Ticker

Yaya Matsayin Karbar Magani A Wurin Mai Aiki Da Jinnu?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam da fatan an tashi lafiya, Allah ya sa muna da rabo mai amfani, Don Allah malam, Ina so a kara min haske ne, wata mata ce ta ji wani mutum yana talla gidan radio, yana ba da maganin sihiri da masu aljanu, sai ta cire number shi ta je, to ashe da aljani yake aiki, a nan ne yake fada mata damuwan ta, wai aljani a ka tura mata shi ke saka ta cikin matsalan da take ciki, shin ya halasta ta karbi magani a wajen shi, ko bai halasta ba? Allah ya kara basira.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, ‘yar uwa bai halasta ta karɓi magani a wurin irin wannan mutumi da ke aiki da aljanu don a yi mata maganin aljani ko sihiri ba, saboda wannan hanya ce ta kaiwa zuwa ga shirka, akwai hanyoyi ingantattu da Shari'a ta tanadar don a yi maganin aljanu ko sihiri, idan an tuntuɓi malamai za su ba da bayani.

Kuma an yi wa malaman Lajnah makamanciyar wannan tambaya sai suka ba da amsa da cewe:

"Neman taimakon aljanu ba ya halasta wajen sanin nau'in ciwon da aka kamu da shi, ko wajen yin maganinsa, saboda neman taimakon aljanu shirka ce, Allah Ta'ala ya ce: "Wasu mazaje daga cikin mutane sun kasance suna neman tsari da wasu mazaje daga cikun aljanu, sai suka ƙara masu zunubi"...

Dubi Fataáwál Lajnatid Dá'ima 1/92. (Almajmu'a ta biyu).

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments