Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 33)
Baban Manar Alƙasim
Yau za mu fara duba wasu
harsasai ne wadan da suke taimakawa wajen gina zamantakewar aure mai ƙarfin gaske, don in ka lura da
rayuwar aure, za ka iske wani tsari ne mai zaman kansa wanda ya fara ginuwa
bisa fahimta, gamsuwa, da karbar juna a matsayin ɓangaren jiki, ko na ce sashe na
rayuwa mai zaman kansa, wannan tsari da ya dankwaru a kan ginshiƙai guda biyu dole a sami
daidaituwar ginshiƙan ta kowani ɓangare, in ba haka ba to za a sami
karkarta, kenan akwai yuwuwar zamantakewar ta jirkice ko ma ta silmiyo ƙasa, maganar da muka so farawa
kenan a baya. 1) Abu ne da yake a bayyane cewa mutane ba daidai suke ba, wato
wani ya fi wani ta kowani ɓangare, wannan ya sa in aka ba ka
shawarar ka nemi wata ko a mafarki ba za ka soma ba, haka wani uban yakan yi ƙememe ya ƙi tura diyassa wani gida, ba
wai don bai amince da dabi'un manemin ba, tunanin yadda diyar tasa ce za ta yi
da rayuwarta a tsakiyar duniyar da ba tata ba, to sai dai ba yadda za a yi ka
sami mutum biyu komai kamancinsu, sai ka sami inda suka bambanta, a tsarin
halitta, ko launi, ko hali, ko ma zuciyar neman na kai da mantawa da abin
hannun wani, babu mai musun wannan sai dai: Shin zai yuwu yarinya ta fito a
gidan wadata sannan ta ƙare a gidan talauci don taƙamar ta hau motar soyayya? To
ko ya ake ciki dai ma'aurata wani hadi ne na Ubangiji SW, wanda su biyun a
kullum dayansu yake aiki don sauke nauyin dan uwansa kamar yadda Allah SW ya
tsara, ban da ci da ciyarwa, tufafi da matsuguni, kula da lafiya da kyautata
zumunta, akwai koyarwa da kula da ibadar juna gami da dagewa wajen yaye wa juna
damuwa ko wani tsanani da wani ya shiga, aikin bai tsaya kan maganin matsaloli
ba har ma da rigakafin faruwarsu, kenan kai da za ka yi aure shin wannan
yarinyar ta dace da kai wajen yi maka waɗannan hidimomin? Ko ke kina
ganin wannan manemin zai iya daukar nauyinki?
2) Ni ba na ƙin talaka ya auri diyar mai
kudi matuƙar akwai soyayya, abin kawai da nake cewa a yi ƙoƙari a tabbatar da cewa
soyayyarce zallanta ba sha'awa ba, in talaka ya yi aure matarsa takan tashi da
sassafe ta hau hidimar abinci don maigida zai tafi wurin aiki, tun daren jiya
ta yi wanke-wankenta, yau sai dai girki da tsaftace gida gaba daya don kar
maigida ya ga wani wurin a surar da ba ta yi masa ba, shin wannan yarinyar da
ya kawo za ta iya haka? Za ta iya yi maka hidima wata ƙila ma ta hada da uwayenka? Za
ta iya daukar gidanka ya fi na mahaifinta don yanzu kai ne maigidanta wanda
rayuwarta take hannunka? Mu je ma cewa za ta iya, yanzu ta zama ma'aikaciya ta
masamman a ƙarƙashin tutar auren soyayya, kana ganin in uwayenta sun ƙyale ta anya ƙawayenta da 'yan uwanta za su
yi bakam su zura muku ido ba za su ce ta lalace ba? Abin da ya sa na ce haka
kwanannan na ga wata yarinya ta auri wani maikudin ƙauye, ta koma can da zama, tun
yanzu har 'yan uwanta sun fara ƙorafin ta fara lalacewa, sannan
ga karatunta zai tsaya cak, ƙawayenta ma cewa suka yi ta
kashe rayuwarta a banza, na tabbata yau da kullum irin waɗannan surutan za su iya yin
tasiri, bari dai ta ƙara jimawa ko kuma ta fara haihuwa.
Wannan fa diyar talaka ce a
birni ta auri mai kudin ƙauye, idan talaka ya auri 'yar
masu hali ya za a kwashe? Bar batun ba ta saba kaza da kaza a gidansu ba, mu
komo batun wace iriyar hidima yake tsammanin samu shi da uwayensa da 'ya'yansa
daga wurinta? A ganina dayan abu biyu zai faru, ko dai ita ta narke ta zama
kamarsa don samun gamsasshiyar zamantakewa (wanda ina da tabbacin cewa ko
uwayenta sun yi shuru sun ƙyale, makusanta ba za su bari
ba), ko kuma uwayenta su finciko shi cikinsu don buda masa yadda zai iya riƙe diyarsu kamar yadda suke so,
in dai dayan biyunnan bai samu ba to akwai matsala, za a kafa ma ta ƙahon zuƙa a duk wuraren sha'ani in da
za ta gamu da 'yan uwa da ƙawaye, inda gazawarta za ta
bayyana a gudummuwa, ko suturar sanyawa, ko rashin abin hawa, ko ma zancen
matsugunin da take, ko rashin aikin yi da dai sauran ababan more rayuwa.
Ba ni ba, ba na tsammanin akwai
marubucin da zai iya ƙarfin halin fitowa kai tsaye ya
ce kar a yi soyayya da 'ya'yan masu kudi, ko kar a aure su, don bai da hujjar
da zai fadi haka, mun sha rubuta cewa soyayya ba ruwanta da wadata ko ƙaranta, ko mu ce ita haduwar
zuciyoyi ce kawai, kuma tana iya shiga tsakanin kowani irin aji, a kowani wuri,
kuma a kowani lokaci, sai dai wannan ba zai hana kuma wani marubucin ya nemi a
tantance cewa dole ta zama soyayya ce ta gaskiya ba sha'awa ba, don a soyayya
kowani ɓangare yakan yi shirin ba wa daya ɓangaren duk abin da yake buƙata, ya kare mutuncinsa da
sunansa, ya taimake shi a addininsa da zumuntarsa, ya kwantar masa da zuciya,
ya yalwata masa natsuwar da zai tabbatar da cewa halinsa a yanzu ya fi na baya.
Wannan ita ce soyayya ta gaskiya ko amfadi a baki ko ba a fadi ba, amma idan ya
kasance son ganin juna ne kawai da jin muryar juna, da fatar Allah ya kawo
ranar da za su tsinci kansu a shimfida guda, da ƙoƙarin gamsar da juna ta haram ko
ta halas (in akwai) kafin daura aure, da bijire wa shawarwarin uwaye da abokai
wajen ƙoƙarin cika burin da aka yi, wannan ba wata tantama sha'awa ce maras
ma linzami, soyayya ba ta makantar da mutum ta yadda zai ka sa ganin abubuwa a
haƙiƙaninsu, ita sanya mutum take yi a kan hanya, ta kuma taimake shi
wajen iida nufinsa.
Wai an taba samun wani attajiri ya miƙe a masallaci yana cewa " Me ya sa jama'a suke gudummu ne ba sa son su auri 'ya'yammu?" Ban tabbatar ba in da gaske ne haka din ya taba faruwa, amma wai amsar da aka ba shi ta ta'allaƙa ne da cewa tarbiyyar da suka ba yaran na su ba wanda zai iya daukarta in ba mutum ne kamarsu ba, ni kuwa sai na so a ce ina wurin, da sai na hada maganganun guda biyu na ce "Tun da dai Allah ya yi muku arziƙi, ku samar wa wanda kuke so ya auri 'yarku aikin da zai iya riƙe ta ku ga aiki da gamawa" a wannan jahar muka ji wai wata ta yi alkawarin ba da jari ga wanda zai aure ta, kuma mun ji wai sai da ma ta zabi wanda take so. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.