Ticker

ZAN IYA JIRA SAURAYINA HAR YA GAMA KARATU, SANNAN MU YI AURE?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum malam tambayata shi ne: shin mace zata iya jiran namiji akan aure ma'ana ita ta isa aure shikuma Yana karatu amusulunce ya halatta tajira shi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh.

To wannan yazama wahalar dakai domin ke kince kin isa aure, muƙaddara kinkai shekara 20, shi kuma yana da shekara 25 kuma yana halin karatu kuma aƙalla da kammala  abin da yasamu dasamun aiki abarshi shekara biyar ataƙaice, babu tabbas ɗin zaisamu aikin ko akasin haka, kinga ke nan kinkai 25 shikuma yana da 30 kuma ahakan ma babu tabbas a lokacin kuma ke kina ganiyar ƙuruciyarki kinada maneman da sunfishi ƙuality amma kince saishi.

Sannan kiyi tunanin zai iya mutuwa akowane lokaci domin bamu da tabbas ɗin zamukai anjima saidai mudinga saka rai, sannan kiyi tunanin zai iya ganin wadda tafiki birgeshi kuma kuma yadaina sonki ƙarshe kin yi zaman banza.

Duk Wanda yazo da niyyar aurenki aka samu duk wata nagarta da ake nema wajan namiji to ina baki shawarar ki aureshi kibar tunanin gaibu, idan kuma har izuwa lokacin baki samu mijin auren ba har ya kammala yatarar dake azaune kuma Allah ya yaƙulla shikenan amma karkisa aranki zaki jirashi domin wannan gurguwar shawara ce wlh, Allah ya haɗa kowa da mazaje nagari.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments