Ticker

Unguwar Gobirawa A Garin Katsina: Baƙi Masu Ciyar da 'Yan Gari

 Tsakure: Lamarin tashin wasu al’ummomi daga mazauninsu na asali zuwa wani mazaunin daban, ba baƙon abu ba ne ga al’ummar duniya gaba ɗaya. Kuma sauyin mazaunin kan tasiranci baƙin, wato dai su ɗabi’antu da wasu halaye da suka taras a sabon mazaunin, ko kuma su kai nasu ɗabi’un ga al’ummar da suka taras. Wannan takarda ta yi nazarin irin wannan yanayi, ta hanyar nazarin yadda al’ummar Gobirawa ta bar ƙasar Gobir ta tafi ta zauna a ƙasar Katsina a wata unguwa wai ita Unguwar Gobirawa. Takardar ta duba irin gudunmuwar da al’ummar Gobirawa suke bayarwa ga al’ummar garin Katsina. An ɗora wannan bincike ne a kan Ra’in Bazuwar Al’adu (Difussionist Theory) na G.E Smith da W.J Perry (1923) Daga ƙarshe, takardar ta lura da cewa, Gobirawan da ke zaune a Unguwar Gobirawa Katsina, zuwa suka yi unguwar kuma zamansu a unguwar yana da matuƙar tasiri ga al’ummar da suka taras.

UNGUWAR GOBIRAWA A GARIN KATSINA: BAƘI MASU CIYAR DA ‘YAN GARI

Abdurrahman Faruk
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina

Gobir

1.0 Gabatarwa

Lamari na sauyin mazauni daga mazauni na asali zuwa wani ga al’ummun duniya, ba baƙon abu ne ba. Ai ma tuni masana Ilmin Tarihi da Zamantakewa suke da ra’ayin cewa duk al’ummar da ke zaune a wani mazaunin da a yau suke iƙirarin nasu ne, to idan aka bi kadin tarihi, za a samu cewa zuwa suka yi saboda wani dalili mai ƙwari. Babu ma kamar al’ummomin nahiyar Afirika, domin su sun ƙware da suye-sauyen mazauni daga wannan wuri zuwa wancan, musamman idan suka matsu ko kuwa suna cigiyar wani abu da suke muradi. Misali ruwa ko mayalwaciyar ƙasar noma.

Kamar sauran alummomin duniya, al’ummar Gobirawa ma ba a bar ta a baya ba dangane da irin wannan sauye-sauyen mazauni. Misali, al’ummar Gobirawa sun matsa daga mazauninsu na farko wato Birnin Lalle zuwa Birnin Magale a gaɓar Gulbin Maraɗi a wajen ƙarni na goma sha bakwai (Augi, 1984: iɓ). Wannan takarda ta yi bincike ne a kan yadda al’ummar Gobirawan, wadda ke zaune a ƙasar Gobir ta jihar Sakkwato a yanzu, ta tashi ta je garin Katsina ta zauna har aka sami unguwa guda da a yau ake kira da Unguwar Gobirawa a Garin Katsina. Bugu da ƙari, takardar ta ziyarci wannan unguwa inda ta gana da mazaunan cikinta waɗanda duk yawancinsu Gobirawa ne, domin bin diddigi tare lalubo irin gudunmuwar da Gobirawan suke bayarwa ga al’ummar garin Katsina.

Bincike-bincike irin waɗannan ba a yau aka farayin su ba. Domin masana sun yi bincike-bincike a kan abin da ya shafi yadda al’ummar Hausawa suka riƙa barin mazaunansu na asali suna sauya wasu mazaunan saboda wasu dalilai, kuma wannan sauyin mazauni ya haifa wa Hausawan ɗabi’antuwa da wasu halaye na al’ummar da suka taras (NNPC, 1970). Wani masanin kuma ya yi makamancin wannan bincike inda ya yi binciken digiri na uku a kan abin da ya shafi al’ummar Gobirawa dangane da yanayin sauye-sauyen mazauni da alaƙar zamantakewa da siyasa da ta sa nasaba tsakaninsu da al’ummun da sukan taras a sabon mazaunin (Augi, 1984). An kuma aiwatar da nazari a kan alaƙar wasu ƙabilu, da yadda har wasan barkwanci ya shiga a tsakaninsu (Tukur, 1994). Tashin Hausawa daga mazauninsu na asali zuwa Lokoja inda suka haɗu da wasu alummomin daban suka tasirance su da halaye da ɗabi’u daban-daban, shi ma wani bincike ne da yake da nasaba da wannan da ake gudanarwa (Suleiman, 2001). Daga baya-bayan nan kuma, an aiwatar da wani binciken wanda ya bayyana yadda Hausawa suka shiga ƙasashen nahiyar Afirika da ma ƙasashen duniya gaba ɗaya (Muhammad, 2011). Shi kuwa Jaja, (2015) bayani ya yi a kan yadda Hausawa suka kawo sauyin rayuwa da ɗabi’u ga alummar da ke zaune a Sabo-Ibadan da dai sauran irinsu.

Kodayake, ba manufar wannan takarda ba ce ta maimaita ayyukan nan da aka ambata a sama. Hasali ma, ita wannan takarda za ta bi diddigin tarihin shigar Gobirawa ne a ƙasar Katsina da yadda aka yi har suka kafa unguwa mai cin gashin kanta wai ita Unguwar Gobirawa. Sannan an dubi yadda baƙin nan (Gobirawa) suke tallafa wa Hausawan garin Katsina da wasu sana’o’i da suka ƙara ɗaga tattalin arziƙin Katsinawan, musamman ma waɗanda suke zaune a Unguwar Gobirawa, wato mazauni ɗaya da Gobirawa ke nan.

1.1 Ra’in da Aka Ɗora Bincike a Kai

A wannan maƙala, an yi amfani da ra’in Bazuwar Al’adu (Difussionist Theory) wanda G.E Smith da W.J Perry suka ƙirƙiro a shekarar (1923). Kuma wannan ra’i ne Gusau (2015) ya kira da Makarantar Tarihin Hayayyafa. A wannan ra’i ana iya bin sawun yadda wata al’umma ta yi riƙo da al’adar da take gudanarwa. Haka kuma, za a iya amfani da ra’in a gane yadda wata al’umma ta yaɗu ko ta bazu a cikin wata al’ummar, da kuma yadda aka sami nason al’adu a tsakanin al’ummomin guda biyu. A ra’ayin Smith da Parry (1923), babu wata sabuwar al’ada a doron ƙasa, duk al’adar da wata al’umma za ta aiwatar, ta are ta ne daga wata al’ummar daban. (Ado, 2017: 89 da Gusau, 2015:41)

Dangantakar ra’in Bazuwar Al’adu (Difussionist Theory) da wannan maƙala ita ce, yadda aka bi sawun rayuwar al’ummar Gobirawa tun daga mazauninsu na asali, har yadda aka yi suka taso daga ƙasarsu suka tafi garin Katsina suka yi kaka-gida. Sanadiyyar haka kuma, suka kafa unguwarsu a Katsina mai suna Unguwar Gobirawa. An kuma nuna yadda aka sami nason al’adun Gobirawa a kan Katsinawan.

   

2.0  Taƙaitaccen Bayani a Kan Gobirawa

“Gobir Gidan Faɗa.” Haka Hausawa kan yi wa ƙasar Gobir da Gobirawa kirari. Wannan ba ya rasa nasaba da kasancewar Gobirawa mutane ne masu hazaƙa kuma jarumai a fagen yaƙe-yaƙe da sauran al’ummomin da suka yi karon batta da su a lokacin yaƙe-yaƙe tsakanin ƙabilu da ba hamata iska ya kasance tsarin rayuwa (Augi, 1984:3).

Masana tarihi sun ruwaito cewa daular Gobir ta fara kafuwa tun a ƙarni na takwas. Kuma tun daga kafuwar daular take fama da yaƙe-yaƙe da sauye-sauyen birni, a dai ƙoƙarin Gobirawan na kafa babbar daula mai ƙarfin gaske. Mazaunin ƙasar Gobir na farko shi ne Gobir-Tudu (Tukur, 1994:112). Gobir-Tudu ƙasa ce mai yawan rairayi, da tsaunuka, da itatuwa, da tsananin zafin rana musamman a lokacin bazara. Akwai kuma, iska da hazo a zamanin hunturu. Amma a lokacin damina kuma, ana samun isasshen ruwan sama. Wannan yanayi ne ma ya sa mazauna wurin suka kasance ƙasaitattun manoma da makiyaya. Ƙasar Gobir tana da wani shahararren sarki mai suna Audu Jan Namiji. An yi wannan sarki a zamanin da daular Usmaniyya ba ta fi shekara ashirin (20) da kafuwa ba (Funtua, 2017:11).

Tarihi ya nuna cewa, Gobirawa sun fito ne daga ƙasashen Gabas, a ƙarƙashin shugabansu mai suna Gubur. Daga nan kuma sai suka yi ta yaƙe-yaƙe da maƙwabtansu suna ƙara faɗin daularsu. Sarki Lamarudu ne ya koro Gobirawa daga Gabas a dalilin yaƙe-yaƙe, suka nufo Yamma har suka iso inda suka fara zama, suka kafa gari sannan suka sa wa wannan gari nasu sunan shugabansu wato Gubur. To, daga Gubur ne suka taso suna ta yawace-yawace har suka iso inda ake kira yanzu da Gobir (Tukur, 1994:112).

Daga cikin al’ummomi maƙwabtan Gobirawa, waɗanda Gobirawan suka riƙa yaƙa suna korar su don su gaje garuruwansu, akwai Zamfarawa. Gobirawa sun yi zaune-zaune wurare da dama. Daga cikin wuraren da suka zauna akwai Alƙalawa, da Sabon Birnin Gobir, da Tcibirin Gobir, da Birnin Lalle, da Birnin Magale, da Gwararrame, da Kadaje, da Gawon Gazau. A Birnin Alƙalawa ne Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya ci Gobirawan da yaƙi a shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari takwas da huɗu (Tukur, 1994:113). Ƙasar Gobir ƙasa ce mai yalwa. Ƙasarsu ta noma jar ƙasa ce mai danƙo kuma tana da kyau wajen aiwatar da aikin noma. Akwai mayalwatan itatuwa masu agaza wa Gobirawa da inuwa da tabbatar da tsaro da sauransu. Daga cikin itatuwan da Allah Ya albarkaci Gobir da su, akwai irin su bishiyar kuka. da tsamiya, da faru da dai sauransu (Augi, 1984: ɓiii)

 

3.0 Taƙaitaccen Bayani a Kan Katsina

“Ta Dikko ɗakin kara, tudu garin Ɗanmarna, mai tururuwa mai gafiya.” Wannan shi ne kirarin da ake yi wa Katsina. Dangane da Katsinawa kuma, akan ce da su, “Katsinawa kunya gare ku ba ku da tsoro.” Katsina gari ne wanda yake daga cikin garuruwa bakwai da aka fi sani da “Hausa Bakwai,”waɗanda suka samu a dalilin zuwan Bayajidda.

Garin Katsina ya yi iyaka da garin Maraɗi da Tasawa daga Arewa, sai Zamfara daga Kudu har Birnin Gwari. Katsina babban gari ne da ke kewaye da ganuwa. Akwai shahararriyar makarantar alƙalai da cibiyoyin koyar da addinin Musulunci har guda tara kewaye da garin. Baƙi daga maƙwabta suna sha’awar zuwa garin saboda kyakkyawar ƙasar noma da dabbobin ni’ima da zaman lafiya da ke tattare da garin. Kila ma shi ya sa Hausawa ke yi wa garin Katsina kirari “Katsina ta Dikko ɗakin kara” (Imam da Commassie, 1995:5)

Tarihin Bayajidda ba ɓoyayyen lamari ne ba, domin an ce asalinsa mutumin Bagadaza ne, inda ya baro ƙasarsa ya nufo Borno, ya auri ‘yar sarkin Borno na wancan lokaci wato Magira. Daga nan, ya garzayo zuwa ƙasar Daura, inda ya kashe macijiya Sarki. A dalilin wannan jarunta tasa, sarauniya Daurama ta aure shi. Sai kuwa Allah Ya albarkaci auren nasu da ɗa namiji mai suna Bawo. Shi kuma Bawo ya haifi ‘ya’ya bakwai duk maza waɗanda suka sari garuruwan ƙasar Hausa. Kuma garuruwan suka ci sunayen waɗanda suka sare su. ‘Ya’yan su ne: Katsina da Daura Kano da Rano da Biram da Gobir da kuma Zazzau ( Dokaji, 1988:1, Imam 1995:1)

Kumayo ɗan Bawo wanda ya yi mulki a shekarar (1102) shi ne sarkin Katsina na farko (Imam da Commassie, 1995:1). Wannan suna na Katsina ya samo asali ne a dalilin auratayya tsakanin Daurama da Janhazo (Sarkin Durɓawa) wanda tarihi ya nuna cewa ya yi mulki ne a Durɓi-Ta-Kusheyi (Imam da Commassie, 1995:1). Wata majiyar cewa ta yi waɗanda suka fara zama wurin da a yau ake kira Katsina, wasu mutane ne guda biyu wato Buga da Urwatu. Shi Buga shi yake da gona a Bugaje. Dukansu sun zo ne daga Hagaga ta ƙasar Daura, suka ya da zango a Durɓi-Ta-Kusheyi. Duk da yake dai, ba a san daga ƙabilar da waɗannan mutane suka fito ba, amma dai ana kyautata zaton Barebari ne da suka ratso hamadar rairayin sahara (Imam da Commassie, 1995:1).

Ya zuwa ƙarni na goma sha bakwai (17), Katsina ta tsere wa tsara, saboda yadda malaman addinin Musulunci, baƙi daga ƙasashen Larabawa suka riƙa karakaina a garin. Waɗannan baƙi suna zuwa ne daga ƙasashen Larabawa, daban-daban kamar Masar da Senegal da Saudi Arabia da Tunusiya da sauransu. Misali, Malam Muhammad ibn Al-Sabbagh, wato mahaifin Wali Ɗanmarna, sai malam Masani, mahaifin Wali Ɗanmasani (Yahaya, 1988: 36-37). Yanayin garin shi ne a yi sanyi-sanyi da safe, sai a yi zafi da rana, da yamma a yi sanyi-sanyi, ko da kuwa a yanayin hunturu ne ko damina. (Imam da Commassie, 1995).

 

4.0  Unguwar Gobirawa a Garin Katsina

Unguwa na nufin shiyya ko ɓangare na gari (Bargery, 1934:1068). Saboda haka, unguwar Gobirawa na nufin shiyya ko ɓangaren da al’ummar Gobirawa suke zaune a cikin gari. Unguwar Gobirawa a garin Katsina tana nan a Yammacin garin Katsina, dab da wata unguwa da ake kira Tsofuwar Kasuwa. Unguwar tana Yamma da majalisa ko fadar sarkin Katsina wato Ƙofar Soro, bisa hanyar zuwa maƙabartar Ɗanmarna, da kuma makarantar firamare ta Ɗanmarna a yanzu. Sannan kuma tana bisa hanyar zuwa Unguwar Rafin Daɗi, Katsina. Da an wuce makarantar firamare ta Ɗanmarna kaɗan daga dama idan daga babban masallacin Jumu’a na garin aka biyo, bisa doron kwana, akwai lungun da ake kira Kwanar Ɗambukari. Da an shiga Kwanar Ɗanbukari aka ɗan taɓa tafiya kamar ƙafa hamsin, to za a taras da Unguwar Gobirawa.

Bugu da ƙari, Unguwar Gobirawa a Katsina ta yi iyaka da gidan Alhaji Hamdana a yanzu daga Gabas. Daga Yamma kuma ta dangano da tabkin Gangambu. Daga Kudu kuma, ta yi iyaka da gidan Alƙali Inusa. Sai daga Arewa kuma ita ce har gidan Alhaji Maje. Akwai gida ashirin da bakwai waɗanda suke na Gobirawa ne a unguwar. (Hira da Malam Ɗanshehu, 2018). Da wannan bincike ya nemi sanin haƙiƙanin iyakar unguwar, sai Malam Ɗanshehu Bagobiri ya ce:

 

Gidajenmu nanniyanga sun kai kimanin ashirin da bakwai, ko ba haka ba? Waɗanda Gobirawa muke na asali. Ko ba haka ba? Kodayake, wasunmu sun koma gida can Gobir cikin dwangi, saboda larurar rashil lahiya da tsuhwa. Ko ba haka ba? Wasu kuma sun koma ga Ubangijinmu, Allah dai Ya ji ƙansu. Unguwag ga ita ta tun dagga gidan Alƙali Inusa, ta kewaya taukin Gangambu, ta kelayo hat tad dawo ƙohwag gidan Alhaji Maje, dug Gobirawa aka hwaɗi (Alhaji Ɗanshehu Bagobiri, 2018)

 

Tarihin kafuwar wannan unguwa ba ɓoyayye ne ba. Da binciken nan ya nemi sanin asalin zuwan Gobirawa, a Unguwar Gobirawa a Katsina, sai ya tuntuɓi malam Ɗanshehu Bagobiri. Ga abin da yake cewa:

 

Ba yaƙi na yak kawo mu Katcina hal muka zauna wagga unguwa ba. Yadda abin shike, Uwayenmu na tun usuli, ko ba haka ba? Mun ji dagga tsohwahhinmu cewa, da can an yi wani Sarkin Gobir mai suna Bawa Jan Gwarzo. Shi wanga Sarki cikin rami shike da zama. Yakan huto kullun swahiya, sai yay yi dawa, ya yi hwarautatai, ya kuma komo yas shige cikin raminai. An tabbatar da jaruntatai, don an ce wai an taɓa aiko ma shi da Mala’ika anka tambaye shi mi yaka so hwaɗin duniyag ga? Sai yac ce shi duniya yaka so, ba ya son wurin yaƙi a kashe shi. To, lokacin da Ɗanhodiyo yat taho Sakkwato ya hwara yaƙin kahurrai, sai mutane sunka ba shi shawarac cewa kada ya kuskura yay yaƙi Bawa, saboda shi Bawa wahayi anka yi mai. Ya saurara in da rabo yam mutu don kainai, sai a yaƙɗanai Yunhwa, saboda shi ya hi taushi-taushi. Da kuwa ya mutu sai Ɗanhodiyo yay yaƙi Yunhwa ya kuma ci naswara. To, lokacin akwai Kakanninmu da sunka bi Ɗanhodiyo sunka Musulunta suna nan inda Ɗanhodiyo. Bayan da Sarkin Katsina Ummarun Dallaje ya tahho Sakkwato inda Shehu ansat tuta, sai Ummarun Dallaje yac ce, “ba ni barin ka kai kaɗai kat tahi Katcina, bari in haɗa ka da mallammai su taimake ka da du’a’i a kan hanya kuma in kun isa Katcina sai su riƙa koya wa mutane karatun addinin Musulunci.” Wannan shi na dalilin da yas sa uwayenmu sunka biyo Ummarun Dallaje Katsina. Da sunka iso sai Dallaje yat tambayi uwayenmu inda suka son zama. Sai sunka zaɓi nanniyanga wada a da dajin Allah na. Sai Sarkin Katcina Ummarun Dallaje ya sa aka yayyanka masu gonaki a nan aka ba su. Sunka gina bukkoki a ciki sukai ta noma. Wannan shi a asalin kahuwar wagga unguwa mai suna Gobirawa. (Hira da Malam Ɗanshehu Bagobiri, 2018)

 

Wannan bayani na Malam Ɗanshehu Bagobiri yana nuna cewa, ba bauta ce ta kawo Gobirawan Unguwar Gobirawa a Katsina ba, a’a malanta ce ta kawo su da amsa kiran Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. To, shure-shure dai ba ya hana mutuwa Bawa dai bawa ne, uban gida kuma uban gida ne.

 

5.0       Gudunmuwar da Gobirawan Unguwar Gobirawa a Katsina Suke Bayarwa ga

            Al’ummar Garin Katsina

Kalmar gudunmuwa a ra’ayin Bargery, (1934) tana nufin taimako ko kawo ɗauki. Saboda haka, Gobirawan Unguwar Gobirawa a Katsina, suna ba da gagarumar gudunmuwa da taimako da ɗauki ga ci gaban al’ummar Katsina. Wannan gudunmuwar ce ta sa har wannan takarda ta yi wa Gobirawan kirari da, “baƙi masu ci da ‘yan gari.” Wato ga su dai zuwa suka yi, amma su ke ciyar da masu masaukin baƙi. Yanzu za a yi bayanin ire-iren ɓangarorin da Gobirawan Unguwar Gobirawa suke taimakon Katsinawa ta hanyarsu.

 

5.1 Noma

Daga cikin ɓangarorin da Gobirawan Unguwar Gobirawa a Katsina suke tallafa wa al’ummar Katsinawa, akwai sana’ar noma. Na duƙe tsofon ciniki.... Noma shi ne ta da ƙasa da cire ciyawa da shuka iri da renon sa har ya kai lokacin girbi (Bargery, 1934:822). Haka ma kiwon dabbobin gida da na daji da tsuntsaye duk noma ne. Noma dai babbar sana’a ce ga Hausawa. Gobirawan Unguwar Gobirawa Katsina manoma ne na gaske. Domin tun lokacin da sarkin Katsina Ummarun Dallaje ya yayyanka musu gonaki a inda a yau ake kira Unguwar Gobirawa a Katsina, suke aiwatar da noman kayan abinci da na sayarwa.

Malam Abdulƙadir Bagobiri, ya tabbatar wa da wannan bincike cewa, babu wani Bagobiri a Unguwar Gobirawa da ba shi da gona tasa ta kansa, duk da cewa yanzu gonakin nasu sun yi musu nisa, wasu na can hanyar ƙaramar hukumar Batsari wasu kuma na hanyar zuwa ƙaramar hukumar Jibiya:

 

Yaya ma za a yi a ce yanzu a sami wani Bagobiri a unguwag ga da ba shi da gona ko bai noma? To ya ci mi? Ai mu nan abin kunya na a sami Bagobirin da bai noma. Kowace irin sana’a yakai, to sai hwa ya haɗa da noma, in ba haka ba kau a kawo ƙaras shi ga Sarkin Gobirawa Kabir, ya kau hukunta shi. Ni kaina da yarana mukan yi a ƙalla buhu maitan tsakanin gero da dawa da masara a shekara. (Hira da Abdulƙadir Bagobiri)

 

Idan aka lura za a ga cewa mafi akasarin abincin da ake amfani da shi a garin Katsina, Gobirawan Unguwar Gobirawa ke noma shi.

 

5.2 Malanta

Aikin yaɗa ilmi, ko malanci shi ne malanta. (CNHN, 2006: 328). Wanda duk ya ilmanta kuma yake koyar da ilmin ga wasu, shi ne malami. Ai hidimar yaɗa ilmi daga wannan mutum ko wuri zuwa wancan, ita ce malanta. Malanta a ƙasar Hausa sana’a ce. Domin ana samun masu yi wa mabuƙata addu’o’i da sauran ayyukan malamai don a biya su. Irin wannan sana’a Gobirawan da ke zaune a Unguwar Gobirawa a Katsina suka runguma. Domin akwai malaman da ke da almajirai sosai da aka kawo musu daga sassa daban-daban na ƙasar Hausa don su sami ilmin Alƙur’ani mai girma. Bayan sun sauke kuma malaman su koyar da su karatun littattafai na ilmi, abin da ya shafi Fiƙihu (ibada), da Tauhidi (Kaɗaita Allah), da Ilmin Hisabi da dai sauransu. Daga cikin malaman addini masu karantarwa, akwai malam Abdulƙadir Bagobiri, wanda aka ce shi jika ne ga Kakan Gobirawan Unguwar Gobirawa Katsina, wato Malam Abubakar wanda ya zo tare da Ummarun Dallaje, kuma ya tashi daga Unguwar Gobirawa ta garin Katsina ya koma bayan Rahi-Ƙarami, a Rafin Daɗi, Katsina, saboda yawan almajiran da yake da su, waɗanda gidansa na Unguwar Gobirawa ya yi masa kaɗan.

 

5.3 Ɗori

Ɗori na nufin gyaran karaya ta ƙashin mutum ko dabba (CNHN, 2006:126). Daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa, wadda idan mutum ko dabba suka ji rauni har ta kai ga karayar ƙashi, sai a ɗora su. Ɗori yana ɗaya daga cikin sana’o’in da Gobirawan da ke zaune Unguwar Gobirawa a Katsina suka sare wa sanda. An san su da wannan sana’a tun tale-tale, har ta kasance yanzu su ne na biyu idan ka cire mutanen garin ‘Yanɗaki, a ƙaramar hukumar Kaita. Gobirawan Unguwar Gobirawa a Katsina ƙwararru ne wajen gyaran karaya ga mutum da kuma dabba, su duba su bayar da magani na sha da na shafawa, kuma cikin ikon Allah a sha a warke sumul. Misalin masu yin wannan sana’a a Unguwar Gobirawa sun haɗa da malam Sahalu Ka-san-Allah, da Malama Salmu ( Hira daAlhaji Ɗanshehu Bagobiri).

 

5.4 Koli

Koli tsofuwar sana’a ce a ƙasar Hausa. Sayar da tarkace da dama kamar su kwalli da masoro da allura da zare da zaren ulu da rumi da sauransu shi ne koli. (CNHN Kano, 2006:249). Masu gudanar da sana’ar koli, ana ce da su ‘yan koli. Yayin da mutum ɗaya kuma ake kiran sa ɗan koli.Wannan sana’a ta koli tana daga cikin irin gudunmuwar da Gobirawan Unguwar Gobirwa a Katsina suke bayarwa ga al’ummar Kastinawa. Har yau, har gobe idan ana buƙatar samun ingantattun kayan koli, kuma masu rahusa a garin Katsina, to sai wurin Gobirawan unguwar Gobirawa. Kodayake, ba a cikin unguwar suke baje kolin ba, suna da rumfuna a kasuwannin ƙauyuka da na cikin garin Katsina. Misali, wasu daga cikin waɗannan Gobirawa suna da rumfuna a Babbar Kasuwar Katsina (Katsina Central Market). Wasu kuma a ƙauyuka kamar Kasuwar Batsari da ta Kaita da Kagadama da Caranci da Mashi da Jibiya da dai sauransu. Daga cikin Gobirawa ‘yan koli da ke zaune a Unguwar Gobirawa a Katsina akwai irin su shi kansa wanda wannan maƙala ta yi hira da shi wato Alhaji Ɗanshehu Bagobiri, da ƙanensa marigayi Alhaji Almu Bagobiri da dai sauransu. (Hira da Alhaji Ɗanshehu Bagobiri).

 

5.5 Ƙira

Daga cikin daɗaɗɗun sana’o’in gargajiya na Hausawa akwai ƙira. Sana’a ce ta narka ƙarfe da sarrafa shi don samar da ma’aikaci kamar fartanya da garma (CNHN, 2006:281). Gobirawan Unguwar Gobirawa Katsina sun ɗauki wannan sana’a ta ƙira a matsayin hanyar rayuwa wadda za ta agaza musu yau da kullum, kuma har su taimaki al’ummar da suka taras a wurin wato Katsinawa. Daga cikin Gobirawa maƙera da ke zaune a Unguwar Gobirawa Katsina akwai malam Abdulhamida na maƙerar Rahi- Ƙarami, da Malam Mudi shi ma dai a wannan maƙerar Rahi-Ƙarami, da ke unguwar Rafin Daɗi a Katsina. (Hira da Alhaji Ɗanshehu Bagobiri, 2018.)

 

5.6 Sasanci

Idan aka yi maganmar sasanci, ana nufin a shiga tsakanin masu husuma guda biyu don sulhunta su (CNHN, 2006:393). Sau da yawa, akan sami husuma ko rikici da tankiya da rashin jituwa tsakanin mutum biyu ko mutane da yawa, abokan sana’a ne ko ma’aurata, ko maƙwabta da dai sauransu, kuma a rasa wanda za ya shiga tsakani. Wannan dalili ne kan sa sai husumar ta yi ƙamari har ta kai ga hasarar rayuka, ko lafiya, ko dukiya. To, Gobirawan Unguwar Gobirawa idonsu ke nan mai gani. Sun ƙware wajen sasanta irin waɗannan matsaloli. Hajiya Ruƙayya da aka fi sani da Inna Bagobira, ‘yar kimanin shekara saba’in da ɗaya, a hirar da wannan maƙala ta yi da ita, cewa ta yi:

 

Wasan ga da at tsakaninmu da Katcinawa, ya sa suke dubin girmammu. Duk inda jidwali yas samu a cikin unguwag ga sai dai in ban twanka ba, amma da na twanka, yanzu ana bari nai. Ban san iyakaj jidwalin da nih hana unguwag ga ba. Ko mace tay yo yaji daga gidan mijinta, ga mijin ya zo biko, uwayen sunka hana, da ya zo ya hwaɗa min, nit tahi ni’i isko uwayen, nib ba su magana, walla hanƙuri sukai, saboda wagga amana da wargi da at tsakaninmu da su. In kuwa han nis shiga maganai, ka ga uwayen maccen ba basuwa ba, to lalle zance ya lalace, kila ƙarshen zama na yaz zo. Domin gori aka yi wa uwayen yaran a ce, “hal Inna Bagobira taz zo biko, amma don ɓalɓalta sunka hana ɗiya.” Koko a ce Inna Bagobira ta tam mai do mashi maccenshi, amma da yake ba ɗan ƙwarai na ba yas sake sakinta.” (Hira da Inna Bagobira, 2018)

 

Wannan bayani ya nuna Inna Bagobira tana taka muhimmiyar rawa wajen sasanta husumar aure a tsakanin ma’aurata. Kuma ba ƙaramar gudunmuwa ba ce wajen inganta rayuwar Katsinawa a garin Katsina. Sauran Gobirawan da kan yi sasanci a Unguwar Gobirawa Katsina akwai Sarkin Gobirawa Alhaji Kabir Abbatuwa, da Malam Ali Bagobiri (mijin Inna Bagobira) da sauransu.

 

5.7 Kamu

Kamu sana’a ce ta daidaita ƙashin dabba ko na mutum wanda ya goce daga muhallinsa na asali wato ba karewa ya yi ba. Haka kuma, sanyin jijiya da na ciki idan za a bincika su, a gane su a ba da maganinsu duk kamu ake cewa (Hira da Alhaji Ɗanshehu Bagobiri, 2008). Kamu ya sha bamban da ɗori. Shi kamu ya fi ta’allaƙa da jijiya da ƙashin da ya goce, a mai da shi muhallinsa na asali a kuma sa magani. shi kuwa ɗori sha’ani ne na karayar ƙashi, a sake haɗa shi, a sa magani ya warke (Hira da Alhaji Bakwai Bagobiri, 2018). Gobirawan Unguwar Gobirawa a Katsina sun tallafi wannan sana’a da hannu bibiyu, kuma suna amfanar da al’ummar Katsina da ita. Daga cikin waɗanda suka ƙware ga wannan sana’a ta ɗori akwai Alhaji Bakwai Bagobiri mai kamun targaɗe, sai Dije ‘Yab Bago ita kuma kamun awazu ko haƙarƙari (na-ƙauye) take yi. (Hira da Alhaji Ɗanshehu Bagobiri, 2018)

 

5.8 Ɗinkin Hannu

Ɗinki na nufin aikin haɗa abubuwa (musamman tufa) ta hanyar amfani da zare ko kirtani ko allura ko basilla ko keken ɗinki (CNHN, 2006:125). Sana’ar ɗinkin tufafi sana’a ce mai asali da daɗaɗɗen tarihi a zamantakewar rayuwar Ɗan’adam gaba ɗaya ba Bahaushe kawai ba. Su Gobirawan Unguwar Gobirawa Katsina, ɗinkin hannu suke yi, wato irin wanda ake murza zare ko a yi amfani da rumi a yi wa riga ado. A Katsina an fi sanin sa da Kwaɗo da linzami, musamman wanda ake yi wa malun-malun. Akan ce kuma surfani idan kaftani aka yi wa aikin. Gobirawan Unguwar Gobirawa Katsina sukan sayi yadi ko shadda su yi musu irin wannan ɗinki, su ɗauki abinsu su kai kasuwannin ƙauye su sayar. Wani lokaci kuma akan kai musu gaban rigunan (algyabba) su yi mata irin wannan aiki a biya su, musamman a lokacin bukukuwan sallah da na takutaha, da bukukuwan aure, ko na haihuwa, da naɗin sarauta da dai sauransu. Gobirawa maɗinka hannu a Unguwar Gobirawa Katsina akwai Alhaji Muntari Geji Bagobiri, da malama Salmu da sauransu. (Hira da Malam Muntari Geji Bagobiri, 2018).

 

5.9 Faskara Itace

Faskara itace sana’a ce ta tsaga itace da gatari (CNHN, 2006). Tsofuwar sana’a ce da Hausawa ke gudanarwa tun tale-tale. Haka kuma, sana’a ce da kan samar da makamashin yin girkin abinci da amfanin masana’antu na gargajiya, wato dafe-dafe da toye-toye da gashe-gashen abincin sayarwa kamar irin su ƙosai da waina (masa) da tubani da ɗanwake da ƙuli-ƙuli dai sauransu. Gobirawan Unguwar Gobirawa Katsina suna ba al’ummar garin Katsina gagarumar gudunmuwa da irin wannan sana’a ta faskara itace. Haka kuma, an san Gobirawan Unguwar Gobirawa Katsina da duk sana’o’in nan da aka ambata a sama, amma an fi sanin su sosai da wannan sana’a ta faskara itace. Wannan bai rasa nasaba da kasancewar su lafiyayyun mutane, majiya ƙarfi kuma masu zuciyar neman na-kai kome wahala ba. Shi ya sa Alhaji Ɗanshehu Bagobiri, da wannan bincike ya yi hira da shi a kan haka yake cewa:

 

Da yake ba a cika samun malalata a cikin Gobirawa ba, yawancin sana’o’in da muke yi na ƙarhi ne. Hwaskara itatuwa sana’ad da aka san Gobirawa da ita ce ba wai kawai a nan garin Katcina ba, a’a duk duniyar da ka je ka iske ana faskara itace a matsayin sana’a, ka tad da Bagobiri na ka yin ta. Duk gungumen da yag gagara, Bagobiri na saratai, kuma ya cim mai (Alhaji Ɗanshehu Bagobiri)

  

Daga cikin masu aiwatar da sana’ar faskara itace a Unguwa Gobirwa a Katsina akwai Isah Bagobiri da Audu Bagobiri mai faskare da Mu’azu Zagin Gatari.

 

5.10 Fatauci

Idan mutum yana gudanar da wata sana’a daga wannan gari zuwa wancan, sai a ce yana fatauci (CNHN, 2006:138). Gobirawan da suke zaune a Unguwar Gobirawa a Katsina fatake ne na asali. Domin sun yi ƙaurin suna wajen sayen haja iri-iri su ɗauka su kai kasuwannin ƙauye su sayar, su kuma saro wata hajar irin wadda babu ita a garin Katsina, su kawo kasuwannin garin irin su ‘Yar Kutungu ko Hi-Mata, su sayar. Wannan fatauci da Gobirawa ke yi ya taimaka ƙwarai wajen haɓaka tattalin arziƙin Katsinawa. Alhaji Muntari Geji Bagobiri falke ne. Ke nan sana’a goma yake yi wai maganin mai gasa. Yana ɗinkin hannu kuma yana fataucin kayan tireda, irin su omo da magi da sauransu, yana kai wa kasuwannin ƙauye yana sayarwa.

 

5.11 Dillanci

Dillanci sana’a ce da Gobirawan Unguwar Gobirawa suka riƙa hannu bibiyu. Sana’a ce da ake karɓar kayan mutane don a sayar a ba mai sayarwar la’ada. (CNHN, 2006:103). Namijin da yake aiwatar da wannan sana’a shi ake kira dillali. Mace kuma dillaliya. Idan dillali ya wuce ɗaya, sai a kira su dillalai. Babu abin da ba a yin dillancin sa. Akwai dillancin tufafi, akwai na kayan ado na mata, akwai na didaje da filaye. Dillancin gidaje da filaye shi al’ummar gobirawan Unguwar Gobirawa a Katsina suka sare wa sanda. Sun yi suna a cikin harkar, kuma babu gara babu zago. Wato mai sayarwa yakan sami kuɗinsa cas! Haka mai saye ya sami hajarsa a hannu, su kuma su kwashi la’ada. Da wannan takarda ta yi hira da Alhaji Ali Dillali, ɗaya daga cikin Gobirawan da ke zaune a wannan unguwa kuma masu aiwatar da wannan sana’a ta dillanci, sai ya ka da baki ya ce:

 

Dillalai na cikinmu ba su iya cuta ba. Kuma ma ai muna da ƙungiyammu ta Gobirawa Dillalai Mazauna Katsina. Ita wannan ƙungiya tsaye take wajen hukunta wanda du’a ad da hannu da cin zalin wani mai gida ko mai hili da yab basuwa a sayas. Saboda haka, kahin ka ji wani jidali da yas shahi dillalan gidaje ko hilaye daga cikinmu, ana daɗewa. Ina cikin wagga harka shekara talatin da taw wuce, ban taɓa zuwa ga iko ba. Alhamdu lilLahi. (Alhaji Ali Bagobiri)

 

                   Dillallan gidaje na Unguwar Gobirawa Katsina sun haɗa da Alhaji Ali Bagobiri da Sarkin Gobirawa Alhaji Kabir da Hajiya Barira Bagobira da dai sauransu.

 

5.12 Limanci

Aikin da Liman ke yi na jagorancin sallah shi ne limanci (CNHN, 2006). Kasancewar Gobirawan Unguwar Gobirawa a Katsina masu ilmin addinin Musulunci, musamman abin da ya shafi karatun Ƙur’ani Mai Girma, ya sa suka shige gaba wajen jagorancin mutane a harkar ibada kamar sallah. Duk yawancin limaman masallatan da ke wannan shiyya ta Yammacin Katsina, Gobirawa ne. Misali, masallacin Unguwar Gobirawan wanda ke kusa da gidan Alƙali Yunusa, Bagobiri ne limaminsa, wato malam Abdulƙadir Mai Almajirai. Sai masallacin bayan Rahi Ƙarami, wanda malam Mansur Bagobiri ne ke limancin sa. Malam Abidu ɗan Malam Abubakar, shi ke limancin masallacin Lalloki. Duk limaman nan Gobirawa ne da ke zaune a Unguwar Gobirawa a Katsina. Kuma limancin da suke yi yana agaza wa Katsina ta fuskar ɗaukaka addinin Musulunci.

 

6.0 Kammalawa    

Tabbas, da gaskiyar Hausawa da suke cewa, “Baƙo da arziƙinsa yake zuwa.” Sukan ƙara da cewa, “Baƙo wuyar samu gare shi.” Kamar yadda bayanai suka gabata, an ga yadda takardar ta bi diddigin tarihin zuwan Gobirawa a Katsina, da yadda aka yi zamansu ya ɗore, har suka kafa unguwarsu mai suna Unguwar Gobirawa. Takardar kuma ta yi taƙaitaccen bayani a kan su wane ne Katsinawa, da yadda rayuwarsu da ma wasu ɗabi’u da halayensu suke. Haka kuma, takardar ta kawo wasu hanyoyin da Gobirawan Unguwar Gobirawa suka bi wajen taimaka wa al’ummar da ke zaune a garin Katsina. Waɗannan hanyoyi kamar yadda takardar ta gano, hanyoyi ne na sana’o’i. Ta fuskar sana’o’in nan ne Gobirawan Unguwar Gobirawa Katsina suke ciyar da Katsinawa gaba, su taimake su, su kuma daɗaɗa musu. Wannan dalili ne ya ƙara sa danƙon soyayya da jituwa da fahimtar juna tsakanin Gobirawa da Katsinawa. Daga cikin waɗannan sana’o’i akwai noma da ƙira da fatauci da dillanci da ɗinkin hannu da dai sauransu. Saboda irin wannan tagomashi da Gobirawa suke ba Katsinawa ya sa wannan takarda take yi wa Gobirawa albishir cewa, daga yau Katsinawa ba su sake cewa, “A Mazaya....!” sai dai, “a mazayo....!”

 

Manazarta

Adamu, M. (1978). The Hausa Factor In West African History. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Ado, A. (2017). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa. Katsina: Kanki Calassical Media Enterprises.

Augi, A. R. (1984). The Gobir Factor In The Social and Political History of The Rima Basin. Circa 1650 To 1808 A.D. PhD. Thesie: Department of Nigerian and African Languages. Zaria: Ahmadu Bello University.

Bargery, G. P. (1934). Hausa-English Dictionary And English-Hausa Vocabulary. London: Oxford University Press.

Bunza, A. M. (2009). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Publishers, Ltd. Ahmadu Bello University Press, Limited.

CNHN, (2006) Ƙamusun Hausa Na jami’ar Bayero. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

Funtua, I.A. A. (2017). A Mazaya: Dangantakar Katsinawa da Gobirawa. Katsina: Kanki Classical Media Enterprises.

Gusau, S. M. (2015).Wasu Mazhabobin Ra’i Da Tarke A dabi Da Al’adu na Hausawa Kano: Century Research And Publishing Company.

Imam, K. and Commassie, D. (1995). Usman Nagogo: A Biography of The Emir of Katsina Sir Usman Nagogo. Katsina: Today Communication Limited.

Jaja, B.M. (2015). Zama Da Maɗaukin Kanwa: Tsokaci Kan Hausawa Mazauna Sabo-Ibadan. A Cikin Kadaura: Journal of Hausa Multi-Disciplinary Studies. Department of Nigerian Languages And Linguistics. Kaduna: Kaduna State University.

Muhammad, M.Y. (2011). Hausa A Yau: Taswirar Ƙasar Hausa Da Maƙwabtansu. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited. NNPC, (2006) Hausawa Da Maƙwabtansu. Zaria: NNPC.

Sarki, H.A. (2000). Tarihin Zuwan Musulunci Afirika da Shigowarsa Ƙasar Hausa. Babu Wurin Bugu.

 

Waɗanda Aka Yi Hira Da Su

1.      Alhaji Ɗanshehu Bagobiri A Gidansa Da Ke Unguwar Gobirawa a Katsina. Ranar 24/5/ 2018 Da Misalin Ƙarfe 5 na Yamma.

2.      Malam Abdulƙadir Bagobiri, A Makarantar Allon Ƙofar Gidansa da Ke Bayan Rafi Ƙarami, Rafin Daɗi Katsina. Ranar 27/5/2018 Da Misalin Ƙarfe 5 na Yamma

3.      Malam Ali Bagobiri, A Gidansa Da Ke Unguwar Gobirawa, Katsina. Ranar 22/5/2018. Da Misalin Ƙarfe 5 na Yamma.

4.      Sarkin Gobirwa Alhaji Kabir Abbatuwa, A gidansa Da Ke Unguwar Abbatuwa Katsina. Ranar 2/6/2018 da Misalin Ƙarfe 5 na Yamma.

5.      Alhaji Bakwai Bagobiri, A Gidansa Da ke Bayan Rafi Ƙarami, Rafin Daɗi Katsina. Ranar 6/6/2018 Da Misalin Ƙarfe 11 na Safe.

6.      Dije Yar Bago, A Gidanta da Ke Unguwar Gobirawa Katsina.

7.      Alhaji Muntari Geji Bagobiri, A Gidansa Da Ke Unguwar Gobirawa Katsina. Ranar 28/5/2018 Da Misalin Ƙarfe 6 na Yamma

8.      Hajiya Barira Bagobira, A Gidanta da Ke Unguwar Gonbirawa Katsina. Ranar 9/6/2018 da Misalin Ƙarfe 5 na Yamma

Post a Comment

0 Comments