Ticker

Kamin Ka Ga Biri, Biri Ya Gan Ka: Yarjejeniya Ta Waya Da ‘Yan Ta’addan Zamfara

This article is published in the Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture – Volume 1, Issue 1.

Muhammad Arabi Umar
Abdullahi Bashir
Department of Languages and Cultures, Federal University Gusau, Nigeria

arabiumar@fugusau.edu.ng

Tsakure

Samar da hanyar kawo zaman lafiya da lumana da kawo hanyoyin magance matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi canyewa a jahar Zamfara, su suka fi ɗaukar hankulan masana da manazarta fannoni daban-daban na ilimi. Wannan maƙala ta dubi yadda sadarwa take gudana da ‘Yan ta’adda a Zamfara ta hanyar musayar waya a matakai daban-daban. Binciken ya gano cewa a kan samu yarjejeniya ta waya don neman masalaha ko sulhu ko kuma don neman kuɗin fansa. Bugu da ƙari an fahimci cewa daba ita ce mafakar ɓarayi kuma a can ne suke yin musayar waya tare da taimakon ‘yan rahoton ɓarayi. An saurari musayar waya tsakanin ‘yan ta’adda da jami’an gwamnati da kuma sarakuna wanda aka naɗa ta waya. An fitar da mafarin ta’addanci da zantukan barazana da ƙabilun yan taadda da kashe-kashe da hijira da ƙorafe-ƙorafen yan taadda. Sakamakon bincikiken ya tabbatar da cewa nazarin musayar waya da ‘yan ta’adda zai taimakawa mahukunta da jami’an tsaro wajen kawo ƙarshen taaddanci a Zamfara. Har wa yau, an ba da shawarar a yi amfani da hanyar binciken laifuka ta kimiyar harshe.

Gabatarwa                                                        

An shafe sama da shekaru takwas ana ta ɗauki ba daɗi da ‘yan ta’addan da suka addabi jahar Zamfara da kewaye. Tashe-tashen hankula da ayyukan ta’addanci sun yi sanadiyar rasa rayuka da yawa, da gurgunta tattalin arziƙi da kuma ɗaiɗaita al’ummar jahar Zamfara. Ga abin da wani shahararren mawaƙi ɗan asalin jahar ke cewa:

Ba tsaro jaharmu gaba ɗaya wanga mulki muke mugun ƙyama,

An kashe uba koko ɗanɗanka don ba tsaro, Allah rama,

Wai har ku ce maimai kuka so, kuna mai da al’umma tsumma,

Ɓarawo ya ga katanga ta faɗi bai jin shakkar hauro.

 (Kabiru Kilasik: Wakar Alhaji Ibrahim Shehu Baƙauye)

A wannan baiti, mawaƙin ya bayyana yadda kashe-kashen alummar jahar Zamfara ya yi ƙamari, saboda sakacin shuwagabanni da haƙƙin kare rayuka da dokiyoyin jama’a ya rataya a kansu.

Zamfarawa ba wani ka ba mu labari ba,

Wanga zaɓe wallahi bai yi albarka ba,

Babu ci ba sha ko tsaro ba a samu ba,

Talakka mai samu hankalinsu bai kwanta ba,

(Kilasik Ƙwayar Rodo)

A wannan baiti ma, mawaƙin ya ƙara fito mana da matsalar rashin tsaro ƙarara, kuma abu ne wanda kowa ya san da shi. Don haka, za mu ji waƙa abakin mai ita, ta hanyar musayar waya da aka yi da yan taadda a lokuta daban-daban, kamar dai yadda muka ji wata shawara da wasu ɓarayi suka ba Nomau a cikin labarin Sarkin noma da ‘ya’yansa na cikin littafin Magana Jari Ce Na BiyuƁarayi suka ce , Ka iya sata? Ba fa sanaar raggo ba ce, ba ko ta yan kirki ba ce, ba ta kuma ta masu tausayi da jinƙai ba ce, ba ko ta masu gudun azaba ba ce. Sanaa ce ta taɓaɓɓu waɗanda shaiɗan ya mallaki zuciyarsu”. Lallai ko wannan mugunyar sana’a ce ta ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane domin su samu kuɗin fansa ta hanyar musayar waya da waɗanda abun ya shafa tare da taimakon gurbatattun mutane masu kai masu rahoto.

Dabarun Bincike

An iyakance wannan bincike a kan musayar waya da ‘yan ta’addan jahar Zamafara kawai. Saboda haka, wannan bincike ya dogara ne kacokan kan abubuwa da aka saurara, da kuma hira da aka yi da waɗanda suka samu kuɓuta daga hannun ‘yan ta’adda; da wasu bayanai da aka samu a kafafen yaɗa labarai na radiyo da talabijin da mujallu da jaridu da aka buga. Har wa yau, an samu yin rangadi a kafafen sada zumunta, inda aka zaƙulo muhimman bayanai tabbatatu waɗanda suka taimaka ma wannan bincike da ƙwararan hujjoji.

An yada zango a ayyukan masana a fannonin tsaro da al’ada da kimiyar sadarwa don ganin yadda suke kallon lamurran tsaro a bincikensu. Bugu da ƙari, an kai ziyara a manyan kafafen yaɗa labarai da ke Gusau, da kasuwar ‘yan waya da ke Bebeji don samu rakodin na musayar waya da ‘yan ta’adda a Zamfara. Har wa yau, an tattauna da wasu da aka taba yin garkuwa da su da iyalansu. Binciken ya samu tattaunawa da wasu ‘yan kabo-kabo da ke ƙauyukan da ke kusa daba. Abubuwa da aka kalato a kafar intanet sun taimaka ƙwarai wajen saman nasarar wannan binciken.

Zamani Riga

Babu yadda za a yi maganar yarjejeniya ta waya ba tare da an dubi sadarwa ta zamani ba. Sadarwa ita ce isar da saƙo tsakanin ɓangarori biyu: Mai bayar da saƙo da mai karɓar saƙo ta hanyar kafar isar da saƙo wacce ka iya zama mutun ko waninsa, sannan kuma cikin sigar da dukkan ɓangarorin biyu za su fahimta. Kowace al’umma tana da hanyar da take bi wajen isar da saƙonta. Daga ciki akwai baka-da-baka, rubutu, gaɓɓoɓi da sauransu. Zamani ya kawo sauye-sauye da dama a cikin rayuwar al’umma baki ɗaya, daga ciki akwai sadarwa ta zamani wadda ta haɗa da yin amfani da musayar waya wajen isar da saƙo.

Me Ake Nufi Da Waya?

Idan aka ce wayar salula (Mobile Phone) ko (Cell Phone) ana nufin “Wayar tafi-da-gidanka ko wayar hannu, mai amfani da siginar rediyo (Radio Signal) don karɓar kira ko amsa kira tsakaninta da waya ‘yar uwarta, a iya kadadar tashar sadarwa (Base Station)”.

 Galibin wayoyin salula na ɗauke da katin SIM (Subscriber Identification Module), wanda ke ƙunshe da lambar wayar wanda ya mallaki wayar, da kuma ma’adanar lambobin mutane (Contacts Memory). Wannan ke nuna mana cewa kafin a kira wayar salula da wannan suna har ta amsa, dole a samu abubuwa guda huɗu tare da ita. Abu na farko shi ne ita kanta wayar, watau wayar hannu, abu na biyu kuma shi ne katin SIM, wanda ke ɗauke da lambar mai wayar. Abu na uku shi ne samuwar tsarin sadarwa ta wayar iska mai ɗauke da siginar rediyo a tsakanin wayar salula da wata wayar. Sai abu na huɗu, watau tashar sadarwa (Base Station) kamar yadda bayani ya gabata a sama. Ita kuma tana samuwa ne daga kamfanin sadarwar da ya bayar da katin SIM ɗin da ke cikin wayar. Sai da waɗannan abubuwa gudu huɗu za a iya amfani da wayar salula don kiran wani ko amsa kiransa. Ke nan babu wata musayar waya da za a gudanar da ‘yan ta’adda a kowane lungu da saƙo na jahar Zamfara ba tare da an yi amfani da katin SIM ba wanda kamfanonin sadarwa kamar MTN, GLO, AIRTEL, ETISALAT ke samarwa. Waya tana taimakawa wajen isar da saƙo da gaggawa, haka kuma tana taimakawa wajen aikata manyan laifuka kamar yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Kamin Ka Ga Biri, Biri Ya Gan Ka

A nazarin falsafar rayuwa, wannan na cikin karin magana da ake amfani da su don yin bayani kan tsaro. Karin magana na taka muhimmiyar rawa wajen fito da falsafa da tunanin al’umma. Malumfashi da Nahuce (2014) sun ce: “Harshe kamar yadda aka sani abu ne na tunani, saboda haka harshen Hausa shi ma ba a bar shi a baya ba wajen tafiya da nasa tunani. A lokutta da dama harshe na fito da halin rayuwar yau da kullum da kuma irin dangantakar da ke tsakanin mutane da dabbobi da tsirai ko ƙwari ko tsuntsaye da ke maƙwataka da su. Ke nan lura da siga, halayya da ɗabi’a ta biri zai taimaka mana mu gano bakin zaren matsalar tsaro a jahar Zamfara bisa ga fikira da basira da tunani da hangen nesa da ke cikin Bahaushen tunani.

 Bunza (2019) ya ce: “Bahaushe ya shaidi biri da wayo da salo. Idan ya yi ɓarna gona, ya tarar da ruwa, sai ya sha, ya wanke ido ya tafi abinsa”. Don haka ashe akwai sifa kala biyu da Bahaushe ke kallon biri da ita. Ta farko ita ce ta ɓarna, kuma abun ƙi ce, ta biyu kuma ita ce wayo da salo, wanda ake buƙatar sa a harkar tsaro. Dole ne jamian tsaro su zama masu wayo da kuma salo don daƙile masu tayar da ƙayar baya. Za mu kalli biri na farko maɓarnaci wato ‘yan ta’adda a tunanin Bahaushe.

Hannun Biri Bai Zama Ba Aiki

 Wannan biri ɗan ta’adda kullum hannunsa ƙaiƙayi yake yi, in bai taɓa dukiya ko kayan mutane ba. Ba shi da wani aiki sai sace-sace da hannunwansa, don haka ne ma, a shari’ance ake yanke hannun ɓarawo idan satar ta kai mizanin da shari’a ta tanadar, saboda da hannun ne ake kitsa duk wani ta’addanci. Ashe don haka ne masu garkuwa da mutane, da ɓarayin shanu, da ‘yan fashi da makami suna ɗauke da manyan bindigogi da makamai a hannayensu domin ba su rabuwa da ta’addanci.

Idan Biri Ya Yi Ɓarna Gudu Yakan Yi Tun Mai Gona Bai Gan Shi Ba

 A 14 ga wata Yuni 2018, ‘yan ta’adda sun kai wasu munanan hare-hare a Illojiya da Madambaji da sabon garin Madambaji da Oho da Dutsen Wake a ƙaramar hukumar Birnin Magaji inda suka kashe mutum 31 a ƙauyukan. Kafin jamian tsaro su isa wurin, ɓarayin sun gudu. Don haka, idan ɗan ta’adda ya aika ta ta’addanci ba ya tsaya wa hukuma ta kama shi.

Don ta Biri a Naɗe Ƙasa

Duk wanda ya yi nazarin irin ta’addancin da aka yi a jahar Zamfara a cikin shekaru takwas, an kashe mutane sama da dubu, an sace shanu na biliyoyin naira, an yi garkuwa da mutane tare karɓar kuɗin fansa da kashe waɗanda ba su samu zarafin biya ba, an kama ‘yan mata da matan aure an yi musu fyaɗe an ƙona dukiyoyi da abun da aka noma aka adana a reheni, an tarwatsa kasuwanni daban-daban a jahar, an hana mutane noma da kiwo, an durƙasar da harƙallolin tattalin arziƙi, duk a sanadiyar ayyukan ta’addanci. Lalle ne kam, don ta biri a naɗe ƙasa.

Banza Barin Biri Jiran Gona

A tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ya rataya ne a kan hukumomi da jami’an tsaro. An samu rahotanni da bayanai da hujjoji da suka nuna cewa akwai sa hannun wasu gurɓatattun uwayen ƙasa, da hakimai, da sarakuna, da alƙalai, da jamian tsaro a hare-haren da ake kai wa a jahar Zamfara saboda kwaɗayi da rashin imani. Dole sai an yi garanbawul da tankaɗe da rairaya a harkar tsaro, idan ana son haƙa ta cimma ruwa, in ba haka ba, za a yi ta kitso ne da ƙwarƙwata. Kuma duk ƙoƙarin da ake yi zai zama na banza wato an ba biri tsaron gona.

Biri bai kula da Allah-tsine, kai dai Mai gona Tsare Gonarka

Zukatan ‘yan ta’adda sun ƙeƙyashe babu sauran imani, don haka, duk tofin Allah-tsine da Allah ya isa da ake yi musu, bai ko dame su ba. Ke nan ya zama wajibi kowa ya ba da tashi gudunmuwa kan yadda za a shawo matsalar tsaro a jahar Zamfara. Mun ga irin rawar da ƙaramar hukumar Gummi ta taka wajen tsare iyakarta daga hare-haren yan taadda, a lokacin da taaddancin ya yi ƙamari sai sarki ya kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki tun daga ciyaman na ƙaramar hukuma da jamian tsaro da uwayen ƙasa, da hakimai, da sarakunan Fulani da ƙungiyoyin alumma kamar Muryar Talakka da manoma da makiyaya, aka kafa wata ƙungiya mai suna Lakuruji ta Fulani zalla wadda aka tantance kuma aka ba su horo ta hanyar zaƙulo yan rahoton ɓarayi daga cikin al’umma. Wannan ƙungiya ta taimaka wajen magance rashin tsaro a Gummi. Abun mamaki, ga shi hare-haren sun sake komawa a yankin na Gummi! Dole a sake lale.

Sauran karuruwan magana da suka shafi ta’addanci da ɓarna irin ta biri, sun haɗa da:

a.       Ɓarnar biri takan sa mai gona hauka

b.       Biri ba kwana lafiya ba, ƙauye ba shi samun lafiya

c.        Biri ya yi kama da mutum, wutsiya ta hana

d.       An sai da kare don tsunguno, an sayo biri Ko biri ya kariye ya hau runhu

e.       Idan aka ɗauki biri na biyu ta la’akari da wayo da salo. Za a ga cewa

f.        Ana Ganin Wuyan Biri Akan Ɗaure shi a Gindi

g.       Ko da biri ya zama wawa, ba shi wasa da ice mai ƙaya.

Wane Ne Ɗan Rahoton Ɓarayi (Informant)?

Ɗan rahoton ɓarayi shi ne wanda ke ba ‘yan ta’adda bayanin sirri game da mutum da kuma hanyar da za a bi, a yi garkuwa da shi. Ɗan rahoton ɓarayi ya fi ‘yan ta’adda illa saboda shi zaune yake cikin al’umma ba tare da wata matsala ba, alhali yana nan yana yi mata zagon ƙasa. Su ne babbar matsalar da suka sa matsalar tsaro ta ƙi ci ta ƙi canyewa a jahar Zamafara. Dole ne sai alumma sun tashi tsaye wajen zaƙulo waɗannan miyagun mutane tare da miƙa su ga hukuma. Wani lokaci ma su ke bayar da lambobin wayar wanda za a kira a karɓi ƙudin fansa. Akan ba su kashi ɗaya bisa uku na kuɗin fansar da aka karɓa. Daga cikin dalilan da ke sa mutane shiga wannan mugunyar sana’a akwai, kwaɗayi da ƙyashi da rashin aiki.

Yarjejeniya Ta Waya Tsakanin Wakilan Emiya Da Buharin Daji

 

Buharin Daji wanda aka fi sani da Buhari Tsoho, ya daɗe yana jan zarensa a cikin ta’addancin jahar Zamfara kafin ajalinsa ya cika. Shi ne shugaban ‘yan ta’adda da suka addabi jahar Zamfara. Gwamnati ta nemi a yi sulhu da shi, domin a kawo ƙarshen tashe-tashen hankula a jahar Zamfara. A wani faifan rakodin waya tsakanin wakilin Emiya da Buharin Daji, ga yadda yarjejeniyar ta kasance:

 

W/Sarki: Elo ya gida? Elo, e ina jinka ya hidimomi?

B/Daji: Ah, Lahiya lau ya jama’arka?

W/Sarki: Lahiya lau, ina tsohon yake?

B/Daji: Shi ne ka magana da kai,

W/Sarki: Ah kai! Buharin duk duniya!

B/Daji: Ah kai! A’a?

W/Sarki: Bari in maka kirari tun da jiya ka hana ni kwana.

B/Daji: Ah sabadda mi?

Wannan matashiyar fara waya ce tsakanin Wakilin Sarki da kuma Buharin Daji, inda yake ƙoƙarin yi ma Buhari kirari domin ya samu su fahimci juna cikin sauƙi.

W/Sarki: ka ce mani yankinmu zai zama gara na Maiduguri da shi, eh yankinmu zai

 zama Maiduguri !

                                                           

B/Daji: To, a nika haka tun da kuna nema ya zama

W/Sarki: Ai ba haka ba ne, ka san mu kullun so muke a zanna lahiya ko Tsoho?

B/Daji: To kuna son a zanna lahiya don Allah don Annabi kai ranka ya daɗe ya za a cewa

 macce ma an kame ta, to wai ko ga yaƙi an ga inda za a taɓa macce?

 

W/Sarki: Babu inda an ka ce a taɓa mata

B/Daji: To.

A nan an fara tattaunawa tsakanin Wakilin Sarki da Tsoho, kuma ya nuna cewa sai Zamfara ta fi Maiduguri zama cikin tashin hankali tun da aka kama mata, ko a lokacin yaƙi ba a taɓa mata da ƙananan yara.

W/Sarki: Amma wannan an yi ne don kai kanka kariyar ka ai shi yas sa munka yi haka,

 ka gane ko? Sannan jiya na yi magana da Emiya ya ce man shi bai ga mis kwal ɗinka         ba.

 

B/Daji: Wai me?

W/Sarki: jiya mun yi magana da Emiya ya ce man shi bai ga kiranka ba

B/Daji: A’a na kira shi

W/Sarkin: Ka kira shi yau?

B/Daji: A’a yau yanzu niz zo ga sabis

W/Sarki: Yanzu kaz zo ga sabis

B/Daji: Eh!

Wakilin Sarki ya tabbatar wa da Tsoho cewa an kama Iyalinsa ne domin a ba su tsaro saboda a lokacin ‘yan-sa-kai da jami’an tsaro suna farautar Buharin Daji ruwa a jallo. Haka kuma ya jaddada masa cewa Emiya bai ga kiransa ba. Wannan shi ya nuna cewa Emiyan sukan yi waya da Buharin Daji! Kuma har wa yau, an gano cewa sukan fito neman sabis a duk lokacin da suke buga waya da hukuma ko wasu daban.

W/Sarki: Yanzu shi gaskiya yana masallaci

B/Daji: Ba matsala ai da kai da shi duk ɗai ne

W/Sarki: Uhm!

B/Daji: To ni ai yanzu ka ga na zama ɗan tsakkiya ko, na zama ɗan saƙo, to ai shi dai

 wannan al’amari kana ji ko? Ni ba na ce ai dole ba ne amma ka san abin da ah haƙƙin

 al’amari ka hwaɗa ma mutum.

 

W/Sarki: Kuma mu kai Tsoho mu ya zama dole ne gare mu, saboda mu kullum dai

kwanciyar hankali muka so a samu.

 

B/Daji: To yanzu don Allah bara da an ka yi shirin nan tsakaninka da Allah da Annabi      ba a samu jin daɗi ba?

 

A nan Wakilin Sarki ya gabatar da uzurin Emiya cewa yana cikin masallaci. Ba zai samu damar tattaunawa ta waya da shi ba. Tsoho ya nuna cewa babu wata matsala domin zai isar da saƙonsa ga Emiya. Gurin kowane Sarki nagari a samu kwanciyar hankali da yalwatar arziƙi a ƙasarsa. Tsoho ya nuna cewa bara da aka yi sulhu tsakanin hukuma da yan taadda an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da walwala da jin daɗi.

W/Sarki: Nic ce maka an hwa ji daɗi amma kai ka zo kay yi wannan hitat wadda an ka

 zargi cewa ba shanunka kat tai biɗa ba.

 

B/Daji: A’a in ji wa? Kowa ya san shanuna nit tai nema.

W/Sarki: E, to shi ya sa nac ce maka ‘yan‘uwanka kai maka kwancin ɓauna.

B/Daji: A’a ba ruwan ‘yan‘uwana waɗannan ma’aikata ne, ni na gan su ai da idanuna.

 Ai na san ‘yan’uwana na san ma’aikata.

 

W/Sarki: Uhm!

 

B/Daji: Kana ji ko?

W/Sarki: Ina jin ka.

B/Daji: Kahin a yi haka nan, kahin ma in tai biɗar shanuna, ka ga yarana sun yi karo da

 mashin kuma sai wagga magana ita na sama wadda kas sani ce ko?

 

W/Sarki: Na sani kai ko, ba dogo ba?

A nan Wakilin Sarki yana ƙoƙarin ya nuna masa cewa ba daga wajensu ne aka samu matsalar warware alƙawarin da aka yi ba, ta iya yiyuwa ko kuma ya zama yanuwansa ne ke yi masa zagon ƙasa. Shi kuma yana zargin jamian tsaro ne suka tare shi. To gaskiya dai ta yi halinta domin kuwa Dogo Giɗe shi ne wanda ya kashe shi daga baya.

B/Daji: To su yaran nan da sun ka yi karo da mashin an kai su an ka kame su, shin akwai dalili?

W/Sarki: A’a

B/Daji: Ai ka ga ba dalili ko?

W/Sarki: E, amma dai, to da yake ni hukumomi ban san su jami’an tsaro, ban san ko mis

 yas sa sun ka yi wannan ba.

 

 B/Daji: kana ji ko?

 

 W/Sarki: Uhm!

 

 B/Daji: Gaban sojoji sun ka yi karo da wannan yaro kuma dare da rana yana inda sojojin

 nan, ka san an yi aje sojoji nan mutum ɗai ko?

 

 W/Sarki: Na sani kai ko.

 

 B/Daji: Duk abun da za ai tare muka yi nai da sojoji nan komi dare da rana da komi

 muna nan.

 

 W/Sarki: Na sani.

 

B/Daji: To sai a ce bayan haka wasu su tai su kai wata ƙarya masu son ɓata ƙasa wasu

 jahillai waɗanda ba su san komi ba, an yi shiri mai kyau ga ƙasa kowa ya tahi koina,

 kowa ya ji daɗi an maida, ka ga kasuwar Didi mu yay yi ta Allah yay yi ta ana jin daɗi.

 

W/Sarki: Uhm!

 

B/Daji: Mun tayar da kwamiti na zakka muna tsakar lissafi, mun lissahwa wajen

 mutanenmu waɗanda za su hitar da zakka 270 mun ka lissahwa.

 

W/Sarki: Uhm!

 

B/Daji: Haryanzu rubutun yana nan.

 

 W/Sarki: Wayyo!

 

 B/Daji: Saboda ba shi ne shika-shikan musulunci ba a ji daɗi kowa ya zanna lahiya ya

 huskanci musulunci ga ƙasa, Allah ya ƙara hikkam muna da zaman lahiya.

 

 W/Sarki: Ƙwarai ko.

 

Tsoho dai yana nuna ɓacin ransa kan kame masa yara da jami’an tsaro suka yi bayan an riga an yi sulhu. Kuma ya ƙara nuna cewa sun riga sun rungumi shariar musulunci don har sun fitar da zakka wadda aka lissafa mutum ɗari biyu da saba’in da za su fitar da zakka.

B/Daji: To amma sai a ce yara ba su yi komi ba haka kawai a tai a biye wa wasu jahillai waɗanda ba su son a zanna lahiya a kame muna mutane, shi kuma mataimakin gwamna da kai nai da girma nai a gama da su a kame mini yara kuma in roƙe su arziƙi in tambaye su mi ad dalili su ce ba dalili wai haka kawai dai an kame su, ka ga su nat tadda alƙawari, to shi ne nic ce maku yanzu an bi ni an ka yi wata an biya ta, wata na 5 an nan.

 

W/Sarki: Im

 

B/Daji: Ana kawo mani hari to ni har yau ban kai ba, to hwaɗa maku niy yi in za a sako mani mutanena a sako mani mutanena mu koma zamnawa, mu zanna mu koma abu guda kamar wada mun ka ɗauko bara, kowa ya tsare gaskiya tai ga al’amarin nan, in ko ba haka nan ba, to wallahi kowa ya shirya yanzu harin ga da an ka yi wata biyar ana kai man, ni ɗa ne ba shege ba ne sai na yi wata goma in dai, kai ko na mutu yarana sai sun yi wata goma suna yi duk wata sai sun mai ɗan ‘uwa.

 

W/Sarki: Mu dai ba mu...

 

B/Daji: Da yardar Allah sai na mai da harin nan, sai na mai da harin nan da an ka kai man, daɗa inda zan mai da shi da inda zan mai da shi ab ba zan hwaɗa ba sai dai in na yi a ji.

 

W/Sarki: To amma ko ni ai kana hwaɗa man ko Tsoho?

 

B/Daji: To ban hwaɗa ma in dai na yi za ka ji.

 

W/Sarki: I, im Tsoho haka nan ba ta dace ba

 

B/Daji: Haba ai ba zan hwaɗa ba kai, kana ji ko? Amman in Allah ya yarda, in gobe an ka sako mani mutanena.

 

W/Sarki: Uhm!

 

B/Daji: Su waɗannan mutane shanuna na nan tsare sun ba Gwamnati rabin duk da sun koran ma dangina da yarana shanu duka sun kore masu shanu, to su ba ni shanuna waɗanda ba su canye ba, su sako mani yarana da mutanena, to batun zaman lahiya na yarda, ta’addanci ƙasarmu ta Zanhwara ba za a ƙara ji nai ba. Amma duk hwaɗa nan da kun ka ji ana yi ɗauki wancan, ɗauki wancan.

 

W/Sarki: E

 

B/Daji: Cikin dubu ɗaya ne an ka yi

 

W/Sarki: Eye!

 

Tsoho ya bayyana cewa an yi wata biyar ana kai masa hari bai rama ba. Amma idan ba a sako masa yaransa ba, to sai ya yi wata goma yana kai hare-hare. Matuƙar aka saki yaransa to za a daina duk wani taaddanci da sace-sacen mutane a Zamfara. Kuma ko bayan ransa yaransa sai sun ɗauki fansa.

 

B/Daji Cikin dubu wallahi ɗaya ce an ka yi, ba a ma yi komi ba kai.

               

W/Sarki: Yanzu kasan halin da ake ciki Tsoho na sace-sacen mutane?

 

B/Daji: Duk abin da an ka yi ƙasan nan na san da shi, duk abin da an ka yi na sani

 

W/Sarki: Iyin Tsoho

 

B/Daji: hwarawa ce an ka yi wallahi, ka ji an kai hari ba hure ba kunne?

 

W/Sarki: A’a

 

B/Daji: To shi za a yi yanzu.

 

W/Sarki: A’a Tsoho!

 

B/Daji: To ai tsaya ka jiya da in ɓoye maka kissa, to ni da an ka yi wata biyar an

 nemana a kashe ni, Allah bai yarda ba.

 

 W/Sarki: Uhm!

 

 B/Daji: Iyim

 

 W/Sarki: To yanzu ni dai Tsoho ka jira ni don isar da saƙo, kuma biizinillahi na ma isar

 da saƙo nan kuma ana nan ana diba yadda za a yi, yadda za a hito ma abun.

 

 B/Daji: In an duba ni lahiya lau, ni ɗan Zanhwara ne, kakannina Zanhwara ma aka haife

 su, nima aka haife ni Zanhwara.

 

Tsoho ya nuna cewa matuƙar ba a sako masu yaransa ba babu sauran zaman lafiya jahar Zamfara. Ya nuna cewa shi ma ɗan jahar Zamfara ne kuma mai kishin jahar. Sannan ya umurci Wakilin Sarki da isar da saƙonsa ga mai martaba Emiya. A sauran tattaunawar ya nuna cewa an kame masa yara da aka kai makaranta Zariya, da kuma waɗanda suka dawo daga Makka da matarsa. Idan aka sake su, to za a samu zaman lafiya.

               

W/Sarki: To babu matsala Allah Ubangiji ya kawo muna Karshen wanga abu.

 

B/Daji: To amin, in dai kun diba, a samu sauƙi, in kau ba ku diba ba, wallahi kau duk

abin da an kai ma ƙasarku, wallahi ku naj ja da kanku.

 

Da wannan kalami Tsoho ya rufe yarjejeniyar ta waya da Wakilin Sarki[1]. Wannan tattaunawa dai an naɗi bayanan da suka yi tsakaninsu.

Ƙumshiyar Zantuka.

Hukumar kula da tsaron jihar Zamfara ta shiga farautar Buharin Daji, da ba ta samu damar kama shi ba ta samu damar zuwa har Zariya inda yaran Buharin Daji ke karatu ta kamo su. Ta kuma haɗa da wasu daga cikin iyalinsa da suka je aikin hajji bayan sun dawo sai ta kama su a filin jirgin Abubakar Na Uku da ke Sakkwato. Wannan kamun da aka yi masu, hukumar tana ganin kamar ta nan ne kawai za ta iya samun sa’ar ya miƙa kansa domin ƙaddamar da bincike a kan tuhumar da ake masa domin kare kansa. Idan kuma abin da ake zargi kansa ya tabbata to sai a ƙaddamar masa da hukunci.

Buhari ya kira wakilin Emiyan Maru sun tattauna dangane da wannan matsala wato kama masa iyalai don ya bayyana gaban hukuma ya wanke kansa. Kamar yadda tattaunawar ta gabata a sama mun ji duk buƙatun da ya zo da su da kuma kashedin da ya yi ko barazanar da ya yi domin ɗaukar fansa idan ba a sako masa iyalansa ba.

Dukkan zantukan da suka gabata a cikin wannan yarjejeniya ta wayar tarho tsakanin shugaban ‘yan fashin daji wato Buharin Daji wanda aka fi sani da Buhari Tsoho tare da wakilin mai martaba Emiyan Maru babban abin da suka ƙunsa shi ne sulhu da neman a saki iyalin shi. Buharin Daji ya kuma kai ƙorafinsa ga hukuma da take da alhaki domin a sake masa iyalinsa.

Haka kuma ya ba da tabbacin idan aka sake masa iyali za a zauna lafiya a yankin. Idan kuma ba a yi ba, aka ci gaba da tsare su ko ɗaukar wani hukunci a kansu; to ya yi barazanar zai hargitsa zaman lafiya a jihar Zamfara baki ɗaya. Kalamansa sun bayyana cewa da gaske yake kuma zai iya aikata duk wani aiki na ta’addanci domin ɗaukar fansa a kan iyalansa.

Mafarin Ta’addanci

Ta’addanci kalma ce da ta yi matuƙar fice a duniya tsakanin ƙasa da ƙasa da shugabanninsu a hulɗoɗi na tsakanin jama’a ko kuma tsakanin mutum da mutum[2].  Kalmar ta’addanci ta ƙara fice ne a tsakanin ƙarni na 19 zuwa wannan lokaci da kafafen watsa labaru na duniya suka yawaita amfani da fassararta ta Ingilishi terrorism.

Ko da yake kalma ce da aka daɗe ana amfani da ita a zantuttukan mutane na yau da kullum. Duk da yake wannan kalmar ta zama sananniya a duniya sai dai akwai taƙaddama a tsakanin jama’a dangane da ma’anarta kai tsaye. Iyiola (2004: 8) ya bayyana cewa Kegley (1990: 3) ya yi ƙididdigar ma’anonin kalmar ta’addanci a sassan duniya har 108 daga 1936 zuwa 1981 kawai.

Atuwo, (2009: 1) ya ci gaba da cewa, “Saboda daidai wannan lokacin ne matsalolin gwagwarmaya da tashin-tashina suka yawaita. Misali mutane kamar su Abu Nidal da Carlos (The Jackal) har ma da shugabannin wasu ƙasashe kamar Mu’ammar Ghaddafi (shugaban ƙasar Libiya) da Fidel Castro (tsohon shugaban ƙasar Cuba 1959-2002) duka an yi lokacin da shugabani Amirka ke kiran su ƴan ta’adda. Dalili kuwa saboda sun nuna ba su ra’ayin manufofin Amirka da ƙawayenta. Har daga bisani ƙungiyoyin masu adawa da irin waɗannan mamufofi na Amirka da hukumomin ƙasashensu kan kira su da wannan sunan na ‘yan ta’adda. Gwandu, (2003: 2)[3] ya bayyana wasu ƙungiyoyin da hukumomin ƙasashensu ke kiran su ‘yan ta’adda tun daga 1960, misali Red Brigades (Jajayen Dakaru) a ƙasar Italiya da ƙungiyoyin gwagwarmayar yaƙi da manufofin Isra’ila a Falasɗinu da kuma dakarun Irish Repulican Army, IRA (wato Rundunar Jumhuriyar Ayilan ) ƙarƙashin jagorancin madugunsu Gerry Adams.

Ƙabilun ‘Yan ta’adda

Binciken da wannan maƙala ta gudanar dai ya nuna ba ƙabila ɗaya ce ke aiwatar da wannan ta’addanci ba. Amma dai a jihar Zamfara za a iya cewa ƙabilun da suka bayyana su ne Fulani da kuma Hausawan kansu. Wani hanzari ba gudu ba, maƙalar ta gano cewa akwai wasu masu ɗaukar nauyin ta’addanci da ake yi a jihar Zamfara wanda kuma ba ya rasa nasaba da irin arzikin da jihar take da shi. Don haka dai za a iya cewa ko bayan ƙabilun Fulani da Hausawa akwai wasu ƙabilu da ba na ƙasar Nijeriya ba fararen fata kamar Turawan Yamma irin su Faransa da kuma Amirka kanta. Haka ma idan aka koma Gabascin duniya za a iya cewa akwai ‘yan China waɗanda suma suna tarfa nasu ruwan wajen kakace dukiyar wannan jiha. Akwai wasu manya daga ƙasar ta Nijeriya da su kansu ba su wasu ke zargin suna da hannu a cikin wannan[4].

Zantukan Barazana

Zance dai suna ne na magana wanda ita magana tana da sunaye daban-daban. Daga cikin sunayen akwai zance, hira, ɗumi, da sauransu. A jam’ince za a iya cewa zantuka.[5]. Ita kuwa barazana yunƙuri ne na tsoratar da mutum da wasu kalamai ko wani aiki da zai sa mutum ya ji shakka ko tsoron sakamakon abin da zai biyo baya[6]. Idan aka haɗa waɗannan kalmomi biyu wato zantuka da barazana da aka kira su da zantukan barazana, wannan na nuni ne ga irin magangannun da aka faɗa don tsoratar da wani ko wasu.

‘Yan ta’adda na amfani da wannan barazana wajen cimma manufarsu ko dai ta samun kuɗin fansa ko ta samun wata buƙata kamar yadda Buharin Daji ya yi wa wakilin Emiyan Maru barazanar cewa sai Borno ta fi Zamfara zaman lafiya. Sanin al’umma ne cewa ƙasar Borno ce aka fara rikicin boko haram wanda ya yi sanadiyar ɗaiɗaicewa da tarwatsewar mafi yawan al’ummu[7]. Ganin irin halin da waɗannan al’umma na ƙasar Borno suka shiga na tashin hankali ya sa Buharin daji ya kwatanta wannan ƙasar (Borno) da Zamfara. Ya ma ce sai na Borno sun fi na Zamfara samun kwanciyar hankali a kan irin harin da shi zai kai a wurare daban-daban a faɗin jihar.

Ba Buharin Daji kaɗai ke amfani da barazana ba wajen neman wata buƙata kusan dukkan masu garkuwa da mutane domin kuɗin fansa suna yin maganganu na barazana ga iyali ko dangi ko hukuma da ya ko ta ko suka shiga yarjejeniya don sako wanda ko waɗanda aka kama. Haka ma idan da akwai buƙata ta su yan taadda a hukuma sukan yi barazana ga duk wanda suke waya da shi. An samu fayafan murya na wayoyin da aka yi tsakanin ‘yan ta’adda da masu shiga tsakani don sasantawa da ciniki don biyan fansa a karɓo mutum ko mutane da a ciki ‘yan ta’addan suke aikawa da barazanar kisa ko kai hari ko wani abu makamanci haka don yin barazana ga waɗanda ake ciniki da su.

Akwai ƙauyuka da dama a jihar Zamfara da suke aikawa da saƙo cewa su tanadar masu da wani adadi na kuɗi idan suna buƙatar a bar su su yi noma, ko a bar kai masu farmaki da kisan gilla ko ƙone masu muhallai.

Daga cikin zantukan barazana da ‘yan ta’addan nan ke yi akwai:

a.       Za mu hana maku noma.

b.       Za mu zo har gidanka mu ɗauke ka.

c.        Kana da labarin abin da ya faru a garin ‘Yankuzo? To za mu yi wanda ya fi shi a garinku.

d.       Za mu kashe su mu ba namun daji su canye.

e.       Za mu yanka su ba abin da ya damemu.

f.        Idan ba ku kawo muna kuɗi ba za mu sanar da ku inda za ku kwashi gawarwakin su.

g.       Muna da makaman da ko gwamnati ba ta da irinsu.

h.       Gyaɗa guda zan yi hasara don na aika shi lahira.

Waɗannan kaɗan ne daga magangannun ‘yan ta’adda na barazana a kan waɗanda ake waya da su don biyan kuɗin fansa ko harajin da suka ɗora wa ƙauye[8].

Kashe- Kashe

Wannan ba sabon al’amari ba ne a cikin aikin ta’addanci. Jihar Zamfara ta tsinci kanta a cikin wannan yanayi na kashe –kashe da ‘yan ta’adda ke yi. Lamarin da ya fara da satar shanu idan mai su ya bi ko ya ce ya ga shanunsa a kasuwa sai a bi shi har gida a kashe.[9]

‘Yan ta’adda sun kashi al’umma da yawa a jihar Zamfara kama daga kisan da suka yi a Kizara da Ɗansadau da Bingi, da Ƙurar Mota da Yankuzo, Yankara, Kurmi, Mada, Kware, Wonaka, Dauran Zurmi, Gurbin Ɓore, Moriki, Faru, Ɓoko, Yanɓaka, Ruwan ɓore, Magazu, wanzamai kai abin ma ya wuce a lisafa. Kusan babu wata ƙaramar hukuma ɗaya a jihar Zamfara wadda ‘yan ta’adda ba su kashi al’umma ba. Kama daga ƙaramar hukumar Gusau babban birnin jihar har zuwa Gummi da wasu ƙauyukanta, Bukkuyum da wasu ƙauyukanta, Mafara da ƙauyukanta, Bakura da ƙauyukanta, Maradun da ƙauyukanta, Shinkafi da ƙauyukanta, Ƙauran Namoda da ƙauyukanta, Barnin Magaji da ƙauyukanta, Zurmi da ƙauyukanta, Maru da ƙauyukanta, Bunguɗu da ƙauyukanta, Tsafe da ƙauyukanta, da Anka da ƙauyukanta[10].

Jaridu da gidajen rediyo sun zo da labarai masu yawa kan kashe-kashen da ake yi a jihar Zamfara kaɗan daga ciki sun haɗa da:

Gidan Rediyon RFI sun wallafa labari mai taken ‘Yan bindiga sun kashe mutane 33 a wani ƙauyen Zamfara.[11] Sun kuma ƙara buga wani a shafin Internet mai taken ‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 da sace sama da 100 a Zamfara.[12]

A gidan rediyo BBc Hausa kuwa an samu labari mai taken “An kashe gwamman mutane a Zamfara”[13]. Akwai wani labari mai taken “ ‘Yan bindiga sun kashe ɗimbin jama’a a Anka”.[14] A gidan rediyon DW kuwa an buga larabi mai taken “Zamfara: ‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama” sun kuma bayyana cewa adadin mutanen da aka kashe ya kai 200.[15]

Jaridar Demokoraɗiyya ta buda labari mai taken “Yadda ‘Yan bindiga suka kashe mutane 40 tare da kai hari a wani asibitin jihar Zamfara. Sun kuma bayyana sunayen ƙauyukan da hare-haren ya shafa wato Damri da Kalahe na ƙaramar hukumar Bukkuyum.[16]

Akwai labarai da yawa irin waɗannan masu alaƙa da kashe-kashe a Zamfara daga gidajen rediyo da jaridu da yawa waɗanda wannan maƙalar ba za ta iya zayyana su duka ba. Akwai a jaridar Amiya, Daily Trust, Leardership, da dai sauransu.

Hijira

Sakamakon ayyukan ta’addanci jihar Zamfara an samu mutane masu ɗimbin yawa da suka yi hijira daga muhallansu na asali suka shiga wasu birane na ciki da wajen jihar. Akwai sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Zamfara kusan kowace ƙaramar hukuma. Yayin da wasu ƙananan hukumomin suna da sansanin da ya kai fiye da ɗaya. Jaridar Daily Trust ta fitar da adadin yawan mutanen da suke a sansanin ‘yan gudun hijira na jihar Zamfara da yawansu ya kai 784000[17]. Gidan talabijin na Channels ya buga labari mai taken “Bandits have Displaced 700000 People in Zamfara – Govt” wato ‘yan ta’adda sun tarwatsa sam da mutane 700000 a Zamfara.[18]Jaridar Vanguard ta rawaito labarin ‘yan gudun hijira a jihar Zamfara inda ta taƙaita labarin a kan kisan mutane 200 da aka yi a ƙaramar hukumar Anka da Bukkuyum tare da haddasa hijirar sama da mutum 10,000 a wannan yankin ta bakin Minista Sadiya Umar Faruq.[19] Akwai bayanai da yawa da aka samu a gidajen rediyo da talabijin da jaridu na Nijeriya da aka buga dangane da hijira a Zamfara sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda.

Ƙorafe-Ƙorafen ‘Yan Ta’adda

Dukkan wannan kashe–kashen da yan ta’adda ke yi suna da dalili. Kamar yadda bincike ya tattaro bayanai daga wasu fayafan muryar yarjejeniya da ‘yan ta’addan da ma na bidiyo da aka kalla duk sun bayyana cewa suna da dalili. Wannan dalilin ta yuwu wasu su karɓa wasu kuma suna ganin rashin ta faɗi ce. Babban dalilin ‘yan bidiga shi ne rashin adalcin hukuma, zaluncin alƙalai, zaluncin Hausawa mazauna gari, zaluncin jamian tsaro da makamantansu.

A wani bidiyo da Shaihin Malami Ahmad Gummi ya ziyarci wasu ‘yan ta’adda don jin dalilin da ya sa suke aikata wannan ta’addanci an kira wani da aka ce shi ne Bello Turji shugaban ‘yan ta’addan yankin Shinkafi da Sabon Birni ya bayyana cewa Hausawa suna kashe masu mutane hukuma ba ta ɗaukar mataki.[20]

A odiyon yarjejeniya tsakanin tsakanin Muhammadu Sani da Gwamnan Zamfara ya bayyana cewa gwamnatin da ta gabata ta bar su ba wani taimako suna cikin mummuna hali wannan ya sa suka ɗauki matakin da suke a kai yanzu.

‘yan ta’addan da suka yi waya da mataimakin shugaban ƙungiya masu saye da sayarwa da gyaran waya na kasuwar Bebeji Plaza nan Gusau sun bayyana cewa hukuma ta bar su kara zube babu wani taimako[21].

Dukkan waɗannan ƙarafe-ƙorafe su ne mafi yawan yan taadda suka fi bayyanawa a matsayin ƙorafinsu. Wasu sukan duba wannan ƙorafi yayin da wasu kuma suke ganin cewa wannan bai isa ya zama sanadin wannan ta’addanci ba.

Sakamakon Bincike

Wannan maƙala ta tattara bayanai ta hanyar sauraran fayafan musayar murya na yarjejeniya da kuma hotunan bidiyo da labarun da aka ji a gidajen rediyo da na talabijin da jaridu da ma hirarraki da aka yi da wasu ɗaiɗaikun mutane a wannan jiha ta Zamfara. Sakamakon wannan bincike da maƙalar ta fitar shi ne:

 Rashin adalcin hukuma ga waɗannan ‘yan ta’adda.

Akwai wasu masu ɗaukar nauyin wannan ta’addanci domin cimma muradunsu.

Shawarwari

Yana da kyau jami’an tsaro da ofishin mai ba gwamna shawara kan lamurran tsaro su riƙa taskace tare da nazarin irin waɗannan fayafayan na yarjejeniya tsakanin ‘yan ta’adda da hukuma ko ɗaiɗaiku. Hakan zai taimaka matuƙa wajen gano yadda za a magance ayyukan taaddanci a Zamfara.

Har ila yau, ana ba da shawara ga gwamnatin jahar Zamfara da ta haɗa kai da sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya ta Gusau; a samar da wata cibiya ta Binciken Laifuka ta Kimiyyar Harshe (Forensic Linguistics).

Gwamnati ta daina barin al’umma suna ɗaukar doka a hannunsu.

Talakawa sun bar al’adunsu masu kyau, kuma sun bar addini. Don haka ya kamata talakawa su dawo da waɗannan al’adun nasu masu kyau, su kuma bi addinin musulunci sau da ƙafa don gyara zamantakewarsu.

Masu hannu da shuni sun riƙa taimaka wa talakawa da abin hannunsu domin talakawan su samu sauƙin rayuwa su daina shiga sabgar taaddanci.

Gwamnati ta taimaka wa talakawa da su kansu Fulani da ke zaune a daji domin su yi sallama da ta’addanci su goyi bayan gwamnati don samar da ci gaba a jihar.

Har wa yau gwamnati ta daina yarda da shigar wasu baƙi a jihar masu ginar zinare na cikin ƙasa da na waje wato turawa domin su ma suna taka rawa wajen haɓaka ta’addanci.

Gwamnatin jihar Zamfara ta fita daga sha’anin siyasar duniya domin ta guje wa shiga tarkon turawa wajen bunƙasa taaddanci a jihar.

Naɗewa

Ayyukan ‘yan ta’adda sun yi yawa musamman a Arewacin ƙasar Nijeriya. Jihar Zamfara ta kasance ‘yan ta’adda suka ƙaddamar da ayyukansu na taaddaci. Sakamakon ayyuakan an samu salwantar rayuka masu ɗimbin yawa, yayin da wasu suka bar mahaifarsu da gonakinsu suka nemi mafaka domin su tsira da rayuwarsu. Wannan maƙala ta fito da wasu daga ayyukan yan taadda da kuma mafarin taaddacin da zantukan yan taaddan, ƙabilunsu, kashe-kashe da aka yi a Zamfara sakamakon taaddanci da kuma gudun hijira da ƙorafe-ƙorafen su masu aikata ayyukan taaddanci. Bugu da ƙari, an bayyana yadda ake amfani da waya wajen ƙulla wata yarjejeniya tsakanin yan taadda da hukuma da kuma karɓar kuɗin fansa.

Manazarta

1.       Abua Ebim, M. (2021). Kidnappers in the News: An Analysis of the Representation of Insurgents and Militants in the Nigerian Press. SSRN Electronic Journal. https: //doi.org/10.2139/ssrn.3998491

2.       Atuwo, A. A (2009). “Ta’addanci A Idon Bahaushe: Yaɗuwarsa da Tasirinsa a Wasu Ƙagaggun Rubutattun Labarun Hausa. Kundin Digirin PhD. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

3.       Block, W. (2008). Should the Law Prohibit Paying Ransom to Kidnappers? Kidnapping|Binding Contracts|Aleinability of Life. American Review of Political Economy6(2). https: //doi.org/10.38024/arpe.106

4.       Bunza, (2017) NAHAWUN MAGANA (Jereƙen Biyar Diddigin Ma’anar Magana da Rabe-Rabenta a Bahaushen Tunani) Takardar da aka gabatar a Sashen Nazarin Hausa Adamu      Augi College of Education Argungu, Kebbi State, a bukukuwan Makon Hausa, 28 ga       Maris, 2017 da ƙarfe 10: 00am na safe a dakin taron na Sashen Hausa Takardar da aka        gabatar a Sashen Nazarin Hausa Adamu Augi College of Education Argungu, Kebbi          State, a bukukuwan Makon Hausa, 28 ga Maris, 2017 da ƙarfe 10: 00am na safe a dakin taron na Sashen Hausa

5.       Bunza, (2019) KURAR GARDI (Tunanin Bahaushe Idan Gari Ya Ci Wuta) Takardar da aka gabatar a taron bukin karɓar digirin farko ga ɗaliban Federal College of Education Technical Gusau, a ƙarƙashin School of Languages, ranar Asabar, 19 ga Oktoba, 2019.

6.       Iyiola, M. L. (2004) Terrorism and the Alqaeda; An Introduction to Terrorism, Lagos

7.       Malumfashi, 1 & Nahuce, M.I (2014) Ƙamusun Karin Maganar Hausa. Kaduna: Garkuwa Media Services.



[1] Wannan tattaunawa ce da aka naɗa yayin da fitaccen shugaban ‘yan fashin dajin nan mai suna Buharin Daji ya yi ta wayar tarho shi da wakilin Emiyan Maru.

[2] A duba kundin digiri Atuwo, A. A (2009). A shafi na 1.

[3] Fassarar bayani daga Gwandu, A.A. (2006), shafi na 2.

[4] Wata hira da gidan rediyon BBC Hausa suka yi da Manjo Hamza Al-Mustafa ɗan takarar Shugabancin ƙasar Nijeriya a ƙarƙashin jamiyyar A.A. a ranar 15 ga watan Mayu 2022

[5] Bunza, (2017) NAHAWUN MAGANA (Jereƙen Biyar Diddigin Ma’anar Magana da Rabe-Rabenta a Bahaushen Tunani) Takardar da aka gabatar a Sashen Nazarin Hausa Adamu Augi College of Education Argungu, Kebbi State, a bukukuwan Makon Hausa, 28 ga Maris, 2017 da ƙarfe 10:00am na safe a dakin taron na Sashen Hausa Takardar da aka gabatar a Sashen Nazarin Hausa Adamu Augi College of Education Argungu, Kebbi State, a bukukuwan Makon Hausa, 28 ga Maris, 2017 da ƙarfe 10:00am na safe a dakin taron na Sashen Hausa

 

[6] Zantawa da Malam Haruna Maikwari, malami a Kwalejin Ilimi da ƙere-ƙere ta gwamnatin Tarayya Gusau, jihar Zamfara. A ranar 5 ga Mayu, 2022 da misalin ƙarfe 12:00nr a Ofishinsa da ke FCE(T) Gusau.

[7] Tun a farko mulkin marigayi shugaba Umaru Musa ‘Yar’aduwa na aka samu wani malami mai suna Muhammad Yusuf ya fara yaɗa da’awar cewa boko haramun ne. Wannan da’awa ta yi sanadiyar rayuwarsa sai almajiransa suka lashi takobin ɗaukar fansa a kansa. Wannan labari na gaskiya ne ya bayyana a jaridu da yawa na ƙasar Nijeriya da ma na waje a lokuta da yawa. Kusan babu wata rana da ba a buga labarin ƙaddamar da harin yan boko haram ba.

[8] Akwai tarin wayoyi da ‘yan ta’addan suke yi da al’umma a jihar Zamfara da suke ɗauke da waɗannan kalamai. Misali idan aka saurari faifan rekodin na Muhammad Sani da shugaban ‘yan sa kai na Ƙaura. Haka idan aka saurari wayan Buba da ɗan ta’addan da ya kira shi amma bai bayyana sunansa ba. Akwai kuma Arɗo wanda yake yankin Shinkafi da ya kira wasu ‘yan sa kai na yankin Shinkafi yana yi masu barazanar za su hana noma a shekarar. Akwai faifan bidiyo da Ƙarami ya yi a bainar jamaa rataye da bindiga yana cewa shi ne ya kashe sojoji ya ƙona masu kunkurai. Akwai wayar da mataimakin shugaban yan kasuwar Bebeji ya yi da ɓarayin da suka yi garkuwa da yaransu inda suka ce in ba a ba su kuɗi ba za su kashe yaran. Akwai dai bayanai masu yawa dangane da wayoyin da suka yi barazanar salwantar da rayuwa da dukiyoyi. Haka ma akwai wasiƙu da suke aikawa a garuruwa daban-daban domin razana alummar da ke yanki.

[9] Tattaunawa da Musa Bala mutumin Kasuwar Daji a ranar 18 ga Yuli, 2022 a Gusau Unguwar Samaru da yamma misalin ƙarfe 5:00 ny. Wanda ya shaidi wannan lamari kusan sau uku a faɗarsa.

[10] Bayanai sun gabata a gidajen watsa labari da manyan jaridu na ƙasar nan Nijeriya duk sun zo da labarai a kan kashe-kashen jihar Zamfara. Wasu yan sa kai kan fara yayin da wasu kuma yan bindiga ke yi. Sai dai binciken wannan maƙalar ya gano cewa yan taaddan sun fi kisa mai yawa.

[11] Labarin da aka buga a safin Internet a ranar 5 ga Febareru, 2022.

[12] Labarin da aka baga a shafin Internet a ranar 23 ga Ogusta, 2021.

[13] An buga shi a 18 ga Nuwanba, 2019.

[14] An buga a 7 ga Junairu 2022.

[15] An buga a ranar 9 ga Junairu, 2022.

[16] An buga wannan labari a ranar 8 ga Mayu, 2022.

[17] An buga wannan labarin a ranar 27 ga Ogusta, 2021

[18] An buga wannan labari a ranar 20 ga Mayu, 2022

[19] An buga wannan a ranar 10 ga Junairu, 2022.

[20] Turji ya bayyana haka a cikin wani hoton bidiyo da aka ɗauka a lokacin da Ahmad Gummu ya kai masa ziyara. Ya ƙara da cewa ya yi noma sama ga buhu 170 amma Hausawa suka zo suka ƙona masa abinci ko buhu 5 bai fita da su ba. Haka kuma idan rikici ya samu tsakanin Fulani da Hausa sai Hausawan su yanka Bafillacen da suke rikici da shi kuma hukuma ba ta ɗauki wani mataki ba. Ya kuma ce an kashe kawunsa da wau ‘yan uwansa. Turji dai ya kuma ce gwamnati ta bar su a daji babu ilimi babu abin more rayuwa yayin da a birni wasu na karɓar albashi.

[21] A saurari odiyon waya tsakanin mataimakin shugaban ƙungiya masu saye da sayarwa da gyaran waya na kasuwar Bebeji Plaza nan Gusau

DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.016

Post a Comment

0 Comments