Ticker

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 24)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 24)

Baban Manar Alƙasim

Sanin wasu 'yan bambance-bambance yakan taimaka wajen yi wa abokin rayuwa hanzari, mace da namiji har abada ba daya suke ba, sunansu dai mutane a jumlance, amma in ka kira namiji da "mace" ransa zai baci, haka da za ka ce wa mace da "namiji" za ta ji zafi, kenan ko a suna mun tabbatar ba daya muke ba, bare mu fara duba sassan halitta da rayuwa, duk in muka ce namiji ya fi mace, zai yi wahala ka ce muna nufin ya fi ta matsayi ne a wurin Allah, don tun halittar namijin farko ba a bar shi shi kadai tare da ita ba, shari'a ta tabbatar a wurare da dama kan cewa dalilin halittarta bayan bautar Allah sai natsar da mijinta, da tattara masa jin dadinsa, gami da hada shi a matsayin cikakken namiji.

Ita kuwa matar duk wata hidima tata ƙarama ce ko babba tana wuyarsa ne, kenan ba ita ce kadai baiwarsa ba, dukansu bayin juna ne, ko mu ce shi ne ma bawan, don ba abincinta da abin shanta da suturarta gami da matsuguni kadai take buƙata a wurinsa ba, hatta ba da kariya na ita kanta da mutuncinta duk yana kansa, wajibinsa ne ya kula da lahiyarta kamar yadda yake kula da tasa, kenan sai ma mun tambayi kayukammu, shin ma waye bawan ita ce ko shi? Namiji kam Allah ya yi shi da girman jiki da ƙarfin zuciya, wannan ya sa za a same shi wani lokaci da zafi gami da ƙarancin tausayi, ita kuwa mace halittarta ta bambanta da ta namiji a jiki da sura, komai na ta mai laushi ne yadda zai iya karbar wancan halittar ta namiji, wasu abubuwan ba sakaci ba ne ko rashin kulawa, Allah bai yi su ne ba da surar da ya yi mu, ya bar su haka ne yadda za mu iya amfana da su, da a ce komai na su irin namu ne, to rayuwar za ta kasance tamkar namiji ne ya auri namiji, ba na gardamar cewa akwai mata tamkar maza, akwai kuma wasu mazan wadan da gwara matan da su, waɗannan ba za mu yi ƙiyasi da su ba.

Yanayin rayuwa kamar yadda muke kallo, jiki gaba dayansa ta ɓangaren zartar da abubuwa shi yake daidaita kai-komo na dan adam, abin nufi a dabi'ance mai rauni yakan jingina ne a jikin mai ƙarfi don ya sami kariya, ya kuma sami rufin asiri, wannan ba a tsakanin mu mutane ba hatta dabbobi da tsintsaye in muka lura abubuwan da namiji yake yi don macen da take tare da shi, akwai jin cewa shi ne mai ƙarfi, kuma shi ne mai ba da tsaro da kariya kuma shi ne mai kula da yara da kuma abinci, ita kuma macen da irin gudummuwar da take badawa don ganin wannan gamayyar ta ba da ma'anar da ake buƙata wajen gina kyakkyawar zamantakewa. Irin waɗannan bambance-bambancen ne suke sanya namiji ya yi ƙoƙarin warware matsalolinsa ko da da masifa ne, abin haushi kuma ba kowani lokaci za ka iske yana da gaskiya ba, ita kuwa mace takan warware matsalolinta ne cikin hikima da natsuwa gami da 'yan dabarbaru, wasu lokutan ma takan hada da 'yan koke-koke don cin ma burinta, kuma tabbas buƙatarta takan biya a wasu lokuta, to amma duk da cewa namiji ƙaƙƙarfa ne kuma jarimi mai ƙarfin zuciya, sai dai mace ta fi shi juriya wajen shanye abin da yake damunta, takan iya jure bacin rai da wahala duk a lokaci guda. In ma ana tunanin cewa ita tana buƙatar soyayya ne, da tausasawa, takan gamu da bacin rai ba ƙarami ba a wurin namiji, har ta tabbatar da cewa ba ya ƙaunarta, amma ta jure wahalhalun nemo wa kanta komai, ta sha wahalar ciki da haihuwa da ƙarancin barci sabo da kukan jira-jirai, amma kullum ka gan ta a tsaye kamar ba ita ba, namijin da mace take gallaza masa cikin sauƙi ake gane shi, ko rana daya ta tabo shi ana iya gane shi a waje, mace kuwa takan yi kukan zuci bakinta yana dariya, don haka koda a ce namiji ya fi mace a aikin jiki, ba shakka ita kuma ta fi shi a juriya.

Ya kamata kowani namiji kafin ya fara neman mace ya san cewa takan canja nan da nan a kan ƙaramin abu, wani lokacin ma ba dalili, sau da yawa namiji yakan hasala, masamman in ya tuna cewa bai yi mata komai ba, to wannan ya fi faruwa ne a dalilin wasu ƙwayoyin halitta da macen take da su, in mace tana al'ada dan abu ƙarami yana iya harzuƙata, haka lokacin da take da juna biyu, ko idan girma ya fara kama ta wato shekara 40 - 45, wasu a lokacin ƙwayoyinsu suke dakatawa, sai ka ga jinin haila ya fara gardama, a irin wannan yanayi ba dole ba ne saurayi ya gane, amma maigida yakan sani, don haka ya san irin ma'amallan da zai yi da ita.

Namiji yakan yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya gina rayuwarsa, don haka duk karatun da yake yi, da wasu ayyuka na ƙarfi, ko na hatsari, yakan yi ne don gina kansa da iyalansa, shi ya sa ba ya iya rayuwa batare aikin ba komai kudinsa kuwa, to ita mace ba dole ba ne ta kalli ƙimar wannan aikin, in tana da wani sha'ani kawai za ta nemi sa hannunsa ne, ko dai ya tafi yara ko ya kai ta, sau da yawa takan nuna damuwarta a kan tafiye-tafiyensa, ko yawan wayoyin da yake yi, masamman in suna da alaƙa da mata, ba ruwanta da cewa aikinsa yana da alaƙa da haka, wani lokacin yakan dawo a gajiye yana buƙatar hutu, sai ta auka masa da surutu, tana neman dalilin makararsa, to in dai kana son ka nemi aure yana da kyau ka san bambancinka namiji da diya mace. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Post a Comment

0 Comments