BABBAN RASHI: Ta’aziyyar Marigayi Darakta Nura Mustapha Waye

 Daga taskar sha’iri Sa’adu Malam Auwal, (Ɗanhausa, Zadawa)

BABBAN RASHI: Ta’aziyyar Marigayi Darakta Nura Mustapha Waye

Sa'adu Malam Auwal
(Ɗanhausa Zadawa)

BABBAN RASHI: Ta’aziyyar Marigayi Darakta Nura Mustapha Waye

1.

Ya Kaliƙi abin bauta

Da kai na fara waƙata

Ya Rabbana ka gafarta

Ga Nura Mustapha Waye.

 

2.

Tsira da amincinka

Ya Ilahuna ninninka

Gun Nabiyyu mai Makka

Sahabu har da Ahlaye.

 

3.

Un-uhm um-uhum!

Ga ni damuwa tsundum

Rayuwa ta zam lum-lum

Ya Ilahuna yaye.

 

4.

Mutuwa fa tilas ce

In ta zo ta haƙƙun ce

Ko namiji ko mace

Za ta ɗauke ko waye.

 

5.

Rayuwa ƙalilan ne

Ajali sadidan ne

Ko a tsaye ko zaune

Kan kawar da na raye.

 

6.

Nura yanzu ya tafi

Mustapha maso Khafi

Rabbu kankare laifi

Mun fa ɗaga hannaye.

 

7.

Rabbana ka gafarta

Ga Nura ya fa fafata

Tarbiyya ya inganta

A lokacin yana raye.

 

8.

Cikin shiri na Izzar So

Iliminsa yai naso

Al'umma fa sun kwaso

Kyawuka na halaye

 

9.

Ɗan uwa ka dudduba

Nura bai yi aibu ba

Shirinsa bai yi ɓarna ba

Ba batu na nanaye.

 

10.

Muhammadur Rasulullah

Tambarinsa ne kalla

Sonsa shi ya yo talla

Nura Mustapha Waye.

 

11.

Ya yi ƙoƙari sosai

Bishiyarsa tai rassai

Ga shi yanzu na ƙassai

Ya bi namu iyaye.

 

12.

Da fa ba ni yin kallo

Na Shiri fa ko ƙwallo

Sai da Izza ta ɓullo

Ɓideo na Sufaye.

 

13.

Na ga darasi jingim

An yi bincike tsundum

Ga tafakkuri suntum

Ya fa zarce wawaye.

 

14.

Al'uma fa sun shiryu

Na ga mata har gayu

Darasinka ya koyu

Allah ba ka benaye.

 

15.

Nura ka fitar jari

Kai ka shuka alkairi

Ambatonka Albashari

A zahiri fa har ɓoye.

 

16.

Rabbu don Habibullah

Muhammadur Rasulullah

Ka jiƙansa Nurullah

Laifuka ka sassanye.

 

17.

Rabbu don Al-Arshinka

Domin Kursiyyunka

Ka jiƙansa bawanka

Darakta Mustapha Waye.

 

18.

'Yan uwa ga Nuranmu

Yayu da iyayenmu

Ta'aziyya nake gunmu

'Ya'ya da iyaye.

 

19.

'Yan shiri na Kannywood

Thank you ɓery good

Ta'aziyarku now i would

Do na Mustapha Waye.

 

20.

Ahababu gun Manzo

Mun rashi na mai ƙwazo

Ta'aziyarku na wanzo

Malamai da Sufaye.

 

21.

Ni Sa'adu Ɗanhausa

Kan rashin ga na amsa

Addu'armu mui ta masa

Ga Nura Mustapha Waye.

Post a Comment

0 Comments