Ba
gashi ba) idan ana son a canza labari.
4.4.5 ILLOLI DA AYYUKAN TA'ADDANCI YA
HAIFAR A GARIN GUSAU
Malam
Rabi'u Aliyu Dangulbi (2021). Ayyukan 'yan ta'adda sun haifar da illoli da dama
a cikin garin Gusau, musamman babbar illa ita ce: muna ji muna gani akwai
unguwanni da yawa a cikin garin Gusau wanda illar ta'addancin da ake yi ya
haifar da sa tsoro a cikin zukatan al'umma, al'umma ba su shiga irin waɗannan
unguwanni muddun suna da abu ga hannun su.
Misalin
irin waɗannan unguwanni.
1-
Tudun Wada Awala
2- Yar
mangorora
3-
Bulunku
4-
Tulluƙawa
5-
Sabon fegi
6-
Tudun Faila
7-
Shiyar Kongo
8- Hira
da Kwaɗɗi
9.
Sinami
10. Yar
Ɗorayi
Misali:
Nura
Mu'azu (2020). Unguwar Tudun Wada Alwala; irin wannan Unguwa matsalar
ta'addanci ya haifar da sa tsoro da fargaba a cikin zukatan al'umma, irin
wannan Unguwa, baka da ikon shiga daddare, saboda irin yadda 'yanta'adda suke
ƙwace wayar hannu da kuɗi ga hunnan al'umma.
Haka
idan muka diba Shiyar Bulunku da ke a cikin garin Gusau, irin wannan al'umma ba
sa son mu'amala a cikin wannan Unguwa, illar ta'addanci yasa al'umma cikin
fargaba da sanya tsoro a cikin zukatan al'umma, wannan Unguwa mutane ba sa son
shigarta musamman da daddare, domin ana tare mutane ana ansar kuɗi da wayar
hannu da kuma garkuwa da mutane.
Haka
idan muka diba illar ta'addanci ya haifar da sa tsoro da fargabar aje abin hawa
wato mashin
Ibrahim
Mahe (2020). Rashin tsaro a cikin garin Gusau, ya haifar da taɓarɓarewar
kasuwanci a cikin garin Gusau, za a tarar da shagona a rufe da ƙananan
Kasuwanni a rufe, a kan matsalar da ke faruwa ta, ta'addanci a cikin wannan
gari na Gusau.
Haka
kuma, illar ta'addanci ya haifar da durƙushewar ilimi a cikin garin Gusau,
musamman irin yadda aka rufe makarantun sakandare da Furamare, yara su na zaune
a gida su na zaman banza zaman kashe wando, muna roƙon Allah ya kawo muna zaman
lafiya mai ɗorawa.
4.5 MATSALOLIN DA TSARO YAKE FUSKANTA
WAJEN AL'UMMA DA JAMI'AN TSARO
Ba za a rasa samun wasu matsaloli ba, da ke
tasowa idan ana so a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali
Misali
Abdulrazak
Bello Kaura (2020). Cin hanci da rashawa; irin wannan matsala kan daƙushe
harkar tsaro harma yakai ya kasa cimma gurinsa, cin hanci kan haifar da matsaloli
da dama, ta fuskar aikin yansanada da sauran jama'an tsaro da suka karɓi kuɗi
don ƙyale masu laifi suci karansu babu babbaka.
Yusuf
Wada (2014 : 26). Rashin bayar da kyakkyawar kulawa ga wanda ya jikita ko ya
rasa rayuwarsa a wajen aikinsa; mafi akasari gwamnati nayi da kaine idan kana
da lafiya da zarar an ce ka naƙasa to shi ke nan sai ajefar da kai, an riga
anci muriyar ganga, haka ga iyalan wanda ya rasa rayuwarsa a wajen gudanar da
aikinsa da zarar aka ba su kuɗin sallama shi ke nan babu wani tallafi da za a
sake ba su.
Matsalar
rashin muhalli. Wani lokaci aikin kantaso da za a nemi ma'aikaci da gaugawa,
amma saboda inda yake zaune ba kusa da wajen aikinsa bane zai yi wuya a samu
damar haɗa ma'aikata fiye da goma a cikin ɗan ƙan ƙanin lokaci. Haka kuma akwai
4.6 RAWA DA JAMA'A KE TAKAWA WAJEN KAWAR
DA AYYUKAN TA'ADDANCI
Al'umma
na iya ƙoƙarinsu na wajen ganin al'ummar garin nan ta gyaru, musamman idan muka
diba ƙoƙarin da iyaye keyi wajen tabbatar da al'umma sun samu kyakkyawar
tarbiya.
1. Kai
rahoto ga jami'an tsaro a lokacin da abun yake faruwa
2.
Iyaye sukan kira ɗiyansu domin ba su shawarwari tare da yi masu nasiha
3. Haka
kuma a kan samar masu da aikin yi kamar turasu a gona da samar masu sana'a
domin hana su zaman banza.
4. Haka
kuma malamai sukan taka rawa wajen ganin an samu nagar tacciyar al'umma.
5. Haka
kuma akwai Hakimi da mai Unguwa da dattawan Unguwa, da limamai su kan taka rawa
wajen ganin al'umma sun samu kyakkyawar tarbiyya.
6. Daga
ƙarshe kuma akwai hukuma mai zaman kanta domin kawar da ɓata gari a cikin garin
Gusau. Kamar hukumar Hizba.
4.6.1 RAWA DA HUKUMA KE TAKAWA WAJEN KAWAR
DA AYYUKAN TA'ADDANCI
Hukuma
ta kan bi hanyoyi da dama wajen ganin ta ɗauki mataki ga ayyukan 'yan ta'adda
domin tabbatar da samun zaman lafiya a cikin gari Gusau. Da farko dai hukuma ta
kan bi hanyoyin samar da kayan aiki ga ma'aikatan tsaro, domin su gudanar da
aikin su yadda ya kamata, haka kuma hukuma ta kan ɗauki matakin hana kai ma
'yan'ta'adda miyagun ƙwayoyi irin na shaye-shaye, da kuma ɗaukar matakin duk
wanda aka kama da makami a hannun shi za a kamashi, bayan haka hukuma ta kan bi
hanyoyin tura jami'an tsaro a cikin gari, domin tabbatar samun kwanciyar
hankali, tare da tura 'yan leƙen asiri a cikin unguwanni daban-daban, domin su
sanya ido ga al'umma, haka kuma hukuma ta kan ɗauki matakin duk wanda zai shigo
cikin garin Gusau, sai an bincike shi, ina ya fito kuma ina zaya tafi, sannan
kuma suna binciken kayan da aka ɗauko a cikin mota. Hukuma ta kanbi hanyoyi da
dama, domin ganin an tabbatar da samun tsaro a cikin garin Gusau, daga ƙarshe
kuma hukuma ta kan taka rawa wajen bayar da shawarwari ga matasa da kuma
al'umma baki ɗaya.
4.7 MUHIMMANCIN TSORO A GARIN GUSAU
Tsaro
shi ne ginshiƙin duk wani cigaba, domin kuwa babu wani cigaba da za'a iya samu
idan har akwai fargaba a zukatan 'yan gari. Haka kuma ta hanyar tsaro ne
gwamnati ta ke tabbatar da abin doka ga 'yan gari, sannan yana daga cikin
ma'aunin da ake auna cigaban gwamnati da ta samu ko akasin haka, ta hanyar
tsaro ne a yau ake kare lafiyar 'yan gari, ta hanyar hanasu shaye-shaye na
miyagun ƙwayoyi. Haka kuma ana kula da irin kayan da ake shigowa da su a cikin
gari, ta haka gwamnati kan samu kuɗaɗen shiga ta hanyar tsaro, domin akwai
harajin da ake sanyawa, a wasu daga cikin sana'o'in kayan da ake shigowa da su,
sannan daga baya a baka izinin shiga gari.
Haka
nan ma yakan kawo haɗin kai ga ma'aikatan tsaro, domin kuwa sukan zama
tsintsiya maɗaurinki ɗaya a kowa ne lokaci don tabbatar da aikin su. Haka nan
ta hanyar tsaro, jama'a da dama sun sami
aikin yi, domin kuwa a yanzu a kan bayar da albashi ne ga dukkan ma'aikatan
tsaro, wanda hakan ya taimaka wajen hana zaman banza a cikin al'umma.
4.8 NAƊEWA
Kamar
yadda muka kammala wannan babin, ya fara ne da gabatarwa tare da bayani a kan
yanayin tsaro na gargajiya da na zamani, haka kuma an kawo ire-iren 'yan ta'adda da kuma abubuwan da ke
haifar da ta'addanci, da kuma irin kalmomin da 'yan ta'adda ke amfani da su,
domin sakaya zancen su na yau da kullum, da illolin da ayyukan ta'addanci yake
haifarwa, haka kuma an bayyana irin matsalolin da tsaroyake fuskanta da, kuma
bayani a kan irin rawar da al'umma da hukuma ke takawa wajen ganin an magance
matsalar ta'addanci a garin Gusau daga ƙarshe kuma an kawo muhimmancin tsaro a
garin Gusau.
BABI NA BIYAR
SAKAMAKON BINCIKE:
5.0 GABATARWA
A
wannan babi na biyar, mai taken sakamakon bincike, za a duba muhimman abubuwa
kamar haka: Sakamakon bincike, Ta’arifin wasu kalmomi na (Rataye), da
shawarwarin da za a kawo da suka shafi wannan bincike.
5.1 SAKAMAKON BINCIKE
A
wannan babi za a yi bayani ne a kan sakamakon da aka samu a wannan bincike da
aka gudanar. Sakamako yana nufin abun da aka gano sanadiyar wani bincike da ake
gudanarwa ko gwaji (Asibiti ko makaranta). Sakamakon bincike a fagen ilimi yana
nufin abun da wani malami ko ɗalibi ya gano ko masana suka gano wajan wani
bincike da suke gudanarwa. Wannan bincike da aka gudanar an gano abubuwa muhimmai kamar haka:
1. A
cikin wannan bincike da aka gudanar an gano cewa yanayin tsaro ya samo asali ne
daga sarakunan gargajiya, tun a lokacin da.
2.
Wannan bincike ya gano cewa a da, sarakuna su ke da alhakin samar da tsaro ga
al'ummarsu.
3. Haka
kuma a yayin gudanar da wannan bincike an zaƙulo wasu keɓaɓɓun kalmomi da yan
ta'adda ke amfani da su domin kawar tunanin jami'an tsaro ko jama'a.
4. Bugu
da ƙari wannan bincike ya gano wasu tsofaffin ƙofofin garin Gusau, waɗanda ake
amfani da su a da wajen tsare garin.
5. Haka
kuma binciken ya bayyana irin matakan da al'umma ke bi wujen ganin an magance
yaduwar ayyukan ta'addanci.
6. Duba
da kutsen zamani kuwa, binciken ya gano cewa a yanzu yanayin samar da tsaro ya
koma a hannun jami'an tsaro da wasu hukomi.
7. Har
ila yau binciken ya bayyana irin yadda jami'an tsaro su ke jajircewa wajen
ganin an kawar da yaɗuwar ayyukan ta'addanci, tare da samar da tsaro ga
al'umma.
8. Haka
kuma wannan bincike ya gano garin Gusau, a lokacin da tana da ƙofofi har guda
tara, amma saboda rikon sakainar kashi da kuma sakaci da sukayi wa ƙofa guda
(1), ta ɓace ba a san inda mazaunin wannan ƙofa take ba.
5.2 RATAYE
A
wannan ɓangaren za a kawo ta’arifin wasu kalmomi na rataye, keɓaɓɓun kalmomi na
nufin wasu kalmomi ko alamomin magana da wasu ƙungiyoyi ko mutane ke amfani da
su wajen gudanar da harkokin su na yau da kullum.
1.
Tsikata; wato gitta wata abu ce mai kamar gatari, sai dai ita tsikata tana da
tsini daga bayanta, a gabanta kuma tana da faɗi, ita ma ana amfani da ita wajen
sara ko suka.
2.
Gariyo; ƙarfe ne mai kama da lauje yana da lankwasa a gaba kuma yana da kaifi
daga waje, shima ana amfani da shi waje sara ko jan wuyan abokan gaba.
3.
Majaujawa; wata igiya ce da ake sakawa takaba ana ƙullata cikin hikima sai ayi
mata gurbi da za a iya sanya dutsi domin yin jefa mai nisa.
4. Baka
; wato kibau, wani abu ne mai lankwasa wanda ake ɗaurawa igiya mai ƙwari, ana
amfani da shi wajen harba kibiya.
5.
Garkuwa; wani makari ne da ake yi da fata ko kuma baƙin ƙarfe wanda ake amfani
da shi domin kare sara ko suka, musamman a harbin kibiya, ko sukar mashi, ko
sarar takobi.
6.
Sulke; wata riga ce, ta saƙa a kan sanyata a jiki, domin tare sara ko sukar
jikin mutum.
7.
Gora; wani icce ne da ake shukawa yana da ƙullutu a ƙasansa, ana amfani da shi
wajen yin duka.
8.
Takobi; wani dogon ƙarfe ne mai kama wuƙa, sai dai shi yafi wuƙa tsawo, yana da
kaifi ciki da waje, mafi akasari ana yin sa ne da farin ƙarfe.
9.
Mashi; wani ƙarfe ne dogo mai tsini daga saman sa, ana amfani da shi wajen suka
ga abokan gaba, a fagen yaƙi.
5.3 SHAWARWARI
Shawara
ba a fagen bincike kaɗai take ba ko a harkokin mu na yau da kullum tana da
mutuƙar muhimmanci ɗari bisa ɗari. Wannan ne muka ga yakamata a matsayin mu, na
ɗalibai da muke gudanar da wannan bincike na yanayin tsaro a garin Gusau, domin
mu isar da shawarwarin mu ga masana da ɗalibai, da malamai, da gwamnati, da
ƙungiyoyin tsaro, da manazarta al'ummomi da ke gudanar da aikin tsaro.
1.
Yakamata hukumar jami'an tsaro ta ƙara ƙyami wajen sa ido ga jami'anta domin
ganin sun gudanar da ayyukansu yadda yakamata.
2. Haka
kuma iyaye su bada kyakkawar kulawa ga ƴaƴansu, tare da basu tarbiya da ilimin
addani da na boko.
3. Har
ila yau gwamnati yakamata ta samar da ayyukan yi ga matasa, domin magance zaman
kashe wando wanda shi ne ummul aba isin ayyukan asha.
4.
Iyayenmu sarakuna na da rawar da su ke iya takawa wajen ganin a magance yaduwar
ayyukan ta'addanci ta hanyar amfani da wasu daga cikin sarautu na gargajiya
kamar: sarkin samari, sarkin baki, da ƴan rahoto/ ƙamshin gari.
5. A
karshe yakamata gwamnati ta yi amfani da yan banga da duk wani wanda yake iya
taka rawar a zo a gani wurin ganin an magance ayyukan ta'addanci, ta hanyar yi
masu ihisani.
5.4
NAƊEWA
A
taƙaice wannan babi ne na kammalawa yana ɗauke da abubuwa kamar haka,
gabatarwa, da sakamakon binciken wannan aiki da aka gudanar, da wasu keɓaɓɓun
kalmomi na (Rataye) da shawarwarin da suka dace da wannan aiki.
MANAZARTA
Aminu,
A da Gusau, M. I (2019) "Hasken Masarauta: Rayuwa
da zamanin Mai Martaba Sarkin Katsinan
Gusau na Tara (9)" Kano:
Century Research and Publishing
Limited.
Abubakar,
A. T. (2015)"Ƙamusun Harshen Hausa"Zaria: NNPC LTD.
Bunza,
A.M (2006) Gadon Feɗe Al’ada. Lagos:
Surulere Tiwal Nigeria Ltd.
Bunza,
A.M. (2017) DABARUN BINCIKE (A Nazarin Harshe Da Adabi Da
Al’adun Hausawa)
Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.
CNHN (2006)"Ƙamusun Hausa "Kano:
Jami'ar Bayaro
Gusau,
A. R (2014) "Mai Dubun Nasara: Rayuwa Halaye
Saƙonni: da Jawabin Mai
Martaba." Gusau: Al-Hudah Ventures.
Gusau, B.M,
Gusau S.M (2012),Gusau ta malam Sambo Benchmark
Publishers. Limited KanoNigeria.
Hassan,
M. B (2019) Kadaura: Journal of Hausa
Multi Disciplinary Studies.
Vol. 1, No. 5 September, 2019.
Hibbatullahi,
dawasu (2014).Nazari AKan Matsalolin Dake Haifar Da
Ta'addanci: ASashen
Hausa, Tsangayar Harsuna, Kwalejin Ilimi Da Ƙere Ƙere, Ta Gwamnatin Tarayya, Gusau
Jihar, Zamfara.
Nalado, A.M (b.she) Kano State Jiya Da Yau
AD.999. 1864 - 1968; Zaria:
Gaskiya Cooperation.
Yusuf,
Wada, da wasu (2014). Nazari a kan Yanayin Tsaro Jiya Da Yau
A Garin Ɗandume. Sashen Hausa Kwalejin
Kimiyya da Fasaha:
Zacas, Gusau Jihar Zamfara.
Shekarau,
M.I (2007) Role of Government in Security of Life and property;
Presented at Ladi Kwalli Hall,
Sheraton Hotel & Towards, Abuja.
MUTANEN
DA AKA YI HIRA DA SU
1.
Abbas Mu'alleɗi, lauyan gwamnati mai shekaru 43, hirar da anka yi da
shi ranar 03/03/2020, a gidansa da
ke Gada Biyu Gusau, da misalin
ƙarfe 10:00am.
2.
Abdulrazak Bello Kaura shugaban 'yan jarida na jihar Zamfara, mai
shekaru 42, hirar da anka yi da shi
ranar 13/03/2020, a wurin aikinsa
da ke "FM Radiyo Gusau".
Da misalin ƙarfe 11:30am.
3.
Abdulmajid Umar Galadima, mai shekaru 41, hirar da anka yi da shi ranar
15/03/2020, a wurin zaman shi da ke
Kanwuri Gusau, da misalin
karfe 5:15pm
4.
Aliyu Rufa'i Gusau, hirar da anka yi da shi ranar (20/03/2020), a
mazaunin shi da ke Kanwuri Gusau, da
misalin ƙarfe 9:20am
5. Abdulhamid A Baba mai shekaru 61, hirar da anka yi da shi ranar
23/03/2020, a mazaunin
shi da ke Unguwar Toka Gusau, da misalin
ƙarfe 6:00pm.
6.
Abdulrahman Abdullahi, mai shekaru 35, hirar da anka yi da shi ranar
17/04/2020, a wurin aikinsa da ke
Tudun Wada Gusau, da misalin
ƙarfe 4:30pm.
7.
Aminu Aliyu, mai shekaru 39, hirar da anka yi da shi ranar 19/04/2020, a
gidansa da ke Sabuwar Gusau, da
misalin ƙarfe 10:00am.
8. Aminu Shehu, mai shekaru 35, hirar da anka yi da
shi ranar 23/05/2020, a
wurin
zaman shi da ke 'Yar Mangorora Gusau, da misalin ƙarfe
9:30am.
9. Alkali Bashiru Mahe, mai shekaru 51, hirar
da anka yi da shi ranar
10/07/2020,
a mazauninshi da ke Unguwar Dallatu Gusau, da misalin
ƙarfe 8:30pm.
10. Bawa Makau, mai shekaru 67, hirar da anka yi da
ranar 26/08/2020, a
gidan sa da ke Tsohuwar kasuwa Gusau 5:43pm.
11. Bello Adamu Dinawa, babban jami'in tsaro na 'yan
sanda, mai shekaru
46,
hirar da anka yi da shi ranar 28/08/2020, a wurin aikinsa da ke
"Central Police Gusau", da
misalin ƙarfe 10:20am.
12. Bello Aliyu Ɗanmaituwo, mai shekaru 73, hirar da
anka yi da shi ranar
05/09/2020, a mazauninshi da ke Tsohuwar Kasuwa Gusau, da
misalin ƙarfe 2:14pm.
13.
Dauda Muhammad, mai shekaru 43, hirar da anka yi da shi ranar
07/09/2020, a wurin gudanar da
aikinsa da ke "Headquarter Gusau",
da misalin ƙarfe 10:23am.
14. Faruk Umaru Auta, mai shekaru 68, hirar da anka yi
da shi ranar
18/09/2020, a mazauninshi da ke Tsohuwar kasuwa Gusau,
da
misalin ƙarfe 10:35am.
15. Garba Abdullahi Aliyu, mai shekaru 71, hirar da
anka yi da shi ranar
25/09/2020, a gidansa da ke Tsohuwar Kwata Gusau, da misalin
ƙarfe 8:20pm.
16. Hassan Muhammadu Ɗanmairi, mai shekaru 68, hirar
da anka yi da shi
ranar 13/10/2020, a gidansa da ke 'Yar shararra Gusau, da misalin
ƙarfe 5:10pm.
17. Hussaini Muhammad, babban jami'in tsaro na 'yan
sanda, mai shekaru
43, hirar da anka yi da shi ranar
26/10/2020, a wurin gudanar da
aikinsa da ke "C.I.D Office Gusau", da misalin ƙarfe 2:23pm.
18.
Ibrahim Mahe, mai shekaru 45, hirar da anka yi da shi ranar
24/11/2020, a gidansa da ke Sabuwar
Gusau, da misalin ƙarfe
8:00pm.
17. Ibrahim Gali Tayi, mai shekaru 31, hirar da anka
yi da shi ranar
18/12/2020, a mazaunin shi da ke Ƙofar Jange Gusau, da misalin
ƙarfe
6:34pm.
18. Jabir Yusuf Auta, mai shekaru 44, hirar da anka yi
da shi ranar
23/0/12/2020, a wurin aikinsa da ke "Headquarter Gusau",
da
misalin ƙarfe 2:20pm.
19.
Nura Mu'azu S.P, mai shekaru 43, hirar da anka yi da shi ranar
27/02/2020, a unguwar su da ke Bakin Tsohuwar Kasuwa
Gusau, da misalin ƙarfe 5:17pm.
20. Namadi Sulaiman Muhammad, mai shekaru 76, hirar da
anka yi da shi
ranar 13/01/2021, a mazaunin sa da ke Bakin Tsohuwar Kasuwa
Gusau, da misalin ƙarfe 5:00pm.
21. Mu'azzam Sulaiman, mai shekaru 32, hirar da anka
yi da shi ranar
27/01/2021, a wurin zamanshi da ke Gangaren Kwata Gusau,
da
misalin ƙarfe 5:30pm.
22.
Munnir Abdullahi, wakilin layauka sadarwa na jihar Zamfara mai
shekaru 41, hirar da anka yi da shi ranar 19/03/2021,
a
mazauninshi da ke Bakin Tsohuwar
Kasuwa Gusau, da misalin
ƙarfe 2:43pm.
23. Muhammadu Kabir Sarki, mai shekaru 58, hirar da
anka yi da shi ranar
23/03/2021, a mazauninshi da ke Tudun Wada Gusau, da misalin
ƙarfe 7:23pm.
24. Malam Rabi'u Aliyu Ɗangulbi, hirar da anka yi da
shi ranar 16/04/2021,
a
gidansa da ke Gidan Dawa Gusau, da misalin ƙarfe 5:15pm.
25.
Sani Muh'd babban jami'in tsaro na 'yan sanda mai shekaru 38, hirar da
anka yi da shi ranar 27/04/2021, a
wurin da gudanar da aikinsa, da
ke Central Police Gusau, da
misalin ƙarfe 12:11pm.
26. Sani Madugu, mai shekaru 74, hirar da anka yi da
shi ranar 14/05/2021,
a gidansa da ke Zawiyya Gusau, da misalin
ƙarfe 5:30pm.
27. Sani Ɗankwamma, mai shekaru 69, hirar da anka yi
da shi ranar
14/05/2021, a Unguwar su da ke Zawiyya Gusau, da misalin ƙarfe
5:30pm.
28. Sani Muhammad babban jami'in tsaro na 'yan sanda,
mai shekaru 38,
hirar da anka yi da shi ranar 16/06/2021, a wurin aikinsa da ke
Central Police Station Gusau, da misalin ƙarfe 3:35pm.
29. Surajo Yalwa Sarki, mai shekaru 43, hirar da anka
yi da shi ranar
23/06/2021, a gidansa da ke Bello
Bara'u Gusau, da misalin ƙarfe
5:12pm.
30. Tsalha Musa Bashiru, mai shekaru 67, hirar da anka
yi da shi ranar
18/07/2021, a gidansa da ke Sabon Fegi Gusau, da misalin ƙarfe
4:30pm.
31. Tukur Ibrahim Rahi, mai shekaru 68, hirar da anka
yi da shi ranar
16/08/2021, a gidan sa da ke Unguwar Dallatu Gusau, da misalin
ƙarfe 9:00am.
32. Yusuf Ummaru Auta Gusau, mai shekaru 78, hirar da
anka yi da shi
ranar 20/08/2021, a gidansa da ke Bakin Tsohuwar Kasuwa Gusau,
da
misalin ƙarfe 3:35pm.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.