Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 10)

    Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar AlÆ™asim ya rubuta.

    Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  10)

    Baban Manar Alƙasim

    Da farko dai loacin neman aure lokaci ne mai matuƙar tsada a wurin samari da 'yammata, masamman ma idan budurwa ta fahimci wani yana neman kusantarta, kuma tana ganin za ta iya ba shi hadin kai, ko wani saurayi ya ga wata 'yar daƙwalwa tana kyarkyara, kuma ta yi masa dari bisa dari, na fadi a baya cewa duk wani abu da muke ganin al'adarmu ne mun saba, in dai addini kai tsaye bai haramta ba, sannan an sami sahabban da suka taba yi, to a fahimtata gwara a ƙaddamar da shi a kan al'adar.

    Abin nufi, duk wata mace, babbace ko budurwa, in dai ta ga wani saurayi ya yi ma ta, kuma tana sha'awar a ce ya zama uban 'ya'yanta, tana da damar da za ta gwada kafa masa tarko, in ta yi ruwa rijiya, in ta ƙi masai, ban taba daukar kaye wajen neman aure wani ƙaton abu ba, bare na dauke shi abin kunyar da za a bar halas dominsa, na nemi aure sau 3 ina shan ƙasa, wannan bai taba sa na yi ƙasa a gwiwa ba, sai dai na ƙara daura damaran neman wani, a ƙarshe dai na ci nasara. Mace ba dole ba ne ta bude baki a cikin jama'a ta ce wa saurayi "Ina son ka aure ni!"

    Kamar yadda muka gani a hadisai da littafan tahiri, tana da hanyoyi kala daban-daban na isar da saƙo, kuma tsakani da Allah saƙonta yakan isa duk inda take ƙoƙarin aikawa, wani lokaci a yi dace, wani kuwa a dawo hannu rabbana, sai dai da za mu nade hannuwammu mu ce ko mace tana sha'awar ta kusanci wani kar ta yi wani motsi har sai in shi ne ya furta, gaskiya za a rasa wasu damammaki wadan da Allah ne kadai ya san iyakarsu, masamman wannan lokaci da maza suke mutuwa kamar ƙwanyin kaji, ga alamomin tashin ƙiyama nan suna ta bayyana. Sannan a zahiri ba dole ba ne sai masoya sun dace da juna dari bisa dari, wani lokacin akan dan sami loba kadan, to amma idan aka yi dace da musayar soyayya ta gaskiya, cikin kyakkyawar niyya da gaskiya da amana, sai ka ga abin ya ba wa kowa sha'awa, don Allah ya ga zuciyoyinsu kuma ya sanya albarka a cikin lamuransu, ita mace masamman wace ta girma a tsakiyar matattarar Hausa-Fulani, da dama akan tauye ma ta hakkin zaban wanda take so, kamar dai yadda galibin alƙalumarmu suke rubutawa, duk kuwa da cewar muna sane da ba ta da ƙarfin ƙwaƙwalwar da za ta iya rabe dan kuka da dan tsamiya a daidai wannan lokacin, takan dogara ne kacokan a kan wanda zuciyarta take ƙauna, ba tare da hangen ko wannan nunin ƙaunar da yake yi ma ta zai ci gaba ko zai yanke ba.

    In mun tafi a wannan fahimtar, ba na tsammanin cewa haƙƙin na ta kenan a bar ta ta zabo tumun-dare, haƙƙin uwaye ne su taya ta neman wanda zai so ta so na gaskiya, ya kula da ita da buƙatunta, ya girmama ta a matsayinta na mace, ya kare ma ta mutuncinta da sirrorinta, ya zama ma ta tamkar uba a lokacin da ta rasa uwaye, masoyi a yayin da take ja-in-ja da sha'awarta, sannan ƙawa a sa'ilin da take neman abokin sirri, aure ba zina ba ne da za a ba mace kudi a hole da ita na 'yan wasu mintoci ko kwanaki, ba kuma ƙaramin abu ne ba da yake buƙatar tsayuwar mutum guda kacal, tsarin rayuwa ne da yake buƙatar hannaye da dama, masu ba da shawara da tsarkakakkiyar zuciya. A daidai wannan gabar zan so na yi magana kan abubuwa guda uku masu matuƙar mahaimmanci:-

    1) Duk lokacin da saurayi ya yanke shawarar neman wata budurwa ya tabbatar da cewa tabbas ta yi masa gwargwadon yadda yake buƙatar ta, ya yi tunanin cewa ita mace ce da zai yuwu su iya fahimtar juna, cikin girmamawa da sanin mutuncin juna, ya kuma fahinci cewa ita fa yadda take mace, haka ƙwaƙwalwarta take a mace, zuciyarta ce take harbawa kowani lokaci, don haka dole ya san cewa sai ya riƙa yi ma ta hanzari tun daga wurin fara nemanta har zuwa lokacin da Allah SW zai raba su.

    2) Kar ita budurwar ta yarda alaƙar da take tsakaninsu ta zama sirri, mutum na farko da zai fara sanin abin da take ciki mahaifinta, in kuma tana da tabbacin cewa mahaifiyarta kamar ƙawarta ce sai ta fara da ita, galibin abin da shari'a ta tanadar shi ne: Saurayi ko iyayensa su nema masa damar da zai fara magana da yarinyar, wasu uwayen in suka ga yaro ne manemin 'yarsu sukan ce ya turo uwayensa, don ƙulla magana gemu da gemu, wace ta sake harkar sha'awa ta ci gaba da saurayi ba tare da shigowar mahaifanta ba, in abu bai yi kyau ba a ƙarshe ita ta so, tana da ƙima da darajar da za ta yi hira da saurayi a dakin mahaifiyarta da rana ido na ganin ido, kowa yana gilmawa. Haka shi ma saurayin da budurwarsa ta ƙi yarda ya sami mahaifanta, wai sabo da wani uzuri, shi ma ya dau haske, don ginarsa ba za ta cin ma ruwa ba.

    3) Sirrorin masoya dole ya kasance a tsakaninsu, amma duk lokacin da budurwa ta ji wata maganar da ba ta gane ba, dole ta nemi shawarar wace ta fi amincewa da ita a kan kowa, namiji makiri ne, wani lokaci yakan dama hura kuma ba sha zai yi ba, sai ya bar ƙudaje su yi ta bin ta, harkar rashin gaskiya ita ake boyewa, Annabi SAW ya ce: Sabo shi ne abin da yake damunka a zuciya kuma ka ƙi yarda mutane su sani._ A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.
    Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  10)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.