Gudummuwa da
Jaruntakar da Dangaladiman Gobir Malam Alu Dan Sarkin Gobir Yakuba, Kuma
Natsinin Kabi Na Farko Ya Tabbatar A Kasar Kabi
Sardauna Muhammad
Lawal Argungu
Wakilin Daular
Gobir
Shugaban Kungiyar
Gobirawan Nijeria
Reshen Jihar Kebbi
1. Asali da Salsalar Dangaladiman Gobir Malam Alu Dan Sarkin Gobir
Yakuba
Shi dai Dangaladiman
Gobir Malam Alu ɗan Sarkin Gobir Yakuba ne, watau jika ga Sarki Gobir Ibrahim Babari, wanda ya kafa
babban Birnin ƙasar Hausa, watau Birnin Alkalawa. Kuma shi ne ƙane ga Sarkin Gobir Ali ɗan Yakuba na Gawon Gazau, wanda ya yi sarauta a
shekara 1817-1835. Sauran ‘yan’uwansa sun haɗa da: Salihu Mai Kadaye da Mummuni da Bunu ɗan Gazumi da Masari Maikai.
Bayan zumansa Ɗan Sarki, ƊanGaladiman Gobir Malam Alu, kuma Malami ne, domin ya rubuta Alqur’ani mai girma hizo sittin, ƙira’ar Warsh da hannunsa. Haka kuma, Ɗangaladiman Gobir Malam Alu shi ne Natsinin Kabi na farko, tun lokacin Sarkin Kabi Yakuba Nabame, ya yi sarauta daga shekaera 1860-1901.
2. Dalilin Tasowarsa Daga Gobir Zuwa Kabi
A hakikani Gaskiya wannan tarihi baya kammala batareda anyi bayani kan watsewar birnin Kabi wato babban birni na Kabawa bayan tshohon Birnin su na surami.
Watsewar Kabawa daga Birnin
Kabbi, inda suka waste
gida
ukku:
wasu suka yi Dandi, wasu Kebbe, wasu kuma Argungu, amma shi Sarkin Kabbi Yakubu Nabame da Mahaifinsa Samaila Ƙarari, su suka zo Argungu. Amma shi Fulani sun
tafi da shi Sakkwato. Zaman Yakubu Nabame a Sakkwato, sai ya zama kamar Sarkin Yaƙin a gare su, saboda ya san hanyoyin
yaƙi.
Wata rana, Fulllani suka ɗaura yaki zuwa ƙasar Gobir, a lokacin Sarkin Gobir Ali ɗan Yakubu a wurin wannan
yaƙi
ne, Gobirawa suka fahimci akwai wanda ke jifar mashi, wanda ba Bafillatani ba ne. Saboda haka, jarumawan mayaƙan Sarkin Gobir, wadanda aka sani
da suna ’Yankwana. Sai ɗaya daga cikinsu ya yi kukan kura, ya nufi Yakubu Nabame. Koda ya isa
wurinsa, sai ya ganshi ashe ba Bafillatani ba ne, da kuma tsagensa na Kabawa, sai suka zo da shi wurin Sarkin Gobir, a inda Sarkin Gobir Ali ɗan Yakuba, ya tambaye shi sunanansa. Sai Yakubu
Nabame ya ba shi amsa da cewa “sunana Yakuba”. Shi kuma Sarkin Gobir Ali ɗan Yakuba, “ai mai sunan baba ka yi ɓarna, domin mu nan da kake gani darnin gidanmu
muke kariya, idan ka yi zucciya ka je ka tayar da Kabi. Haka kuma, a duk lokacin da ka shirya, a shirye muke mu taimaka maka”.
Tun lokacin da Gobirawa suka yi wa Yakubu Nabame habaici, tun
daga wannan ranar bai sake fita zuwa yaƙi ba, sai tunanin komawa gida, watau ƙasar Kabi.
A lokacin da Yakuba Nabame ya dawo gida, wato Argungu, sai ya
tarar da ‘yan’wansa, Lailabawa, kuma su
ke mulki a lokacin.
Haka kuma, suna ƙarƙashin mulkin Fulanin Gwandu, domin a duk
shekara a Gwandu suke biyan haraji, kuma Kabawa suna kai musu haki na bayabaya.
Saboda haka, A
shekarar da Yakubu Nabame ya dawo gida, sai Fulani suka aiko da cewa, Kabawa su
biya haraji. Shi kuma ya aika musa da cewa, a gaya musu Nabame ya dawo. Don
haka biyan haraji, da kai haki na bay-baya ya ƙare. (A nan ne cikin waƙar Marigayi Aliyu Ɗandawo Shuni yake cewa, ‘bayan shekara dubu biyu, sannan Nabame ya
bayyana, ya fanshi Kabawa, ya gagari Fulani, da ruwan kebo da masu, kun sun yi kulli kulinsu, ina ruwan sadauki, ya dai buwaye ku, bindiga
ai ba ta ƙara tashi). Ana cikin wannan hali ne
sai Sarkin
Kabi ya aika wa
Maigirma Sarkin Gobir cewa, yana yi masa tuni, kuma ya dawo gida.
Saboda haka, sai Sarkin
Gobir ya turo ƙaninsa
Dangaladiman Gobir Malam Alu da ya zo Kabi, domin taimakawa Kabawa, kamar yadda suka yi mass alkwali. Don haka, Dangaladiman Gobir Malam
Alu Dan Yakuba,
ya bar
ƙasar Gobir da dawakai ɗari (100) tare da ’yan ƙasa mutun ɗari biyu da tamanin (280). A lokacin da ya bar Gobir zuwa Kabi, Dangaladiman
Gobir Malam Alu ya yi
sansani a wani wuri da aka sa wa
suna ‘Gobirawa’ a ƙasar Augie. Bayan ya taso zuwa garin Natsini, saboda ƙura ta yawan dawaki, sai mutanen Sarkin Kabi, suka sheda masa cewa, suna ganin alamun an
kawo masu yaƙi. Sai Sarkin Kabi ya amsa da cewa, ba yaƙi ba ne. Yana sane da zuwansu. A lokacin da Dangaladiman
Gobir Malam Alu ya iso garin Natsini,
sai ya aika wa
Sarkin Kabi Yakubu Nabame cewa ya yi
baƙo.
Don haka,
Sarkin Kabi ya je wannan gari na Natsini, inda suka sadu da Dangaladiman
Gobir da ayarinsa. Bayan da Sarkin Kabi Yakubu Nabame ya sadu da Dangaladiman Gobir
Malam Alu da jama’arsa, sa’annan ya yi masa bayani irin matsalar da yake fuskanta da
Fulani. Saboda haka, ya nemi a shiga yaƙi gadan-gadan. Sai Gobirawa suka ce, ‘ka san cewar sun yi tafiya mai nesa, saboda haka a bari su huta’. Sarkin Kabi Yakubu
Nabame ya amince da wannan shawara, bai san da cewa Gobirawa sun yi wannan, domin su nuna mass suna da dabarun yaƙi daban-daban. Saboda haka, Gobirawa sai da suka
bari dare ya yi, suka ɗaura yaƙi, suka je wuraren Fulani suka sa
masu wuta.
Haka kuma, duk Bafullatanin da ya futo sai su kashe shi. Koda safiya ta yi, Gobirawa sun gama da Fulani.
Da gari ya waye, Sarkin Kabi da rundunarsa da dawaki ashirin (20), suka zo domin a haɗa da dawakan Gobirawa ɗari (100) domin shirin yaƙi. Sai Magaji Mai doron yaƙi, kuma shugaban mayakan Dangaladiman
Gobir Malam Alu,
ya shaida masu cewa,
ai tun cikin dare suka gama da Fulani.
Saboda haka,
sai Sarkin
Kabi Yakubu Nabame ya naɗa
Dangaladiman Gobir Malam Alu ɗan
Sarkin Gobir Yakuba, a matsayin Natsini, kuma
shi ne
wanda ya daɗe
da wannan sarauta,
domin ya shekara arbain
da ɗaya
(41) yana sarauta,
daga shekara 1860-1901.
Ga kirarin da ake yi wa wannan basarake
Gabjiya Magajin Adam,
Jagaban Sarakai.
Dangaladiman Gobir
Malam Alu,
kuma Natsinin Kabi,
shi ne
ke jagorar sarakuna da zarumawa a wurin yaƙi, tare da taimakon sarkin
yankinsa watau Magaji
Mai doron yaƙi.
Haka kuma, Gobirawa sun taimaka wa Kabawa a lokacin yaƙin da ya faru tsakanin Kabawa da Fulanin Sakkwato. Dangaladiman
Gobir Malam Alu tare,da
taimakon almajiransa,
watau Magajin
Baberi da Magajin Kulodo, su ne suka taimaka aka ba Sarkin Kabi Saman Yakubu laya mai suna ‘Gogarna babbar laya’, wadda aka umurce shi da ya cije ta, kuma ya hau dokinsa tana
cije
ga bakinsa. A lokacin ne aka gan shi
bisa toran giwa ɗauke
da jariri a baki. A lokacin ne Sarkin Musulmi Abdulrahman, shi da mutunensa suka gudu, suka bar tamburransu, su ne Kabawa suka ɗauka a matsayin ganimar
yaƙi.
Bayan rasuwarsa, Dangaladiman Gobir, kuma Natsinin Kabi, Malam Alu, ɗansa Malam Usman Manu ya gade shi, kuma ya shekara goma sha ɗaya watau daga 1901-1912. Haka kuma, ɗansa Malam Muhammadu Nababa, ya zama babban Malami a ƙasar Argungu, wanda ake girmamawa matuƙa, shi ne kakan Wakilin Daular Gobir Sardauna Muhammad Lawal Argungu.
Al-ƙur’ani Mai Girma, Hizu Sitin –ƘIra’ar Warsh, wanda Dangaladiman Gobir Malam Alu ɗan Sarkin Gobir Yakuba, ya rubuta da hannunsa, a shekarar 1860, kuma shi ne Natsinen Kabbi na farko, daga shekara 1860 – 1901.
Gogarma babbar laya, wadda Ɗangaladiman Gobir
da almajiransa suka bai wa Sarkin Kabi Sama
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.