Ticker

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 05)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  05)

Baban Manar Alƙasim

Akwai kuma batacciyar soyayya, ita ce soyayya maras tabbas, abin da aka sani kishiyyar soyayya ƙiyayya ce, soyayya takan sanya jin dadi ne da farin ciki da sakewa, ƙiyayya kuma ta sanya damuwa da lalacewa, shi ya sa in mutum ya ji wani aljani ya ce yana son wane ko wance yake shakkar haka, domin wanda ake ƙaunar kullum cikin wahala za ka isko shi, a maimakon sakewa da walwala da walawa. Wannan batacciyar soyayyar tana da alamomi ne a wargaje, sai dài kowacce alama tana da masabbabinta, amma a ƙarshe sukan ba da sakamako guda daya:-

a) Alokacin da aka sami soyayyar da sha'awar saduwa ce gaba, babu ko shakka ba ta iya haihuwar 'ya mai ido, shi ya sa addini ya gindaya wasu shingogi don tsarkake rai, dukiya da mutunci, yanzu dai duba auren holewa (Mutu'a), in za ka auri mace na tsawon sa'a guda kuma ka bakka ta sadaki, amma da zarar sa'ar ta gama cika shikenan kudinka ya ƙare, ka ga a nan ba a tsare maka dukiyarka yadda za ka amfana da ita na tsawon lokaci ba, addini ba zai yi umurni da asara ba, shi ya sa ma nan da nan ya hana caca don tsare dukiyar jama'a.

In kuwa maganar soyayya za a yi, da wahala duk wani mai hankali ya yarda da cewa akwai wata soyayya ta gaskiya da za a iya yin ta na 'yan mintuna ko sa'o'i ko kwanukka da watanni, soyayyar gaskiya akan yi ta ne na dindindin, in wani dalili ya shigo to ba da gangan aka sanya ba, to a lokacin da namiji zai sadu mace ya rabu da ita na tsawon minti 15 da zarar kudinsa ya ƙare, shin a kan kudin ake soyayyar ko a kan kwanakin da yi alƙawari?

A nan babu wani zancen soyayya, macen kudin kawai take nema kuma ta samu, in zai ci gaba da irin wannan soyayyar to lallai sai ya ƙaro kudi, shi kuma jikinta kawai yake nema, in ya gama amfani da ita shi kenan, ita da banza kuma duk daya, ta zama tamkar karuwa, cinta da shanta duk na ta ne bare a yi zancen sutura ko tausayi da soyayya. Wannan soyayyar tabbas batacciya ce, don mai yin ta ba ya buƙatar ƙaruwa da ita, ita macen ba ta fatar samun ciki, don ta san dan ba zai bi uban ba, shi uban da aka ce dansa ne yana shakku, don mazinaciya ba ta kwanciya da mutum guda, tambayar a nan: Shin da gaske ne wannan dan na sa ne, ko na wani ne? Cinsa da shansa a wuyar wa suke? In da soyayyar gaskiya ake yi murna ake yi in ciki ya shiga ta kowani banagare, ita da mijin, 'yan uwanta da na sa, wannan soyayya ta holewa ba ko shakka mai cutarwa ce, addini ya fadi ƙarara babu cuta ba cutarwa.

b) Soyayya ta zamto ba ta da manufa, saurayi yana soyayya ne amma shi kansa bai san dalilin da yake yi ba, galibin irin wannan soyayyar ta fi yawa a makarantu da jami'o'i, inda dan talaka zai fada soyayya da 'yar mai kudin da tabbas ya san ba zai aure ta ba, ko shi ke da kudin gidansu ba za su yarda ya wuro mace kamarta ba, sau da yawa samari kan ƙulla irin wannan soyayyar, wani lokaci ko karatu ba sa iyawa, har ma a fadi jarabawa ko a sami ƙaramin sakamako duk a banza, tunda in suka gama karatu ba wanda zai sake ganin wani, amma fa in ya zo da tsautsayi ko ba a sami ciki ba an dai bata juna, addini kuwa ba ya umurni da alfahasha.

c) Samun rudu wurin soyayya, wannan kuwa takan kasance ne inda wata budurwa take mugun son wani saurayi, shi kuma sai ya riƙa biye ma ta ba tare da zuciyarsa tana wurinta ba, akan dade ana yi amma babu wani abin sha'awa na a zo a gani, ko ya kasance ita yake ƙaunar ya ga ya mallaka amma zuciyarta ba ta tare da shi, tana lallaba shi ne kawai don kar a ce ta wulaƙanta shi, sau da yawa saurayin yakan ji labarin ta yi aure ne kawai, ina da abokai guda biyu, daya ya je zance ne aka ce masa ta yi aure da mako biyu, dayan kuwa ce masa ta yi ka zo ranar kaza, da ya zo sai isko ana daura aurenta da wani, su biyu dukansu sun nuna soyayya ta gani ta fadi ga samarin amma ga yadda ta ƙarasa.

d) Ya kasance ana nuna soyayya ta ƙarshe amma bisa wata fa'ida da ake samu, wasu lukutan irin wannan soyayyar ta fi faruwa a karkara, koda yake takan faru a marayan ma, yarinya ce guda amma tana da samari kusan biyar, ina ƙarami ma na ga yarinyar da ta ajiye lefen mutum 6, kuma saurayi daya tal za ta aura, abin da ya sa ta haƙura da su don 'yan kurdin da suke bakka ta, su ma samarin a kan sami mai 'yammata da yawa, yau yana nan gobe yana can, abin da yake so kawai ya riƙa jin dadin muryarsu ko ya yi alfaharin yana da 'yammata kaza.

e) Sai kuma lokacin da samari da 'yammata za su sami kansu tsundum cikin yanayin da kowa yake hanƙoron biya wa wanda yake raya cewa masoyinsa ne buƙata ba tare da an daura aure ba, galibin irin wannan auren ko an yi bai cika yin albarka ba, don an gama tamfatsewa kamin aure, duk sun san kawunansu cewa ba kamammu ba ne, irin wannan sau da yawa mijin yakan riƙa shakkun alaƙarta da kowani namiji, ita ma duk lokacin da ya fara alaƙa da wata ta riƙa zarginsa kenan, an ƙulla soyayyar kan barna da sabon Allah. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Post a Comment

0 Comments