Farillai, Sunnoni, Da Mustahabban Alwala Tare Da Hukunce-Hukuncen Tsarki (A Taƙaice)

Ya yin da muke ƙoƙarin zurfafa ilimi kan fannonin addini daban-daban, kada mu manta da ire-iren waɗannan abubuwa da suka kasance ababen lura a matakin farko.

Alh Auwal Abubakar Kobi (Talban Ajiyan Bauchi)
08026673587 or 08032979559

Farillan Alwala

Farillan alwala guda bakwai (7) ne:

1. Niyya

2. Wanke fuska

3. Wanke hannaye zuwa guiwar hannu

4. Shafar kai

5. Wanke ƙafafuwa

6. Cuccuɗawa

7. Gaggautawa

 Sunnonin Alwala

Sunnonin alwala guda akwas (8) ne:

1. Wanke hannaye zuwa wuyan hannu

2. Kurkure baki

3. Shaƙa ruwa a hanci

4. Fyacewa

5. Juyo da shafar kai

6. Shafar kunnuwa

7. Sabunta ruwa a gare su

8. Jeranta tsakanin farillai

 Mustahabban Alwala

Mustahabban alwala guda bakwai (7) ne:

1- Yin bismillah

2- Yin asuwaki

3- Ƙari a kan wankewa ta farko a fuska da hannaye

4- Farawa daga goshi

5- Jeranta sunnoni

6- Ƙaranta ruwa a bisa  gaɓoɓi

7- Gabatar da dama kafin hagu.

Muhimman Abubuwan Tunawa Game Da Fasalin Alwala

1. Wanda ya manta da wata farilla daga  gaɓoɓinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abun da ke bayanta. Idan kuma ya yi nisa, sai ya aikata ta ita kaɗai, ya kuma sake abun da ya sallata bayan faruwar abun.

2. Idan kuma ya bar sunna, to sai ya aikata ta ita kaɗai. Ba zai sake salla ba.

3. Wanda kuma ya mance lam'a sai, ya wanke ta ita kaɗai da niyya. In kuma har ya yi sallah bayan faruwar hakan, to sai ya sake ta.

4. Wanda ya tuna da kurkurar baki ko shaƙa ruwa bayan ya rigaya ya fara wanke fuska, to ba zai dawo gare su ba har sai ya gama alwalarsa, sannan sai ya yi su.

5. Tsettsefe 'yan yatsu hannuwa yana wajaba. Ana so a tsettsefe 'yan yatsun ƙafafuwa. Tsefe gemu mara duhu yana wajaba a cikin alwala. Tsefe gemu yana wajaba a cikin wanka ko da mai duhu ne.

Muhimman Abubuwan Tunawa Game Da Fasalin Alwala (2)

• Babu yana halatta ga wanda ba shi da alwala ya yi sallah, koh ɗawafi, ko ya taɓa Ƙur’ani ko da a cikin gafakarsa ne, ba da hannunsa ba sai dai idan juzu'i ne ga mai neman ilimi a cikinsa.

• Yaro a wajen taɓa Ƙur’ani kamar babba yake, amma laifin yana wuyan wanda ya ba shi Ƙur’anin ya taɓa.

• Wanda ya yi sallah da gangan ba tare da alwala ba to shi kafiri ne. Allah ya kiyashe mu.

Abubuwa Masu Warware Alwala

Karrai (Hadusa) da Sababai (Sabuba)

 Karrai guda biyar (5) ne:

1- Fitsari

2- Bayan gida

3- Tusa

4- Fitar maziyyi

5- Fitar wadiyyi

 Sababai su ne:

1- Bacci mai nauyi

2- Suma

3- Farfaɗiya

4- Marisa

5- Maye

6- Hauka

7- Sumbata

8- Shafar mace, idan an yi da niyyar jin daɗi ko kuma aka samu jin daɗin ko da babu nufi

9- Shafar azzakarinsa da cikin hannu ko da cikin 'yan yatsu

Muhimman Abubuwan Tunawa Game da Karyewar Alwala

a. Wanda ya yi ko kokonton samuwar kari/hadasi to alwala ta wajaba a gare shi, saidai in mai yawan waswasi ne, to babu komai a gare shi.

b. Ya wajaba ga wanda ya fitar da maziyyi ya wanke dukkannin azzakarinsa.

c. Shi maziyyi wani ruwa ne da yake fitowa lokacin 'yar sha'awa ƙarama, ta yin tunani ko kallo ko yin wanin wannan.

 Muhimman Bayanai Game da Tsarki

Tsarki kashi biyu (2) ne:

1. Tsarkin kari

2. Tsarkin dauɗa

A- Dukkan su ba sa inganta sai da ruwa mai tsarki, mai tsarkakewa shi ne: wanda launinsa bai jirkita ba, ko ɗanɗanonsa, ko ƙamshinsa, da abin da yake rarrabe shi marinjayi. Babu laifi ga ƙasar gishiri da ƙasar kanwa da makamancinsa.

B- Idan najasa ta fito fili sai a wanke gurin. Idanta fantsama ta yi, sai a wanke tufar gaba ɗaya.

C- Wanda ya yi kokonto a cikin samuwar najasa, to sai ya yi yayyafi da ruwa a jikin kayan.

D- Idan kuma wani abu ya same shi sai ya yi kokonton ko najasa ce, to ba sai ya yi yayyafi ba.

E- Wanda kuma ya tuna da najasa yana cikin sallah sai ya yanke sallar, saidai idan ya ji tsoron fitar lokaci. Wanda ya yi sallah da ita yana mai mantuwa sai ya tuna bayan ya yi sallama, to ya sake sallah idan da lokaci.

Allah ya karbi ibadunmu ya sa mu cika da imani.

Ya ‘yan uwa masu albarka, ku taya mu yaɗa wannan karatu/saƙo, za ku samu lada mai yawa, domin yaɗa ilimi yana daga cikin abubuwan da suke kusanta bawa ga Mahalicci.

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.