Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren
Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma.
A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban
Manar Alƙasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 11)
Baban Manar Alƙasim
Hausawa suka ce "Zo mu zauna, zo mu saba"
in dai har mutum biyu za su yi alaƙa kowace iri ce
kuwa dole a sami dalilin da zai hada su rikici, sai dai ana sa rai za su sami
abin da zai janyo hankalinsu su daidaita tsakaninsu, galibin abubuwan da suke
hada mutane fada su ne:-
1) Rashin damar fahimtar juna a tsakanin maneman
guda biyu, shi saurayin ya gaza fahimtar cewa ita fa mace ce, kuma ƙasa da
shekarunsa, ba ta alaƙoƙi da mabambantan jama'a kamar yadda yake da su,
kuma takan dogara ne kawai da abin da zuciyarta ta ba ta, ita kuma ta kasa gane
cewa shi maigidanta ne ba tsaranta ko ƙaninta ba.
2) Sai kuma rashin daidutuwar yanayi a tsakaninsu,
wani namijin mai kishin gaske ne ga azaban riƙo, ita kuma
tana da samarin da ta saba da su tun kafin ta fara ganinsa, amma lokaci guda
sai ya nemi ya raba ta da su, ko in yagan ta da wani namiji ko bai san me suke
tattaunawa ba sai nan take ya haye, ko ta ba shi haƙuri sai ya yi
kamar zaginsa ta yi, ita kuma ta ga cewa ba za ta yarda da wannan ba, ko kuwa
ta ce ba ta riga ta zama matarsa ba don haka ba wata dokar da zai iya ƙagara ma ta,
saurin fushi, ko zargi ba dalili, ko yawan surutu a kan masoyi yana saurin kawo
matsalar rabuwa tsakanin manema.
3) Wani lokaci kuma akan sami sabani ne game da
abin da ya shafi kudi, sau da yawa zumbuli bai ƙaunar abin da
zai tabi aljuhunsa, in ya kasance yarinya mai yawan roƙo ce, ko mai
kwadayin abin hannun saurayi ce tabbas dayan abu biyu zai faru, ko dai ya yi
sa'ar sauke ma ta inji, ko ya nemi rabuwa da ita, gwargwadon yadda mace ba ta ƙaunar marowaci
da mai ƙoro, haka namiji ba ya son mace mai kwadayi da mai
roƙo, Annabi ya
fadi a wani hadisi cewa: Ka guji abin hannun mutane sai su so ka.
4) Wani sa'in kuma ba waɗannan kadai ba,
in ya kasance daya cikinsu bai iya ma'amalla ba tabbas dayan zai guje shi, mace
mai yawan feleƙe da surutu, da harka da wasu mazan ba kamun kai,
ko ba ta wani abu da su, samarin sukan guje ta, haka namijin da bai iya gyara
kansa bai sakin fuska, sau da dama 'yammata sukan ji tsoronsa, in ka zama mai
kwakwazo da yawan fada, lallai za ka kori 'yammatan da suke zagaye da kai.
5) Wani lokacin kuma tazarar da ake samu a tsakanin
masoya ce take wargaza kan manema, na san wani mutum mai haiba da sifar girma,
in ya dau wanka sai ka yi zaton wani alhaji ne, ya sami kansa cikin soyayya da
wata lauya, alhali shi ko digiri bai fara ba, abokansa da dama ba su goyi baya
ba, haka malamansa, ban san uwayensa a cikin gida ba, to ko shi ne ya ba ta tazara
mai fadin gaske zai riƙa raina ma ta a abubuwa da dama, ko ma ya riƙa kiranta
jahila, shi ya sa wasu lokutan akwai buƙatar duba
daidaituwar wayewa, masamman in ya kasance ita ce a gaba da shi.
6) Sabanin fahimta ta ɓangaren addini: Wannan ina nufin masu addini guda kamar
'yan Izala da 'yan dariƙa, wadan da a fahimtar aƙida suka sami
sabani ba wai a ita kanta aƙidar ba, koda yake an fara gyara wasu abubuwan a
yau, dan Izala yana iya auren 'yar dariƙa, a baya in
uba ya ji cewa dan Izala ne saurayin 'yarsa sai dai su rabu, yanzu kuwa ba haka
ba ne, amma tabbas Shi'a wani sabon addini ne wanda ya zama dole uwaye su san
inda za su sanya diyarsu, sau da yawa mace tana kan fahimtar mijinta ne.
7) Shigar wasu bangarori cikin lamari tana daya
daga cikin musabbaban haifar da sabani a tsakanin manema guda biyu, wasu ƙawayen ba su da
adalci, dazarar wata ƙawa ta sami saurayi na gari sai ta yi ƙoƙarin zugata ta
yi masa laifin da za su rabu har abada, daga bisani kuma ita ta tura kanta,
wani lokacin kuma abokai ne suke hana saurayi ya daidaita da yarinya, sau da
yawa wata takan sami saurayi na ƙwarai, in wani
ya taba nemanta ta wulaƙanta shi, sai ya yi aiki da wasu wadan da za su kai
gulmar cewa 'yar iska ce ko tun farko, na taba jin wace aka soka wai ta yi fim
din batsa, nan take aka watsa tsakaninta da saurayin.
8) Uwaye mata ma ba a bar su a baya ba, in ya
kasance uwar tana da wanda ta ajiye zai auri 'yarta, masamman in dan uwanta ne,
to ko yarinya ta yi saurayi a waje da wahala in uwar ba ta raba tsakaninsu ba,
haka in kishiyar uwar ce take riƙon yarinyar, ya
zamo uwar ba ta a gidan, kuma tana kishi da uwar, ga 'yar ta sami saurayin
kirki, in ba a yi sa'a ba ita ma matsala ce, don kuwa za ta iya ƙulla makircin
da za ta raba su, su kuwa maza wannan na kai tsaye ne, wani lokaci ko sabanin
fahimta ce a tsakaninsu da uwayen yaro ko yarinya auren da ba za a yi ba kenan.
A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.