Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 13)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  13)

Baban Manar Alƙasim

Idan soyayya ta tsaya a kan kula da juna ta ɓangaren abin sakawa a bakin salati, ko matsuguni, ko sutura, ba shakka dabbobi da tsuntsaye ga wanda yake lura da rayuwarsu suna yin sama da abin da mu mutane muke yi, hatta ta ɓangaren saduwa da ƙoƙarin biyan buƙatar juna a matsayin ma'aurata kuma masoya, ga ƙaramin taƙadiri nan zakoki, birai, tantabaru da giwaye, Allah SW ya bambanta mu da sauran dabbobi ta fuskoki daban-daban. Dan adam shi yake tunanin wa zai nema? Ya dabi'un wanda zai nema suke? Ya aƙidu da tarbiyarta? Ya iyayenta suke?

Sannan ya yi tunanin irin 'ya'yan da za ta haifa da irin tarbiyar da za ta ba su, shi ne din dai yake tunanin cewa aurennan fa ibada ne, kuma lada zai samu idan har ya yi, ya riƙi surukai a matsayin iyaye, ya je zance gidan yarinya yadda iyayenta za su kalli dabi'unsa su tantance shi, su tabbatar da cewa lalle ya isa ya zama uban jikokinsu. Kafin a fara tunanin wasu hidundumu na sanayya da al'adu wadan da za su tabbatar wa uwayen yarinya cewa tabbas yaronsu zai iya riƙe diyarsu, ta fuskar mu'amalla da zamantakewa? To idan ba zai zo ba sai da daddare, kuma daga shi sai ita, sannan a can waje yadda ba wanda zai san abin da suke ƙullawa tabbas an yi kuskure wajen fassara ma'anar soyayya, ina da tabbacin in kishi da kula da manne wa juna su ne soyayya, to ba 'yan adam ne kadai suke yi ba, kuma dabbobi sun fi mu iyawa, don kuwa ba sa yi sai sun yi shaƙuwar aure, mu kuwa kafin aure ne namu yake da ƙarfi, bayan haka kuma sai zaman haƙuri da juna. Don me aka halicci ma ce?

Don ta yi gogayya da namiji a matsayin abokiyar halitta? A'a, don ta zama wa namiji ne ruwa mai bice wutar sha'awa da kadaituwa, da rigingimun waje, wadan da suke balbala a zucuyarsa, ta yi masa magana mai dadi da Allah ya siranta ma ta dominsa, ya raunana duk wasu gabobinta yadda za ta iya yi masa hidima, ya sanya murnarsa da farin cikinsa a hannunta, ya mallaka ma ta zuciyarsa yadda ko'ina ya je tunaninsa yananan tare da ita, hanƙoronsa kawai shi ne ya kare ta da mutuncinta, ya zama ma ta komai har ta manta da iyayen da suka haife ta ma, in don hidima ne ba don uwayantaka ba, duk in abin farin ciki ya taso sai a tuna masoyi, haka in na baƙin ciki ya taso masoyi ne farkon wanda yake fadowa rai.

Da yawa mata da 'yammata suna jahiltar dalilin da ya sa Allah SW yahalarci mace, a haƙiƙa Allah ya halicce ta ne don ta yi soyayya ta wajen ba wa maigidanta damar samun natsuwa a wurinta, ga ma aya nan Allah SW yana gaya mana dalilin halittar mace:- (Daga cikin ayoyinSa ne Ya halitta muku mata daga jikinku domin ku sami natsuwa a wurinsu, Ya sanya ƙauna da tausayi a tsakaninku, haƙiƙa akwai ayoyi a kan wannan ga mutanen da suke da tunani). Mace dai mutum ce mai daraja kamar kowani namiji, an halicce ta ne daga namiji, tana dauke da daidaituwar karamci da tausayi da tausasawa, ba wani abu da Allah SW ya yi ma ta sai ka gan sa kyakkyawa; Murya, fuska, tafiya, ado da kwalliya, matsayinta a wurin wadan da suka san darajarta babba ne, don ita ce asalin duk wani alkhairi, wasu can da suka rayu nesa da muslunci sun riƙa yin jayayya a tsakaninsu ko mace mutum ce kamar kowa, don wasu suna ganin dabba ce maras matsayi a tsakaninsu.

Mu kam a Muslunce MACE MUTUM CE, Allah SW ya halicce ta ne da sura ta dan adamtaka, ta wajen tsari da siffa, har ma kuma tsarin halittarsa ya fi ma na namijin, ta yadda zai buƙace ta don ya gama kammaluwa a matsayinsa na mutum, ta ba shi natsuwa da farin ciki, ta zama masa rumbun taskace asiransa, kuma ministar harkokin cikin gidansa, mai ba da shawara game da alaƙoƙinsa na waje, masamman abubuwan da suka shafi 'yan uwansa da zumuntarsa, irin waɗannan abubuwa ba su da alaƙa da sha'awar saduwa kamar yadda dabbobi suke yi, abubuwa ne da suke daure zuciyoyin aminai su sanya su begen juna in an rabu, ko ƙaunar juna in ana tare.

Mun sha gani ba sau daya ba ba sau biyu ba, inda wani baƙi dan Arewa yake jewa kudu ya auro farar mace, wace ta saba masa a al'ada, addini, abinci da tufafin sanyawa, amma da zarar ta zo gidansa sai ta mai da uwayensa na ta, ta fara koyon harshensa, ta yi kyakkyawan shirin hayayyafa masa yadda za ta daure kanta da shi, har dai ta kai inda ba ta da sauran natsuwa in ya fita har sai ya dawo, ƙoƙarinta dai ta gan sa a gabanta, yana dawowa ta tarbo shi cikin farin ciki da jin dadi kamar wace ta yi shekaru ba ta gan sa ba, wannan ita ce soyayya ba sha'awa ba. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Post a Comment

0 Comments