Zawan Turawa Katsina Da Irin Tarbar Da Akayi Masu A 1903

 Katsena boasts itself to be the seat of learning of Hausaland. It is probably a more ancient town than even Kano, and is built in the same style. I explained to the king (Sarki Abubakar) the conditions of British suzerainty, which he accepted with apparent cordiality" - Lord Lugard (1903).

Zawan Turawa Katsina Da Irin Tarbar Da Akayi Masu A 1903

Yusuf Lawal Kankia
Makaman Kankiya
(Yulaks Ky)

Katsina Palace

Turawa sun zo Katsina kamar yadda suka je manyan garuruwan Arewa da Ƙasar Hausa. A wasu garuruwan an ja daga, a wasu garuruwan kuma komi ya tahi kodai salun alin ko kuma bisa tilastawa.

Mu a Katsina saboda basira da kuma wayewa tun a wancan lokacin ba'a yarda aka sakan ma Bature fuskar maida mutane bayi ba ko kuma ya mulke su da tsiya. Sannan kuma ba'a yi faɗa dashi ba sai dai akayi mashi karimci aka kuma nuna mashi gogewa da ilimi wadda tasa yaji dadi kuma ya saki jiki sannan har ma ya saki ragamar mulkin ba kamar sauran wurare ba.

 Lokacin da Gwamna Lugga da Jama'ar shi su Sittin suka baro Sakkwato zuwa Birnin Katsina sai Sarkin Katsina Abubakar ya shirya masu tarba ta karimci. Wannan yasa basu yi amfani da wani makami ba kan kowa. Sarkin Katsina ya tarbi Gwamna Lugga Watau Governor, Lord Frederick Luggard tare da tawagar shi. A wannan hoto (pic1) za'a iya ganin daga Hagu zuwa Dama: Governor Lugga, Sarkin Katsina Abubakar, Kauran Katsina Isiyaku, Galadiman Katsina Sallau, 'Yanɗakan Katsina Mani, Marusan Katsina Altine. A layin baya kuma akwai: Durbin Katsina Muhammadu Dikko (Kafin ya zama Sarkin Katsina) sai, Yariman Katsina Abdulkadir, da Baturen Yandoka da sauran wasu.

 

Shi dai Gwamna Lugga ya shigo Katsina ne ta Kofar da ake kira Kofar Yanɗaka (pic2) a ranar 28 ga watan Maris 1903. Wannan ita ce ranar da Turawan Ingilishi suka amshi Katsina.

Daga nan kuma Sarki Abubakar yasa aka kai su masafki. An kai su wani gida da ake kira "Gidan Yarima" (pic3) wanda aka gina shi a shekarar 1809 bayan an gama jihadi. An kuma kara yima gidan gyare gyare a shekarar 1888. Katsina ta burge kwarai yadda ta safkar da Turawan Mulkin Mallaka a gidan da ya burge su har suka yaba. Hakazalika Katsina ta ciri tuta akan yadda ta amshi turawan mulkin mallaka kuma su da kansu suka yaba da tsarin da suka iske a Katsina wanda yake cike da basira. Gwamna Lugga ya yaba da ilimi da kuma kaifin basira da tsari na Katsinawa a wancan lokacin.

Wannan yasa shi kanshi Gwamna Lugga yake cewa:

"Katsena boasts itself to be the seat of learning of Hausaland. It is probably a more ancient town than even Kano, and is built in the same style. I explained to the king (Sarki Abubakar) the conditions of British suzerainty, which he accepted with apparent cordiality" - Lord Lugard (1903).

Allah Ya ƙara ɗaukaka mamu Jahar mu ta Katsina, da Masarautar mu da Kasa baki daya.

Post a Comment

0 Comments