Jiya da na kai wa kakata Tasalla ziyara a ƙauye, sai na same ta zaune a ɗaki rungume da kaskon wuta tana ta ƙahon dandi. Muka gaisa, na samu wuri na zauna na fara raba ido a cikin ɗakin ina kallon tarkacen da tsohuwar nan ta tara. Ita har yanzu ba ta yarda ta rabu da wasu karikitan nata ba.
A can wata kusurwa ta bangon ɗakin na ga an jingine zunguru an kuma zube azargagi kusa da shi. A wani ɓanggaren kuma ga mazari bisa taskira har da abawa, ga kuma akwasa jingine. Na ga kuma gafaka rataye a jikin agalemin da aka kafe a bango. Hatta akushi da ƙoshiya tsohuwar nan ba ta watsar ba, ba maganar gidauniya da tarde ake yi ba. A ɗaya gefen kuma an girke tulu an rufe bakinsa da jemo ga kuma ɗan jallo kusa da shi. Da na ƙyalla ido wani saƙon sai na hangi shantu, na ce a raina lallai su Kaka an yi duniyanci.
Da na gama nazarin kayan ɗakin sai na ce mata, "kaka sanyi kike ji hala, na ga kin tasa wuta gaba kamar za ki faɗa ciki?"
Ta ce, "kai dai bari ɗan nan, wannan ruwa da ake shatatawa kwanan nan, ga kuma ɗan karen sanyi sai ka ce jaura ke wucewa, idan mutum ya yi sake sai a yi masa sakiyar da ba ruwa." Ta jawo ɗan kindai daga tsariyar gado ta buɗe, ta ɗauki farsa ta cika bakinta. Ta dube ni ta ce, "dube ka, ko taguwar kirki ma ba ka sanya ba. Ahir ɗinka da sanyi!"
Na dubi 'yar shet ɗin da ke jikina na yi dariya na ce, "to ni tsoho ne kamarki da zan ji sanyi?"
Ta yi dariya, bakinta ya yi bajau ya fara ɗaukar ala. Ta ce, "garin da za a me ake yi wa albada?" Ta sake duba na ta ce, "amma dai ka samu taguwar kirki ka riƙa sanyawa, ina amfanin wannan figaggiyar riga kamar ka roƙa?"
Na ce mata, "yadda kike jin sanyi, to ni zafi nake ji, shi ya sa na sanya ta domin na sha iska."
Ta ce, "to ai wannan rigar Nasaru ce, ka kuwa ji an ce Nasara asarar duniya. Ka nemi 'yar shara ita ce taguwar Bahaushe ta shan iska."
Na ce, "to ita ma 'yar sharar ai ga Bature Bahaushe ya kwaikwaye ta."
Ta tsarga yawu a cikin kurtu ta ce, "yaro dai yaro ne. Ai ko da iska ya zo ya tarar da kaba na rawa. Ko da Bature ya zo ƙasar nan ya iske Bahaushe da cikakkiyar suturarsa, ba kamar wasu ƙabilun da ya tarar tumbur suna ɗaura ganyaye ba. Bari in ba ka tarihin asalin taguwa ka ji. Wani mutum ne mai suna..."
Na katse ta domin na san idan ta fara zuba, sai dare ya kwace mini ban sani ba. Na ce mata, "yanzu babu lokacin jin wannan tarihi, kin ga rana har ta yi gora za ta fara ruɗa-kuyangi, ga hanyar taku babu kyau idan an yi ruwa, ko yanzu sai da kwiɓin bazawara ya yi kusa ya kayar da babur ɗina. Ga kuma rashin tsaro da ake fama da shi. Idan Allah ya kai mu jibi, amaryar wata, zan dawo na ji wannan tarihi."
Na zaro kuɗi daga cikin aljihuna na miƙa mata, na ce ta sayi goro. Ta sa hannu ta kalmashe tana godiya, ta jawo mayani ta dunƙule kuɗin ta jefa ciki. Muka yi sallama, na ɗage asabari na fita daga ɗakin, na buga babur ɗina na nufi gari, kamar mil biyar daga ƙauyen, ina ta hirji a cikin zuciyata.
.
Menene ma'anar waɗannan kalmomi kamar yadda suka fito a cikin labarin?
1. Ƙahon dandi
2. Zunguru
3. Azargagi
4. Mazari
5. Taskira
6. Abawa
7. Akwasa
8. Gafaka
9. Agalemi
10. Akushi
11. Ƙoshiya
12. Gidauniya
13. Tarde
14. Jemo
15. Jallo
16. Shantu
17. Jaura
18. Kindai
19. Farsa
20. Albada
21. 'Yar shara
22. Kurtu
23. Ala
24. Ruɗa-kuyangi
25. Kwiɓin bazawara
26. Mayani
27. Tsariya
28. Asabari
29. Hirji
30. Amaryar wata
#RanarHausaTaDuniya
Bukar Mada
26/08/2022
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.