Ticker

Yaushe Ne Lokacin Sallar Walha?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam, ina so a yi min bayani kan sallar Walha. Sannan yaushe ne lokacin wucewarta? Na gode Allah saka maka da alkairi, ameen.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Sallar Dhuha ita ce Bahaushe ke ce mata "Walha". Kuma ita ce Annabi ﷺ ya yi mata laƙabi da sallar masu tuba (صلاة الأوّابين) a wani hadisi, sannan ita ce wasu malaman suke kiranta da suna Salatul Ishraƙ (صلاة الإشراق), an kira ta da wannan sunan ne saboda sai bayan rana ta ɗago ake yin ta. Kuma sunnah ce ba farillah ba. Amma tana da falala mai girma.

Sallar Walha tana cikin sallolin nafila mafi falala wadda Manzon Allah ﷺ ya yi a aikace kuma ya kwadaitar akanyinta, sunnace mai karfi daga cikin sunnonin Manzon Allah ﷺ da yake kiyayeta hatta a lokacin Bulaguro".

Farkon lokacin sallar Walha yana farawa ne daga lokacin da Rana ta kammala ɗagowa har zuwa kusa da kafin zawali, wato kusa da kafin lokacin Azuhur ya shiga, kamar yadda Sheikh Ibn Uthaimeen da wasu malaman suka kimasta. Duba Assharhul Mumti'u 4/88.

Amma mafificin lokacin sallar walha shi ne kamar yadda Manzon Allah ﷺ ya faɗa cewa:

Lokacin sallar walha lokacin da ‘ya’yan raƙuma suka fara jin zafi ne” Muslim 748. Wato lokacin da rana ta riga ta ɗau zafi.

Lokacin sallar Walha a kasarmu (Nigeria) shi ne daga Karfe 9:00am Zuwa 11:30am Na Safe ne Za ka yi a wannan dan Tsakanin. Ana yinta ne a Lokacin da Akasarin Mutane Suka Gafala Akan Harkar Duniya. Domin a Daidai lokacin ne yan Kasuwa Suke Fita kasuwarsu kuma a irin wannan Lokacin ne Zakaga Yan Kasuwa sun Gafala da harkar cinikayya da kuma saye da Sayarwa, Wasu Kuma Sun Tafi Wajen aikinsu na gwamnati da dai Sauransu.

Ibn Usaimin Rahimahullah Yana cewa: "Sallar walha idan lokacinta ya wuce to ta wuce ba a ramawa domin Sallah ce mai lokaci kayyadadde".

Imamu Maliku Ya Rawaito a Cikin Muwadda cewar Mafi Akasarin Raka'o'inta shi ne 8, ko dai ka yi 2 ko 4 ko 6, idan ka yi da Yawa ka yi Raka'a 8. Amma ba a Wuce Raka'a 8 ɗin. Babu wata Surah da Aka keɓance a karanta a Sallar Walha. Zaka Iya Karanta Kowacce surah.

Kaɗan daga Falalar Sallar Walha Shi ne. Ka Fanshi kanka a Wajen Allah a wannan yinin, zaka sami kusanci ga Allahu Subhanahu Wata'ala, Allah zai Ɗaukaka Darajarka, Uwa Uba Manzon Allah ﷺ Yace SALLAR MUTANEN KIRKI CE, MASU MAIDA LAMIRANSU GA ALLAH KO KACE SALLAR MUTANEN ALLAH.

Manzon Allah ﷺ yana cewa;

(Jikin mutum akwai gabobi guda 360, kuma an ɗora masa yin sadaka akan kowace gaɓa) sai Sahabbai suka ce masa:

"Wa zai iya sauka wannan nauyi ya Manzon Allah ﷺ?" sai ya ce:

(Goge majinar ko kakin da akayi a masallaci, ko ɗauke wani abin cutarwa daga akan hanya, idan kuma mutum bai sami damaba, to ya yi sallah raka'a guda biyu na Walha ya isar masa)

@الألباني رحمه الله ,صحيح الترغيب

Allah ne mafi sani.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments