Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 32)
Baban Manar Alƙasim
To bayan mun waiwayi abubuwan
da suka wajaba a kan maigida, muka sake duba wadan da suka wajaba ga uwargida,
zai yi matuƙar amfani kuma mu duba wadan da suka wajaba a kansu su biyu:- 1)
Ta kowani hali yakan wajaba ma'aurata su duba kawunansu, kuma su amince wa
kawunansu 'yan matsalolin da kowanne a cikinsu zai iya aukawa, namiji ya san
shi babba ne, Hausawa sukan ce "Babba juji ne" juriya dama ta wajaba
ne a kansa, ita kuma ta yarda cewa ita mataimakiya ce, amma maigidanta shi ne
shugaba, da wannan za a iya maganin abubuwa da yawa. Domin warware wannan
tankiyar bari na gaya maka wani abu:-
a) Nakan ga hotuna suna yawo
wai namiji yana ba wa mace furanni, ko kuma ya fasa ƙirjinsa ya ciro zuciyarsa ya miƙa ma ta, wannan kuskure ne,
mace ita ce take nuna wa namiji ƙauna ta ƙarshe, take sauke masa abubuwan
da suke damunsa, ta hanyar mantar da shi su da soyayyar da take nuna masa,
hoton da ya ba ni sha'awa shi ne wanda namiji ya zama wa mace gado ta kwanta a kansa
tana barci, ko wanda ya zama ma ta gada ta taka ta wuce, don ba za ta iya
tsallake rami ba.
b) Ita mace babban abin da za
ta yi shi ne duk zafin da namiji ya shigo da shi ta sauke masa, in ransa ne a
bace ta faranta masa, in ya dawo a matsayin mabuƙaci ta gamsar da shi, ya zama
dai ba wani abin da za ta bari ya ƙuntatu da shi, bare har ya nemi
taimakon wani ba ita ba, ita ce matattarar rayuwarsa, kuma manajan gidansa, in ƙauna ta ginu a tsakaninta da
maigidanta da wahala ta riƙa kallon abin da ta yi wa
maigidan a matsayin ta taimake shi, ko tana buƙatar ya gode ma ta, babban abin
da za ta buƙata kawai shi ne ta nemi sani ko ransa ya yi masa dadi. d) Ya zama
cewa in namiji ya yi wa mace kyauta kar ya riƙa ganin kamar ya ba ta duniya
ne da abin da yake cikinta, ya sanya a zuciyarsa cewa ya yi wani abu ne da ya
zama wajibi a kansa, kuma in har bai yi ma ta ba to shi ne ya gajiya, kenan in
ta gode masa ta kyauta, in kuma ta manta to da ma bai zama dole a kanta ba,
wannan ba zai rage komai ga abin da yake da niyyar yi nan gaba ba, kenan
ma'aurata matuƙar abubuwan da za su aikata don jin dadin juna ne, to kar su jira
dayansu ya gode musu, don in ka yi wa kanka abu wa za ka jira ya ce ma ka ya
gode? e) Tsakanin namiji da mace ba wanda za ka samu cikakke, don haka in
namiji ya gano cewa matarsa tana da rauni ta wuri kaza, kamata ya yi ya ƙarfafa ta, ba wai ya ruguza ta
gaba daya ba, don ya nuna wa duniya cewa yana ƙaunarta, kamata ya yi ya nuna
cewa shi ne fa maigidanta, don haka ne ma suka je sheda cewa lallai sai ta zama
matarsa, sai ta yi masa hidima, kuma sai ta zama uwar 'ya'yansa, in da kuma ya
gan ta da ƙarfi sai ya ririta shi yadda za a dade ana amfana da shi, haka ita
ma macen in da ta ga baraka a gidan mijinta sai ta yi ƙoƙari ta rufe, don sirrin maigidanta
na ta ne, in asirinsa ya rufu na su ne gaba daya ya rufu in da ya tonu to daga
ita har 'ya'yanta ba mai ganinsu da daraja, wannan shi ne sirrin dinke gida,
duk lokacin da mace take ganin ita ce maigidan, shi ma goje yake jin kamar shi
ne kowa na gidan to matsala ta ƙare.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.