This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.
Ƙalubalen Tsaro a Masarautar Gummi: Sigoginsa da Dabarun Tunkararsa
Abdullahi Sarkin Gulbi (Ph.D.)
Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, Nigeria
gulbi.abdullahi.udusok.edu.ng
Sa'adu Musa
Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, Nigeria
Tsakure
Matsalar tsaro a yau ta zama tamkar wutar
daji da ta buwayi a kashe musamman a Arewacin Nijeriya da sauran sassan ƙasar nan. Jihar Zamfara ta zamo ɗaya
daga cikin jihohin da suke fuskantar irin waɗannan matsaloli na tsaro. Galibi yankunan da
wannan matsala ta yawaita kuwa sun haɗa da Zurmi,Shinkafi, Tsafe, Maru, Maradun, Talata
Mafara, Bakura, Anka, Bukkuyum da kuma Gummi. Wannan muƙala an gina ta ne da nufin nazartar irin ƙalubalen tsaro a masarautar Gummi ta jihar
Zamfara da zimmar fito da irin yankunan da suke fama da taɓarɓarewar
tsaron da kuma irin ɓarnar da ake yi wa jama’ar da nufin samar da wasu dabaru ko hanyoyin da
za su taimaka wajen rage matsalar tsaron ko magance ta kwata-kwata. A ƙoƙarin
tabbatar da binciken an lura da nau’o’in ta’addancin
da ake yi wa mutanen yankin kama da satar shanu da garkuwa da mutane da uwa uba
kashin gilla na babu gaira babu sabar. An yi amfani da hanyar hirarraki da waɗanda
abin ya shafa domin tace bayanan da aka samu a wajen su.
1.0 Gabartawa
Maƙasudi wannan muƙala shi ne domin a nazarci irin matsalar
tsaron da take addabar mutanen ƙasar Gummi
da kuma hanyoyin magance ta. Don haka, za a yi waiwaye game da taƙaitaccen tarihin Gummi da kewayenta da
sigogin matsalar tsaron da kuma dalilan taɓarɓarewar tsaron tare da hanyoyin magance
matsalar.
1. 1 Ma’anar
Tsaro
Kalmar tsaro kalma ce da ke nufin kare wani abu,[1] kalmar tana kuma iya ɗaukar ma’anoni kamar
kiyayewa, ko kula, ko kariya, ko fako.
A wannan muƙalar kuwa an jingina tsaro’da nufin dabaru ko hanyoyi ko tsare-tsare, ko
tanade-tanaden domin kiyaye ko tabbatar da kariya ga rayuka da dukiyoyin al’umma. A wata fahimtar kuwa, tsaro na nufin kariya
daga duk wata tsangwama da barazana ga walwalar al’umma tare da bai wa al’umma damar gudanar da hulɗa
da zamantakewa cikin lumana.
1.2 Rabe-Raben
Tsaro
Idan kuwa aka yi duba dangane da rabe-raben
matakan tsaron kuwa, za a ga cewa akwai tsaron gargajiya da kuma na zamani.
Haka kuma akwai tsaron cikin gida (internal Security) da kuma tsaron waje
(external security) Tsaron cikin gida (internal security) na nufin kariya ko
rashin ababen da ka iya yin zagon ƙasa ga
fahimtar juna tsakanin mabanbantan al’ummomi
da ɗorewar kyakkyawar zamantakewar ‘yan-ƙasa. Haka
kuma, yana nufin matakan da ƙasa ke ɗauka
wajen kare muhimman hukumomi daga maƙiya da ‘yan kanzaginsu da ke cikin ƙasar domin ta tabbatar da buƙatunta na kiyaye ɗiyaucinta,
al’adunta,
tattalin arzikinta da samar da ababen more rayuwa domin biyan buƙatun ‘yan-ƙasa (DSS 2012).
Tsaron Gargajiya: Wannan tsari ne tsaro da ya
shafi dabarun samar da kariya a gargajiyance wanda al’umma suka tashi a cikinsa tun kafin haɗuwar
su da dabarun tsaro na zamani. Irin wannan ya kasu zuwa gida biyu muhimmai
kamar haka;
1. Tsaro na jiki: Wannan tsaro ne da ya shafi dabarun kariyar
kai daga cuta, misali akwai magungunan tsari irin su; Baduhu da layar zana da
sagau da shashatau da kuma magungunan tauri da makamantansu waɗanda
ake tanada domin samun kariya daga cuta ko ɓacin
rana.
2. Tsaro na gari: Wannan nau’in tsaro ana yin sa ne domin samar da kariya
ga gida da dukiya da gari ko yanki. Daga cikin matakan wannan tsari na tsaro
sun haɗa da; kafin gida ko gona ko mata da katanga
ko darni ko ɗaurin gari ko haƙo ko ganuwa ko ƙofa ko kura waje da sauransu. Akan yi amfani
da waɗannan nau’o’in
tsaro ne a gargajiyance domin a samar da tsaro ga gida ko gari ko kuma yanki ko
wata dukiya.
3. Tsaron Zamani: Wannan tsaro ne da ya shafi amfani da
dabarun tunkarar tsaro irin na zamani wanda ya haɗa
da jami’an tsaro
masu kaki da farin kaya da na’urori da
makamai irin na kimiyyar zamani domin a kawar da barazanar rashin tsaro.
2.0 Kafuwar
Garin Gummi
Garin Gummi ya kafu da kuma bunƙasa ne a ƙarƙashin
jagorancin Zamfarawa da suke da asali daga wani ƙauye da ake kira “Tunfafi ko Tunfafiya[2].” Wato Zuri’ar Ali Bazamfare) Wani masanin[3] tarihi cewa ya yi “Su waɗannan Zamfarawa da suka taso daga Tunfafi ta ƙasar Talata Mafara, sun yi hijira ne zuwa yamma
a ƙarƙashin
jagorancin Ali Bazamfare zuwa wani
gari da ake kira Fakai a ƙasar Zuru,
daga nan ne kuma suka dawo wani gari da ake kira Danko duk a ƙasar Zuru ɗin
, a wannan gari Ali Bazamfarae ya haifi ɗa da ake kira “Kure,” bayan
yaron ya girma sai ya ba shi sarautar garin, ya koma wani gari da ake kira “Zauma,” a wannan
gari ma ya haifi ‘ya’ya guda biyu, ɗaya
ana kiran sa Ɗanƙofa
ɗayan kuwa ana kiran sa Muhammadu Waru.”
A shekarar 1782 ne sai Muhammadu Waru ya ɗebo
wasu daga cikin jama’ar
mahaifinsa (Ali Bazamfare) da ke zaune a can Birnin Zauma suka dawo wani ƙauye da ke kusa da garin Gummi mai suna “Kagarar Fulani” suka zauna. Kasancewar Muhammadu Waru jarumi
a fagen yaƙi da
taimakon jama’ar da suke
kusa da shi, ya ba shi damar samun karɓuwa a idon jama’a, har mazauna Gummi suka ga ya dace da ya zo
ya shugabance su a matsayin Sarkin Gummi na farko a tarihin Sarakunan Masarautar
Gummi.
Tarihi ya tabbatar da cewa, lokacin da
Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo
da jama’arsa suke
je Zamfara, musamman a ƙasar
Gummi, ya tarar da cewa Sarki Muhammadu Waru ya gama haɗa
kan dukkanin ƙauyuka da
ke maƙwabtaka da shi a ƙarƙashin
kulawarsa. Ya taimaka wa Shehu wajen jaddada addinin Musulunci a ƙasar Kabi, wanda a sakamakon hakan ne Shehu Ɗanfodiyo ya ba shi Tutar Girmamawa. Jin daɗin irin yadda Shehu ya karrama shi, Muhammadu
Waru ya ga ba a bin da zai yi ya rama abin da aka yi masa, sai ya yanke
shawarar sanya a gina wa Shehu Ɗanfodiyo Masallaci a garin Sifawa. An gina
wannan masallaci ne a shiyar ‘Yar
Katanga wadda a halin yanzu ake kira shiyar Yamma. Wannan Masallaci har yanzu
yana nan ana amfani da shi, duk da yake an mayar da shi ginar zamani[4]
2.1 Jerin
Sarakunan Masarautar Gummi
|
Suna |
Lokaci |
Adadin
Shekaru |
1 |
Muhammadu Waru |
1782-1807 |
25 |
2 |
Sarki Ɗankunyau |
1807-1819 |
12 |
3 |
Sarki Bawan Yari |
1819-1847 |
28 |
4 |
Sarki Salihu |
1847-1847 |
Wata 6 |
5 |
Umar Ɗan A’isha |
1847-1864 |
17 |
6 |
Ibrahim Ɗangwado |
1864-1867 |
3 |
7 |
Abdullahi Laje |
1867-1892 |
25 |
8 |
Sarki Aliyu Na ɗaya
(I) |
1892-1904 |
12 |
9 |
Sarki Ɗan ba’u |
1904-1910 |
6 |
10 |
Muhammadu Andi |
1910-1933 |
23 |
11 |
Muhammadu Maidabo |
1933-1976 |
43 |
12 |
Muhammadu Ɗanguntu |
1976-1983 |
7 |
13 |
Alhaji Aliyu Isah Andi |
1983-2011 |
28 |
14 |
Alhaji Aliyu Adamu |
2011-2013 |
Shekara (1) da W.7 |
15 |
Alhaji Justice
Lawal Hassan |
2013-Yau |
Sarki mai Ci yanzu |
An sami wannan
bayani ne a ofishin sakataren Emiyan Gummi 12/10/2019.
3.0 Dabarun
Tsaro a Masarautar Gummi
Wannan fasali zai yi bitar irin sarautun da
ke janye da a akalar tsaro ne a gargajiyance a faɗin
masarautar tun gabanin lamarin tsaro na zamani ya yi cikakken tasiri a kan su.
Daga cikin irin sarautun da suke da alhakin tsaron kuwa sun haɗa
da;
i.
Sarautun Bayi na Sarki.
ii.
Sarautun Bayi masu kula da fada.
iii.
Sarautun kula da tsaro na gari.
iv.
Sarautun fitattun Sana’o’in
gargajiya.
3.1 Sarautun
Bayi na Sarki.
A ƙarƙashin wannan, za a bayani ne dangane da wasu
sarautu da suka shahara ga aikata hidima da samar da tsaro a ciki da wajen
fadar Sarki. Waɗannan sarautun kuwa, sarautu ne da ake yi a
cikin zuri’ar bayin
sarki tun a jiya da kuma yau. Akan yi sarautun ne a bisa gado. Daga cikinsu
akwai;
i.
Shamaki:
Shi ake fara gani kafin sarki ya fito daga cikin gidansa kuma shi ke yi ma
mutanen iso ga sarki. Wannan sarautar tana da muhimmancin gaske domin bincikar
abin da yake tafe da mutum kafin ya ga sarki. Irin wannan matakin kuwa, yakan
taimaka wajen magance matsalar kai wa sarki marmaki a fada.
ii.
Sallama:
Aikinsa shi ne raba kyautar sarki, musamman ga makaɗan fada. A wasu lokuta kuma
yakan isar da gaisuwar talakawa zuwa ga sarki, tare da yi masu iso wajen sarki.
Wannan ya nuna cewa a tsarin sarauta a ƙasar Hausa sarki mutum ne mai darajar gaske, wanda
ake taka- tsantsan da barin jama’a na saduwa da shi kai tsaye. Domin ka da wani abin
shairi ya same shi.
iii.
Shimfiɗa:
Wannan sarautar akan kira ta da suna “Baraya”
a wasu masarautun ƙasar Hausa, shimfiɗa ne yake da hakin kula da
shimfidar sarki da abin da duk ya shafi shimfiɗun masarauta da tufafi da
abinci. Wannan mutum ke kula da abincin da sarki zai ci musamman idan sarki ya
fita rangadin yankinsa. Ana yin haka ne domin ka da sarki ya sha guba a cikin
abinci.
iv.
Barga:
Shi ne mutumin da ke kula da abincin dawaki da kilisarsu da tafiyarsu da kuma
zaɓensu
da ƙaruwar
ko raguwarsu. Haƙƙinsa ne ya zaɓI
dawakan da za a tafi da su wajen yaƙi.
v.
Zagi:
Shi ne wanda ke yi wa sarki ja gaba duk inda za ya tafi, yana riƙe
da kayan doki ya kuma dafa wa sarki sirdi a lokacin da yake hawa da sauka da
kuma riƙe
buta idan shantali baya kusa. A wasu masarautu irin wannan sarauta ana kiran
tad a suna “Ma ja sirdi.”
vi. Uwar Soro: mahaifiyar sarki ko ‘yarsa
ko gwaggonsa, ko uwar gidansa wadda ta wanke shi wadda ke iya gaya masa duk
abin da ake jin nauyin gaya masa, aikin ta shi ne kula da huldar cikin gida a
tsakanin sarki da ‘ya’yansa da danginsa musamman mata. Sannan takan ci
abincin da aka yi ma sarki domin ta tabbatar da daɗinsa, da lafiyar abincin.
vii. Jekadiya: Mace ce wadda ke isar da saƙon
sarki zuwa ga iyalinsa ko saƙon ‘ya’yansa da ƙannensa zuwa ga sarki. Galibi akan naɗa babbar yayar sarki ko
gwaggonsa a wannan sarauta. Aikinta ya so ya yi kama da na Uwar soro.
3.2 Sarautun
Bayi Masu Kula da Fada.
Wannan kaso na masu hidimar tsaro su ne waɗanda
alhakin tsaro a fada ya rataya a kan su. Fada waje ne da ake shirya doka da
tsare ta, hakan ya sa ake da wani tsari na musamman domin samar cikckken tsaro
a fada, kuma hakan ya sa ko a zaman fada aka yi tsari na musamman domin yin
kafa-kafa da samun matsalar tsaro a fadar sarakunan ƙasar Hausa. Daga cikin waɗanda
ke janye da akalar tsaro a fada sun haɗa da;
Sarkin Dogarai
Sarkin Fada
Tsara
3.2.1
Sarkin Dogarai
Shi ne shugaban
dogarai a fada. Shi yake da alhakin yanke hukunci ga duk wani dogari da ya
aikata wani laifi a fada ko cikin gari, kafin a sanar da sarki. Sarkin dogarai
mutum ne da ya ƙware a sha’anin tafiyar da
mulkin gargajiya. Yana ɗaya daga cikin makusantan sarki, hakan ya sa da wuya sarki ya zartar da
wani abu a fada ba tare da saninsa ba. Yana bayar da gudunmawa ga tsaro a fada
da kuma faɗin masarauta.
3.2.2 Sarkin
Fada
Shi kuwa sarkin
fada shi ne shugaban fadawa baki ɗaya. Shi ke kula da yadda lamarin fadanci ke gudana a fada, yakan bayar
da shawara ga sarki idan bukata ta taso. Akan yi shawara da shi masarauta
dangane da lamarin tsaron gari ko yanki.
3.2.3 Tsara
Wannan shi yake
kula da yanayin zama a fada. Shi ne ked a alhakin kula da inda baƙi za su zauna a cikin fada musamman ga wanda bai sa yadda tsarin zaman
fadar yake ba. Ga al’adar masarautar ana zama ne gwargwadon darajar ‘yan
majalisar sarkin. Yana daga cikin aikinsa hana duk wata baƙuwar ijiyar dab a ya aminta da ita ba ga ganin sarki.
3.3 Sarautun
Kula da Tsaro na Gari
A nan, takardar ta zaƙulo wasu daga cikin masu hidimar bayar da
tsaro ne a cikin gari. Gudunmawarsu a tsarin sarauta a ƙasar Hausa shi ne, domin tabbatar da zaman
lafiya da kwanciyar hankalin al’umma. Ire-iren waɗannan
sarautun kuwa sun haɗa da;
- Ƙamshin
gari
- Barade
- Makama
- Maza Waje
- Yari
- Sarkin Baƙi
- Baushi
- Ƙofa
Ƙamshin
Gari
Kamar yadda sunan
ya nuna, wannan mutum ne daga cikin fadawan sarki wanda yake da alhakin shaƙo abubuwan da ke gudana a cikin gari da kewaye domin ya kawo wa sarki
rahoto na abin nan take. Daga cikin abubuwan da yakan samo labarin abkuwarsu
sun haɗa da; sata da kwartanci da faɗace-faɗace da duk wani laifi da ake zargin mutum da aikatawa. Idan Ƙamshin ya kawo wa sarki labarin faruwar wani abu a masarauta, lallai
sarki ba ya wasa da ɗaukar matakin hukunta duk mai laifi. Hakan ya sad a zarar aka ga Ƙamshin gari a unguwa ko ƙauye, to, lallai za a ga cewa mutane sun sha jinin
jikinsu domin ka da a ce ga abin da suka yi. Aikinsa ya yi kama da ma’aikatan farin kaya (SS) na yanzu.
Sarkin Yaƙi (Magayaƙi)
Shi ne shugaban
rundunar yaƙi, idan yaƙi ya tashi shi yake
tanadin abubuwan da ake buƙata, shi ne kuma yake aikawa sarakuna da sanarwar yaƙi.
Barade
Shi ne ke
shugabantar mayaƙan sama wato waɗanda suke akan dawaki a wajen yaƙi, sarautar ta kasu
kashi biyu, akwai Baraden ‘ya’yan sarki akwai kuma Baraden sarauta watau Baraden sarki.
Maza Waje
Babban aikinsa ga
samar da tsaro shi ne yake bayar da sanarwa idan aka sami labarin wasu za su
kawo hari a yankin. Saboda haka, da an ji sanarwarsa to, sai batun azama a fita
fagen daga. Watse da irin wannan tsari a zamantakewarmu ta yau ya haifar da
samun yawaitar ‘yan ta’adda a cikin al’umma.
Sarkin ƙofa ( Ƙofa)
Shi ke tsaron ƙofar gidan sarki, ya rufe ta, kuma ya hana wanda ba a yarda da shiga
gidan sarki ko fada ba. Ga al’adar Hausawa, Ƙofa shi ne shugaban masu kula da ƙofofin gari domin
samar da cikakken tsaro. A nan ma idan an lura al’adar tsaro ta amfani da ƙofofin gari ya zama abin tarihi.
Sarkin Baƙi
A zamanin da, babu
garin da ba a samun sarkin baƙi a faɗin ƙasar Hausa. Sarkin baƙi mutum ne da akan naɗa tare da aza masa nauyin kula da shiga da ficen baƙi a faɗin gari. Shi ne yake saukar da baƙin da aka yi a
gari. A yau wannan al’adar tsaro ta yi
rauni ƙwarai.
Yari
Wannan sarauta ce
ta kula da ladabtar da masu laifi. Al’ummar Hausawa suna da wannan tsari tun
kafin haɗuwar su da Turawa. Galibi idan aka kama wani mai laifi akan bai wa Yari
ajiyar sa ne na tsawon wasu kwanaki. Bayan zuwanTurawan Mulkin mallaka ma aikin
Yari bai sauya ba, domin sarakuna kan kai masu laifi a gidan Yarin gari ne
kafin a tura su zuwa kotu ko ga ‘yansanda. Har yanzu a wasu ƙauyukan ƙasar Gummi akan kai dabbobi da aka kama a gonaki
idan Fulani sun yi ɓarna a gidan Yari domin hukunta su.
4.0 Waiwaye a Kan
Matsalar Tsaro a Ƙasar Gummi
a Yau
Taɓarɓarewar tsaro a yankin Gummi daga bayan nan ya
samu, tun lokacin da aka fara satar shanu da garkuwa da mutane a nufin amsar kuɗin
fansa, Gummi ba ta zama ɗaya daga cikin garuruwa ko yankunan da suka
sami wannan matsala ba. Sai dai duk da haka, akwai rashin jituwa na Manoma da
Fulani da ake samu nan da can. Matsalar rashin tsaro ta samu ne bayan har an yi
zaman sasantawa da ‘yan ta’addan jihar Zamfara. Sai kawai suka mayar da
hari a wasu sassa na ƙasar
Gummi, musamman a garuruwa da ƙauyukan da
suke da daji mai ruƙuƙi, wato a yammaci da kudancin Gummi ke nan
kamar Barikin Daji da maƙwabtan ƙauyukan da suke kusa da garin.
4.1 Garuruwa
da Ƙauyukan da
Suke Fuskantar Matsalar Tsaro a Ƙasar Gummi
A nan muƙalar za ta
zayyano garuruwan da suke fuskantar matsalolin rashin tsaro a yankunan ƙasar Gummi. Daga cikin fitattun garuruwa da ƙauyukan da suke fama da waɗannan
‘yan
bindiga sun haɗa da;
1. Barikin Daji
2. Bardoki
3. Gayari
4. Ƙaraye
5. Gwalli
6. Babban Rafi
7. Gyalange
8. Gaftu
9. Lanke
10. Unguwan Noma
11. Illelar Auwal
12. Ɗan’awo
13. Gidan Illo
14. Tudun Baushe
15. Sago
16. Kabawa
17. Kagali
18. Masallaci
19. Maikada
20. Birnin Tudu
21. Falale[5]
4.2 Sigogin Matsalar
Tsaro a Ƙasar Gummi
Yanayin taɓarɓarewar
tsaro a ƙasar Gummi
kamar sauran sassan Arewacin Nijeriya da jihar Zamfara yana tafiya ne bisa siga
ɗaya. Galibi masu addabar mutane sukan aiwatar
da waɗannan nau’ukan ta’addanci
a cikin garuruwa da ƙauyuka ko
kuma a kan hanya. Waɗannan sigogin rashin tsaron kuwa sun haɗa
da;
i. Garkuwa da Mutane
ii. Satar Shanu da ɓarnata
kayan gona (Abinci)
iii. Kisan Gilla da ƙare dangi
iv. Fyaɗe ga mata da ‘yanmata
4.2.1 Garkuwa
da Mutane
Wannan babbar matsala ce da ta saka dubban
mutanen yankin shiga cikin zulumi da ko ta kwana a cikin garuruwa da ƙauyukan yankin. Dukkan garuruwan da aka
lisafo a sama suna fuskantar wannan barazana daga ‘yan bindiga.
4.2.2 Satar Shanu
Matsalar tsaro a ƙasar Gummi da satar shanu ta soma, har abin
ya gagari magancewa. Ana samun irin wannan matsalar ne a yankunan da suke zaune
cikin daji sosai da Fulani. Wani mugun abu da yake faruwa a wasu lokuta da
mutanen ƙauyukan ne
ɓarayin ke haɗa
kai a yayin aiwatar da satar.
4.2.3 Kisan
Gilla
Wannan nau’in ta’addanci
yakan faru a dukkan wuraren da wannan muƙala ta
rattaba. A wasu lokuta ‘yan
bindigan kan aike da saƙon kai
hari a gari kuma su je, su yi ɓarna yadda suke so, su wuce. Akwai dalilai da
dama da suke haifar da irin wannan ta’addanci
a yankin Gummi, galibi ɓarayin sukan kai irin wannan hari ne inda
suka sami turjiya daga mutanen ƙauye ta
fuskar ƙalubalantar su ko fito-na-fito da su har su
yi wa ɓarayin ɓarna, ko kuwa a garuruwan da suke da matasa
masu aikin sa-kai.
5.0 Dalilan
Taɓarɓarewar
Tsaro a Ƙasar Gummi
Dalilai da yawa sun taimaka wajen taɓarɓarewar
tsaro a Gummi da kewaye. Daga cikinsu kuwa akwai;
i. Rashin Ilmin addini da na zamani ga jama’ar yankin.
ii. Rashin nagartattun sana’o’in
dogaro da kai.
iii. Rashin isassun jami’an tsaro a cikin garuruwa da ƙauyukan yankin.
iv. Rashin wayar da kai ga jama’ar yankin game da amfanin zama lafiya.
v. Yawaitar ‘yan rashin kishin ƙasa da suke haɗa
kai da ‘yan ta’adda wajen aiwatar da miyagun ayyukansu.
vi. Sakacin hukuma da jami’an tsaro wajen daƙile hare-haren ‘yan ta’adda
a yankin.
vii. Ayyukan ‘yan sa kai na kashin gilla ga Fulanin yankin.
viii. Sakacin shugabannin Fulani da Manoman
yankin wajen magance matsalar ɓarnar kayan gona.
ix. Rashin hanyoyin sufuri a cikin dazukka da
garuruwan da suke a nesa da manyan garuruwa.
x. Sakacin Iyaye da shugabanni wajen
tarbiyyar matasan yankin.
xi. Rashin Jami’an tsaro masu kula da kan iyakokin Gummi da
makwabtanta.
6.0 Dabarun
Magance Matsalar Tsaro a Ƙasar Gummi
Magance matsalar tsaro da ake fuskanta a
Gummi da jihar Zamfara baki ɗaya abu ne mai sauƙi idan an yi amfani da waɗannan
matakai kamar haka;
a. Samar da
kyakkaywar makoma ga matasan yankin wajen ilmantar da su da kuma samar masu da
sana’o’in dogaro ga kai. Yin haka zai hana su haɗa
kai da baƙin haure
wajen addabar ‘yanuwansu
ta hanyar garkuwa da su ko satar dukiyoyinsu.
b. Inganta
tarbiyyar matasan yankin daga matakin gida da unguwa da sauran jama’a.
c.
Tsayar da mulkin adalci daga sarakuna da
shugabannin siyasa. Hakan kuwa ba zai samu ba sai sarakuna sun kawar da kwaɗayin
samun kuɗi cikin sauƙi daga talakawansu. Samuwar hakan ne ya sa
ake zargin wasu sarakuna da hakimai da hannu wajen rura wutar rashin tsaro a
Zamfara.
d. Tsare dokokin
Allah SWA da martaba su.
e. Martaba
dabarun tsaron ƙasa irin
na gargajiya da muka gada kaka da kakanni.
7.0 Sakamakon
Bincike
Wannan muƙala kamar yadda aka gani ta yi nazarin rashin
tsaron da yake addabar yankin Gummi a yau da kuma tantance wuraren da matsalar
tsaron ta yawaita da fayyace dalilan rashin tsaron da hanyoyin magance shi.
Dangane da haka, muƙalar ta
taskace sigogin rashin tsaro guda uku da ake da su a ƙasar Gummi da gano garuruwa da ƙauyuka guda ashirin da ɗaya
(21) da suka fi fuskantar matsalar. An fayyace dalilai guda goma (10) da suka
haddasa samuwar rashin tsaro a ƙasar Gummi
tare da tsakuro dabaru ko hanyoyin magance matsalar tsaro guda biyar (5) a yankin.
8.0 Naɗewa
Wannan muƙala kamar yadda aka gani wani yunkuri ne na lalubo
dabarun magance taɓarɓarewar tsaro a ƙasar Gummi. An nazarci abin ta fuskar ma’anar tsaro da rabe-rabensa da kuma sigoginsa da
wuraren da suke fuskantar barazanar tsaro a ƙasar Gummi. A ƙarshe an fito da dalilai da kuma hanyoyin da
za su taimaka wajen magance matsalar tsaro a Gummi da ma Zamfara gabaɗaya.
Manazarta
Abbas, H (2014), Gargajiya da Tsaro: Mafita
Ga Rashin Tsaro A Ƙasa. Journal of Hausa Studies. F.C.O.E
(TECH), Gusau, Zamfara State.
Achi, B. (1985), “The Development and Functions of City Walls in
the Savanna Belt of the Nigerian Area.”
M. A Dissertation, ABU Zaria.
Adamu, M. (1979), The Hausa Factor In West
African History. ABU Press, Zaria.
Adamu, M. T. (1997), Asalin Hausawa Da
Harshensu. Ɗan Sarkin
Kura Publishers, Kano.
Alhassan, H. da wasu (1982) Zaman Hausawa,
Zaria: Longman.
Bunza, A.M. (2006) Gadon Feɗe
Al’ada, Legas :Tiwal Nigeria Ltd.
CNHN (2006) Ƙamusun Hausa, Kano: Jami’ar Bayero.
Department of State Services (2012). Manual.
Abuja: National Headquarters State Services.
Dokaji, A. A. (1978), Kano Ta Dabo Ci Gari.
NNPC, Zariya.
El-Amin, A. (2007), Hassan sarkin Dogarai. Printed in Kano.
Garba, A.S. (2020) Insecurity in Bukkuyum
L.G.A From the Lenses of Ungoverned Spaces. Paper presented at the National
conference on Zamfara Kingdom. Organized by FAIS UDUS.
Sarkin Gulbi, A. (2013), Tsafe-Tsafen
Dimokuraɗiyya. Maƙalar da
aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa na farko da Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero Kano ta shirya daga ranar 14-16 ga Janairu,
2013.
Sarkin Gulbi, A. (2014), “Magani A Ma’aunin Karin Magana.” Kundin Digiri na Uku. Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato
Yahaya, Y. I. (1988), Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. NNPC, Zaria.
[1] CNHN,
(2006) Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero Shafi na 452.
[2] Wani kauye ne a
yankin karamar Hukumar Talata Mafara
[3] Hira da Mai martaba
Sarkin Gummi Alhaji Aliyu Abara Gummi Emir na biyu, A gidansa ranar Assabar
12-2-2000 da misali karfe 10:00 na safe. Mun yi wannan tattaunawa ne kafin ya
zama Sarki.
[4] Wannan bayani an same
sa ne ga Ubandoman Sifawa Hakimin cikin gari, ɗan kimanin shekara sittin a gidansa, ranar
Juma’a 28-08-2014, da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
[5] Akwai sassacin
faruwar irin wannan ta’addanci a cikin garin Gummi da wasu kauyukka
da dama da suke cikin karkara inda babu rukukin daji a zagaye da su.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.