Ticker

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 17)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  17)

Baban Manar Alƙasim

Aure yana da fa'idodi da daman gaske, mu dai za mu dan gutsura kadan ne kawai mu fadi, sauran sai a saurari karatun malamai:- 1) Babban maƙasudin yin aure dai shi ne zama a doran ƙasar da Allah SW ya turo mu, hikimar da ke cikin haka ita ce mu yawaita ta hanyar da Allah SW ya tsara mana, yin hakan kuwa yana daya daga cikin ababan da ake bauta masa da su, to amma babbar hanyar da za ta tunkudo mutum har ya kai ga saduwar da za a yawaita din ita ce sha'awa, sai dai musulmi a kowani lokaci yana buƙatar mace ta ƙwarai wace za ta kula da shi da kuma 'ya'yansa. 'Yar mutu'a ko na ce mazinaciyar da take holewa da kowa ba ta a cikin mata na gari wadan da suka kame kansu domin mutum guda, domin tun asali babu buƙatar tara zuriya a alaƙarta da namiji, babu wata soyayya sai dai biyan buƙatar sha'awar saduwa, shi kansa namijin bai da wata buƙata ta ya mai da ita uwar 'ya'yansa da za ta riƙa jingina kanta gare shi, mai yin aure don Allah da son kasantuwa da masoyi shi ne Allah SW Yake magana a kansa. In mun duba wata aya a Ƙur'ani Furƙan 74 zamu taras ma'anarta tana nufin:- Wadan da suke cewa "Ubangijimmu ka sanya ƙaunar junammu a tsakanin matammu da zuriyarmu, ka sanya mu shugabanni ga masu tsoron Allah".

A wani hadisi ma Annabi SAW haka ya ce:- Ku yi aure ku hayayyafa, haƙiƙa zan yi alfahari da ku a kan sauran al'umma ranar ƙiyama._ Kenan akwai buƙatar ƙaruwa da kuma hayayyafar amma ta hanyar da Allah SW ya tsara wa bayinsa. 2) Sai kuma kare kai daga shedan da kuma hanyoyin da yake bi wajen yaudarar bayin Allah, tabbas yakan yi amfani da sha'awa, mutum in dai lafiyarsa lau, namiji yake ko mace Allah ya riga ya sanya masa sha'awar kinin halittarsa ba yadda zai yi, dole sai ya buƙace shi, amma idan ya kasance nasa ne zai iya amfani da shi a kowani lokaci shi kenan matsala ta ƙare, aure shi ke halasta wa namiji mace a gaban kowaye, ya halasta wa mace namiji, in ba haka ba sai a fada tarkon shedan, Annabi SAW ya ce wa mata "Ban taba ganin wadan da suka gaza a hankali da addini sannan suke da ƙarfin rinjayar gwarzon namiji kamarku ba". Tabbas namiji a hannun mace yake sai dai in ba ta yi niyyar kama shi ba, ko kuma shi din bai da lafiyar da za ta sanya shi ya yi sha'awar buƙatarta, amma aure garkuwa ne da zai iya hana Shedan ya auka wa mutum ta wurin yin amfani da mace, Annabi SAW yana cewa: Ban bar wata fitina a bayana wace ta fi cutar da maza kamar mata ba. Mace ce za ta gama zagin namiji wai ya sanya ma ta ido, alhali da za ka dube ta sai ka ga ta gama cika rukunan sha'awa wadan da dole namiji ya kalle ta din, ba macen da ba ta san sirrin daga sha'awar namiji ba sai dai ko budurwa, budurwar ma ba duka ba. Da wannan Annabi SAW ya ba da maganin kawar da wannan mugunyar sha'awar ya ce a hadisin Muslim:- Idan dayanku ya ga wata mace ta ba shi sha'awa har ta kutsa zuciyarsa to ya koma wurin maidakinsa, don tana da abin da wancan take da shi.

Ke nan aure ya zama magani kenan, wanda bai da shi kuma zai fara neman wata hanyar don kawar da sha'awarsa Allah ya kyauta, Shedan kam yana aiki da sha'awa a tsakanin matasa wajen cimma manufarsa, amma aure yakan taka masa burki sau da yawa. 3) Ba ko shakka zaman hira, da 'yan wasanni, ko kallo, sukan dan hutar da zuciya, su ƙarfafa mutum a kan ibada, koda yake akwai buƙatar sanin wace iriyar hira, wasa ko kallo din, dukansu akwai na halas da ake samun lada da na haram da ake samun zunubi, ba kuwa a aikata sabo don a sami lada, a cikin masu kwadaitar da auren budurwa na ji wani malami yana cewa:-

Auren budurwa (Wato ko yarinyar da ba ta gama sanin namiji ba, irin sakin wawannan ko wace mutuwa ta yi ma ta ba kan zata) ya fi lada, domin takan yi wasa da mijin, ga wata iriyar kissa ta ƙaramar yarinya me saye zuciyar namiji ta sa aikata sunna cikin gaggawa, ga 'yan dararraku da manne wa namiji, sannan koyar da ita da yake yi kullum, da ƙoƙarin tarbiyantar da ita, ga haƙuri da wautarta duk lada za ka samu. Yasir Ramalan Gwale (Allah ya ja kwana da aiki na gari) ya taba ba mu labarin wani dattijo da ya auri ƙaramar yarinya, (me yuwuwa yana ta saƙar yadda zai fito ma ta ne, kasancewarta ƙarama, kar ta yi masa kallon tsohon banza, a maimakon wanda yake ƙoƙarin aikata sunnar Annabi don neman lada), dattijo yana kishingide kamar yana barci, ai sai amarya ta gaza haƙuri ta bi kadin haƙƙinta, ji kawai ya yi ana ja masa tazuge, gari na wayewa ya nemi diyoyinsa mata duk su fidda miji, don wace yake ganin ba ta san komai ba ashe malama ce.  A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  17)

Post a Comment

0 Comments