Ticker

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 06)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  06)

Baban Manar Alƙasim

Ita ma batacciyar soyayyar tana da tata tasirin wanda alamunta suna bayyana ya zama dole ga mutum ya nemi magani:- a) Mutum ya gaza bayar da aikinsa kamar yadda ya dace, don zuciyarsa kullum tana wajen wata, duk dan abin da ya samu ya bakka ta, in ba ta karba ba hankalinsa ya tashi, ya gaza tsayuwa a wajen aiki don yana son ya je wajen masoyi, a irin wannan matsayi dole a nemi matsaya, don ba ingantacciyar soyayya ake yi ba, sha'awa ita ce a kan gaba, da zarar an daura aure ita matar za ta fara ganin wasu 'yan canje-canjen da ba ta taba tsammani ba.

b) Akan sami kuma ƙunci da damuwa, masamman idan ya kasance mutum ya yi nesa da masoyi, wani lokaci mutum yakan rasa abin da yake masa dadi, har da kansa ya yanke hukuncin cewa maganin hakan kawai shi ne kasancewa da masoyi, amma da a ce ingantacciyar soyayya ce, ba a yin ta inda bai dace ba, don soyayya ce da ba a rabuwa, kuma ita masoyiyar tana da damar gamsar da shi da duk abin da yake buƙata, kuma a lokacin da yake so, a nan ba za a sami hauhawar sha'awa ba, sai dai son saduwa da masoyi gami da yi masa hidima.

c) Ƙoƙarin zama da wanda ake kira masoyi ne na gaskiya kowani lokaci, da son taban jikinsa in zai yuwu, ko taban wuraren fitina duk dai da sunan soyayya, mutum shi a kan kansa ya san ya sabi Allah, zuciyarsa za ta yi ta raya masa cewa Allah fa zai yi fushi da shi, wannan in yana da dan sauran imani kenan a zuciyarsa, na zauna da wani mutum da yake ce min ya kai matsayin da budurwar ta yi masa tayin biya masa buƙata matuƙar yana so, tsoron a kama su ne kawai ya hana shi, amma duk wani nau'i na sabo ya aikata, a nan zai kira sha'awar da take tsakaninsu ne da sunan soyayya, wata ƙila ma su ce soyayya ce ta gaskiya, alhali sam ba haka ba ne, tasirin batacciyar soyayya ne.

d) Akwai kuma nisantar 'yan uwa da abokai, da ma kowa da kowa don dai a kadaitu da wanda ake ganin masoyi ne, duk in ka raya wa zuciyarka cewa ba wanda zai hana ka zama da wance, ko kuwa ita ta ce in sama da ƙasa za su hadu sai ta auri wane, ba shakka wannan tasirin makauniyar soyayya ne, wanda ake ce ma ta "hana ganin laifi" irin wannan ko abokkai da ƙawaye ba su cika ba da gudummuwar a zo a gani ba wajen taimakon masoyan, domin abin da masoyiyar take so ƙawarta take ba ta shawara, shi ma saurayin bai samun gamsasshiyar shawara wajen abokansa sabo da wannan dalilin.

Domin a taimaka wa waɗannan masoyan dole a bi wasu 'yan shawarwari:-

a) Ka zabi babban dalilin da ya sa kake son wance, ko dalilin da zai sa ta karbi soyayyar wane, kar ya zama cewa kyawunta kawai da tsarin surarta suka hisgi hankalinsa, ko ita ta sakankace cewa zai iya biya ma ta buƙatunta na rayuwa da zumunci don haka za ta aure shi, a yi ƙoƙari a duba lamuran da ba sa canja wa mutum, kamar dabi'u na ƙwarai, son ibada, neman ilimin addini, ko shiryarwa ta ƙwarai.

b) Ya zama dole a nisanci kallon fima-fiman batsa, da karanta littafansu, a nisanci zama da wani jinsi na daban, da son ganin wuraren da suke motsa sha'awa a jikinsa, yanzu har hotuna na batsa da bidiyo ana iya kallo a wayoyi, su kuma sukan ƙara sha'awar da in mutum bai yi a hankali ba ba shakka zai fada zuwa ga batacciyar soyayya wace ƙarshenta nadama ne, ba ina wajabta sanya niƙabi ne ba wajen hira da masoyi, ko hana zance gaba daya, amma dole a guji abin da zai dauwamar da sha'awa a maimakon soyayya.

c) Kusantar Ƙur'ani mai girma, da koyarwar Annabi SAW a hadisai tana matuƙar taimakawa wajen rage aukawa cikin baƙar soyayyar da take ƙarewa da nadama, masamman zama a wuraren karatun addini, inda ake gina mutum don ya fahimci aure ibada ne, nemansa kuma yana da tsari yadda addini ya wasafta, ba abu ne da mutum zai yi yadda ya ga dama ba, duk lokacin da mutum ya sami kansa ba ya aikin komai to ya daure ya nemi abin da zai shagalta da shi, masamman 'yan karance-karancen abubuwa masu amfani.

d) Mutum ya yi ƙoƙari ya sanya wa zuciyarsa cewa soyayya kamar dambe ce; Wanda yake kallo shi yake ganin da zai naushi wuri kaza tabbas zai yi kaye, kai da kake ciki ba ka da sararin da za ka iya hango wurin, don haka sauraron shawarwarin abokai da na gaba suna matuƙar taimaka wa matashi wajen gyarar rayuwar soyayyarsa, kar mutum ya ce ya fi kowa sanin abin da ya dace da shi, raina shawarwarin uwaye alama ce babba ta makauniyar soyayya. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  06)

Post a Comment

0 Comments