Ticker

    Loading......

Ramin Karya

 Saurayinta ya zo gaishe da iyayenta, aka Kai shi wajen tarɓar baƙi. Sun fara hira ke nan, sai ƴar aikin gidan ta kawo musu Lemo da Pizza.

Ya sanya hannu ya ɓantari Pizza ya fara ci. Ta ce, Ka ji daɗinta kuwa? Ya ce, sosai ma kuwa.

Ta ce, Ni nayita, na sha wahala sosai, duk don na burgeka. Umma ce ta kai ni wajen wasu ƙwararru, ta kashe kuɗi masu yawa suka koya mini, kuma fa na koya ne saboda kai kaɗai..!!

Ya ce, wallahi ta yi daɗi sosai, nagode da wannan hidima da kika yi, lalle in na aureki bani da matsalar abinci, na yi murna sosai, tabbas kin ƙware wajen sarrafa abinci...!!!

Bayan ya tafi, ta je ta samu Babarta ta ce, a ina kuka samo Pizza mai daɗi haka? Babarta ta ce, ai saurayinki ne ya kawo ta, shi ne na gutsuro muku.....!!!!😀

Saurayinta ya zo gaishe da iyayenta, aka Kai shi wajen tarɓar baƙi. Sun fara hira ke nan, sai ƴar aikin gidan ta kawo musu Lemo da Pizza.  Ya sanya hannu ya ɓantari Pizza ya fara ci. Ta ce, Ka ji daɗinta kuwa? Ya ce, sosai ma kuwa.  Ta ce, Ni nayita, na sha wahala sosai, duk don na burgeka. Umma ce ta kai ni wajen wasu ƙwararru, ta kashe kuɗi masu yawa suka koya mini, kuma fa na koya ne saboda kai kaɗai..!!  Ya ce, wallahi ta yi daɗi sosai, nagode da wannan hidima da kika yi, lalle in na aureki bani da matsalar abinci, na yi murna sosai, tabbas kin ƙware wajen sarrafa abinci...!!!  Bayan ya tafi, ta je ta samu Babarta ta ce, a ina kuka samo Pizza mai daɗi haka? Babarta ta ce, ai saurayinki ne ya kawo ta, shi ne na gutsuro muku.....!!!! Copied 😀

Post a Comment

0 Comments