Cite this article as: Sani, A-U., Maikwari, H.U., & Bazango, B. (2022). Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashintashinar Zamfara. In Bakura, A.R. et al (eds). Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, Vol. 1, Issue 1, p. 95-107.
Haruna Umar
Maikwari
Babangida Bazango
Tsakure
A yau, kafafen sada zumunta sun kasance wani ɓangare na rayuwar al’umma, musamman matasa. Suna da tasiri (mai kyau ko marar kyau ko duka biyu) a ɓangarorin rayuwa daban-daban da suka haɗa da zamantakewa da kasuwanci da ilmi da sana’o’i da mulki da shugabanci da makamantansu. La’akari da haka ne ya sa wannan bincike ya yi ƙoƙarin haska fitilarsa domin ƙyallaro ko kafafen na da tasiri a kan tashe-tashen hankulan jahar Zamfara? Idan suna da , yaya nau’in tasirin yake? Binciken na da manufar (i) bitar yanayin tashe-tashen hankulan jahar Zamfara, da (ii) nazartar tasirin kafafen sada zumunta kan waɗannan tashe-tashen hankula. Kasancewar Zamfara ɗaya daga cikin manyan daulolin ƙasar Hausa masu tsohon tarihi. Binciken ya yi amfani da Bahaushen ra’i domin jan akalarsa. An ɗora aikin a kan tunanin Bahaushe mai cewa: “kowane allazi da nasa amanu.” An bi manyan hanyoyi guda biyu domin tattara bayanai. Na farko shi ne hira da aka yi domin samun bayanan nau’ukan tashe-tashen hankulan daga tushe (ganau ko jiyau daga ganau). Na biyu kuwa, an bibiyi kafafen sada zumunta da sauran kafafen sadarwa na yanar gizo (intanet) domin ganin wainar da ake toyawa dangane da batun da ake magana kansa, tare da tattarowa da nazartar bidiyoyi da hotuna da rubuce-rubuce da suka shafi manufar binciken. Binciken ya gano cewa, duk da ɗimbin amfanin kafafen sada zumunta, suna taka rawa kai tsaye ko a kaikaice wajen ruruta wutar tashe-tashen hankular jahar Zamfara. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da kira ga hukomomi da su fara tunanin yin wata huɓɓasa na bibiya da jagorancin al’amuran kafafen sada zumunta.
Fitilun Kalmomi: Zamfara, Kafafen Sada Zumunta, Tashe-Tashen Hankula
1.0 Gabatarwa
Duk da kiran da Abubakar Ladan Zariya ya
yi cewa: “Fitina Bacci take ba ta fita," da kuma tofin Allah wadai da ya
yi wa masu tado da ita,[1]
wasu kam ko a jikinsu wai an tsikari kakkausa. A ‘yan shekarun
baya-bayan nan, musamman daga wajajen 2013 abin da ya yi sama, an ci gaba da samun
tashe-tashen hankula nau’uka daban-daban. Tashe-tashen hankulan sun haɗa da garkuwa da mutane da kai farmaki kan al’umma musamman mazauna
karkara da sace-sace.
Zamfara ƙasar
Hausawa ce,[2] wadda
kuma tana daga cikin (ƙannai bakwai) banza bakwai. A hirar da aka yi
da Bunza, (2019) a gidan rediyon
Pride FM na Gusau, ya bayyana ra’ayin cewa: “A yi ƙoƙarin binciko
tushen Hausa daga Zamfara.” A bisa wannan dalili, akwai buƙatar gudanar da
Bahaushen nazari dangane da yanayin da ƙasar
ta tsinci kanta.
Kamar yadda Bahaushe ya faɗa: “Ruwa ba ya
tsami banza.” Dole ne a gano yadda ƙasar al’umma da ke da
tarihi na tarbiyya da zamantakewa mai nagarta (halaye da ɗabi’un Hausawa na ƙwarai) ta wayi gari cikin halin tashin hankali . Bincike-binciken
da za a gabatar na iya shafar ɓangarori da dama,
sannan na iya kasancewa ta fuskoki da dama, duk dai domin a gano:
i.
Mafari
ko tushen inda
matsalar take domin a yi wa tufkar hanci daga tushe,
ii.
Gano tasirin nau’ukan kayayyakin amfanin
yau da kullum wurin ruruta lamarin,[3]
iii.
Ƙoƙarin gano waɗanda ke da hannu cikin tashe-tashen hankulan kai tsaye ko
a kaikaice domin shawo
kan matsalar.
iv.
Nazartar fasali da
siga na tashe-tashen hankulan domin ba da hasken kan yadda za a tunkari
matsalar.
Wannan bincike ya
ta’allaƙa kan mas’ala ta biyu (ii) da aka zayyana a
sama. Binciken ya mayar da hankali wajen nazartar tasirin kafafen sada zumunta
a tashe-tashen hankulan na jahar Zamfara. Farfajiyar binciken ba ta wuce jahar ta
Zamafara ba. Saboda haka, ko da akwai yanayi makamancin wanda ake magana a kai,
ba za a waiwaice shi ba idan dai ya fita daga bagiren binciken.
1.1 Manufar Bincike
Babban manufar
wannan bincike ita
ce nazartar yanayi da matsayin kafafen sada zumunta a tashe-tashen hankulan
jahar Zamfara. Kai tsaye aikin zai mayar da hankali kan:
i.
Bitar yanayi da
sigar tashe-tashen hankulan jahar zamfara, da
ii. Nazartar rawar da kafafen sada zumunta ke takawa a tashe-tashen hankulan.
1.2 Ra’in Bincike
Ƙasar Zamfara na ɗaya daga cikin ƙasashen Hausa masu tsohon tarihi. Wasu daga
cikin masana na ganin cewa: “Idan za a lalubo asalin Bahaushe da
tushen Hausa, to a neme shi a Zamfara.”[4]
A bisa wannan dalili, aikin ba zai je wani wuri daban domin kalen ra’in da zai
masa jagora ba. An ɗora aikin kan
ragamar tunanin Bahaushe da ke cewa: “Kowane allazi da nasa amanu.” A bisa
wannan tunani, kafafen sada zumunta sun kasance hanjin jimina, wato akwai na ci
akwai na zubarwa. Ma’ana ke nan, suna taka rawa iri biyu dangane da
tashe-tashen hankulan Zamfara. Suna
taimakawa a ɓangare guda, a ɓangare ɗaya kuwa suna ƙara iza wutar
matsalar. Idan haka ne kuwa, ya rage ga wannan bincike ya bi dabaru da hanyoyi
mafiya dacewa domin tabbatar da wannan ikirari ko ƙaryata shi.
1.3 Hanyoyin Gudanar da Bincike
An bi manyan hanyoyi uku wajen
gudanar da wannan bincike. Ta farko ita ce bitar ayyuka daban-daban da aka
gudanar dangane da tashe-tashen hankula musamman waɗanda suka shafi jahar Zamfara. Wannan ya ba da haske game
da yanayin tashe-tashen
hankulan.
Bayan wannan, wata hanya da aka yi amfani da ita
wajen tattara bayanai ita ce bibiyar kafafen sada zumuta domin zaƙulo hotuna da
bidiyoyi da rubuce-rubuce dangane da batun. An yi ƙoƙarin sakaye sunayen waɗanda suka ɗora ire-iren
bayanan a kafafen na sada zumunta saboda dalilai na tsaro.
Daga ƙarshe kuwa, an yi
hirarraki da mutane daban-daban sannan a matakai mabambanta. Yayin waɗannan hirarraki, an yi la’akari da wurin zama da shekaru
da ilmin duniya da kuma cuɗanya da kafafen
sada zumunta daga ɓangaren waɗanda aka yi hirar da su. Manyan ɓangarorin da hirarrakin suka taɓo su ne:
i.
Tantance ingancin
duk wasu bayanai da aka samu daga kafafen sada zumunta, da
ii.
Samun bayanai game
da yanayin tashe-tashen
hankulan jahar Zamfara, da
iii.
Samun bayanai
dangane da tasirin kafafen sada zumunta kan tashe-tashen hankulan jahar
Zamfara, da kuma
iv.
Tantance bayanai da
aka samu daga hirarrakin.[5]
1.4 Bitar Matsayin
Kafafen Sada Zumunta a Zamantakewa
A duniyar yau, kafafen sada
zumunta sun zama wani ɓangare na rayuwar
al’umma. Kusan za a iya cewa, duniyar mutane ba za ta iya rayuwa ba sai da su.
Dalili kuwa shi ne, rayuwar mutane da dama ta dogara kacokan kan ire-iren waɗannan kafafe. Nan ne cinsu,
nan ne shansu![6] A rahoton da Clement,
(2019: 2) ya fitar, masu amfani da kafar Whatsapp a wata kaɗan sun kai kimanin biliyan guda da miliyan ɗari biyar (1,005,000,000). Binciken da Jayasekara, (2015) ya gudanar ya nuna cewa, ana samun ƙaruwar masu amfani da kafafen sada zumunta matuƙa.
Masana da manazarta da dama sun yi bincike da
rubuce-rubuce game da tasirin kafafen sadarwa a zamantakewa.[7] Siddiqui
& Singh sun bayyana cewa:
Now a day’s social media has been the important part of
one’s life from shopping to electronic mails, education and business tool.
Social media plays a vital role in transforming people’s life style. Siddiqui & Singh, (2016: 71)
Fassara
A yau, kafafen sada zumunta sun zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar ɗan’adam tun daga kan sayayya da tura saƙonni da ilimi har zuwa
kasuwanci. Kafafen sada zumunta suna taka muhimmiyar rawa dangane da salon
rayuwar mutane.
Lallai wannan batu haka yake, domin kuwa ko a ƙasar Hausa akwai mutane da dama da suka raja’a matuƙa kan kafafen na
sada zumunta. Akwai muhimman ɓangarorin rayuwa da waɗannan kafafe suka
fi shafa. Sun haɗa da:
i.
Sada
zumunta
ii.
Tattaunawa a matakin ɗaiɗaiku ko ƙungiyoyi
iii.
Kasuwanci da cinikayya
iv.
Ilimi da karantarwa
1.
Tun farko dai waɗannan kafafe an samar da su ne domin sada zumunta. Misali, Facebook da aka
samar a wajajen 2004, ya kasance huɓɓasa ne na ɗalibin Jami’ar Harvard mai suna Mark
Zuckerberg. Ya ƙirƙire shi ne a matsayin kafar sada zumunta tsakanin ɗaliban makaranta. Sannu a hankali ɗaliban wasu makarantu na daban suka fara amfana da shi.[8]
A shekarar 2006 ne kuma aka fitar da shi a matsayin kafar sada zumunta da
duniya gaba ɗaya za ta iya
amfani da shi
(Baruah, 2012: 4; Clement, 2019: 2). A zuwa yau, Facebook ke kan gaba duk cikin kafafen sada
zumunta. Wasu daga cikin fitattun kafafen sada zumunta bayan shi sun haɗa da:
a.
Instagram
b.
Twitter
c.
Whatsapp
2.
A ɓangare guda kuwa, ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da kuma
ma’aikatu na amfani da waɗannan kafafe wajen
tattaunawa. A tattaunawar da aka yi da Babban Mai Kula da Ayyuka (Senior Vendor
Manager) na kamfanin Amsoshi Digital Services[9],
ya bayyana cewa:
Ta hanyar kafafen sada zumunta ne kamfani ke samun damar tattaunawa alhali kowa yana gidansa... Matsalar da aka fi fuskanta ita ce, har yau an bar Hausawa a baya a wannan fanni. Ko da tattaunawa za a yi, sun fi ganewa da Whatsapp kawai da Facebook, watakila saboda sun fi sauƙin sha’ani. (Arabi, 2019)
Ko ba komai, kafafen na tallafa wa kamfanoni wajen sauwaƙa kuɗaɗen zirga-zirga
(don zuwa tarurruka). A maimakon tafiye-tafiye domin ganawa, akan tattauna ne
kawai ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.
3.
Ana amfani da kafafen sada zumunta wajen kasuwanci. A
wannan ɓangare matan
Hausawa ma ba a bar su a baya ba wajen morar wannan dama. Kafafen sun taimaka
wajen ba wa mata damar gudanar da kasuwanci a natse, ba tare da dole sai sun fita waje
domin kasa haja ba. A maimakon hakan, suna kasa hajar ne bisa iska a kafafen
sada zumunta. Waɗanda suka yaba, za
su tuntuɓa ta waɗannan kafafen. A hirar da aka yi da Malama Sa’adatu Umar Ɗandare, ta bayyana
ra’ayinta game da matsayin kafafen sada zumunta kamar haka:
A nawa kasuwanci, kafafen sada zumunta su ne jigon kasuwa
saboda kayan da duk zan saya ta intanet zan gan su, kuma ta nan zan sayar da
su. (Ɗandare, 2019)
Shi kuwa Malam Muhammad Zulyadain[10]
yana ganin ai rayuwa ma kacokan ba ta yiwuwa a yau sai da kafafen sada zumunta.[11]
A ɓangaren
kasuwancinsa, ya ce:
Yanzu kusan kasuwanci ya koma yanar gizo kama daga manya
har ƙananan kasuwanci... Kaso mafi yawa (ɓ75%) na abokan
huldar kasuwancina muna haɗuwa ne a kafafen sadarwa. (Zulyadain, 2019)
4.
Tuni kafafen sada zumunta suka zama wani fili na koyo da
koyarwa. Ko bayan rubuce-rubuce da hotuna da bidiyoyi da odiyo-odiyo na ilmi da
ake yaɗawa ta kafafen,
akwai shafuka da zauruka da ake buɗewa na musamman
domin karantarwa. Karatun
kuwa yakan shafi ɓangarorin rayuwa daban-daban. Sun haɗa da addini da kimiyya da kiyon lafiya da ilmin intanet
da ilmin kwamfuta da ilmin zamantakewa da ilmin kasuwanci. Wasu daga cikin
fitattun makarantun da ake da su kan kafafen sada zumunta sun haɗa da:
a.
Hausa Musical Institute
b.
Makarantar Malam Bambadiya
c.
Zauren Markazus Sunnah
2.0 Tashe-Tashen Hankula a Zamfara
A shekarun baya, tun kafin shekarar 2007, Zamfara ta kasance
cikin ruwan sanyi.[12]
A wancan lokaci, akan samu ƙananan laifuka ne kawai irin su sace-sace ko rashin
jituwa tsakanin al’umma da kan kai ga faɗa da dai makamantansu.[13]
Aminu, (2020)[14] ya bayyana cewa: “A
wancan lokaci, babban aikin ta’addanci da ke
wakana shi ne faɗa tsakanin matasan
shiyar gabas da na
yamma.” Faɗan na yin tsananin da har yakan kai ga samun munanan
raunuka ko ma rasa rayuka. Wani nau’in aikin ta’addanci da ake samu wanda kan
kai ga munanan raunuka ko rasa rai shi ne bangar siyasa.
Daga wajajen 2008
ne kuma aka samu ɓullowar
tashe-tashen hankula cikin nau’uka daban-daban da suka haɗa da:
i.
Fashi da makami
ii.
Satar
shanu
iii.
Garkuwa da mutane
iv.
Hare-hare (Almustapha, 2020; Aminu, 2020; Ibrahim, 2020)[15]
Tsakanin 2008 zuwa
2019 an samu rashe-rashen rayuwa da salwantar dukiyoyi sakamakon waɗannan tashe-tashen hankula. Duka waɗannan ayyuka akan danganta su ne da Fulani. Binciken ya
ci karo da bayanan da ke tabbatar da cewa, tushen tashe-tashen hankulan ya samu
tsira ne a sakamakon fansa da Fulanin suka ƙuduri ɗauka game da rashin adalci da suke ganin an yi masu. Wannan ya kasance ta fuskoki biyu:
i.
Bayan an fara samun yawaitar fashi da makami, wasu daga
cikin jami’ai ‘yan sa kai sun danganta abin da ayyukan Fulani. Daga nan ne suka
ɗauki mataki kan Fulanin da suke zargin na da hannu cikin
fashi da makamin. A hirar da aka yi da Almustapha, (2020) da Ibrahim, (2020)
sun tabbatar da cewa, ɗaya daga cikin
shuwagabannin Fulanin ya taɓa bayyanawa ƙarara cewar sun
kai wasu hare-haren ne a matsayin ɗaukar fansa. Daga
cikin garuruwan da aka kai wa waɗannan hare-hare na
ɗaukar fansa akwai Kizara da ke ƙaramar hukumar
Gusau da ‘Yargaladima da ke ƙaramar hukumar Maru da kuma wasu ƙauyukan yankin Ɗansadau.
ii.
Aminu, (2020) ya bayyana a hirar da aka yi da shi cewa,
wasu daga cikin masu hannu cikin tashe-tashen hankulan sun yi iƙirarin bin hanyar sakamakon karya masu alƙawari da aka yi.
Sun bayyana cewa, ‘yan siyasa sun masu alƙawura
goshin zaɓen 2007 (yayin da ‘yan siyasar suka ɗauke su a matsayin ‘yan bangar siyasa). Bayan zaɓe kuwa, sai aka yi abin da Bahaushe ce ke cewa: “An ci
moriyar gangan, an ya da goronta!” Ko ma dai yaya abin yake, to “da walakin
goro a miya,” domin kuwa “ruwa ba ya tsami banza.”
iii.
Wasu daga cikin masu riƙe da makaman na
ikirarin cewa, an ƙwace gonakan da suke noma an mallaka wa ‘yan siyasa. Hakan ya samar masu da takunkumin tattalin arziki da
dole sai sun nemi mafita. Idan laila ta ƙiya sai a koma basha.
iv.
Wasu kuwa na kukan cewa, burtalan[16]
da suke bi aka mayar gonaki. Shiga gonakan kuwa ya kasance laifi da ke janyo
hukunci ga duk wanda ya aikata. Wannan ya sa makiyayan suka kasance cikin
wahala. Da tura ta kai bango, sannan tafiya ta yi tafiya, sai hannun agogo ya
juya.
v.
Akwai kuma masu ikirarin cewa, an fara samun yawaitar
tashe-tashen hankulan ne tun lokacin da aka fara sace wa Fulanin yankin
dabbobinsu. A wannan lokaci, ɓarayin shanun ɗauke da makamai na far ma ƙauye tare da
kwashe shanu masu adadi da yawa. Dabbobin kuwa na daga cikin kaso mai tsoka
daga ɓangaren tattalin
arziki wanda makiyayan suka dogara a kai domin rayuwa.[17]
A ɓangare guda kuwa, akwai masu yi wa tashe-tashen hankulan
kallo na daban. Dangane da musabbabinsu, tashe-tashen hankulan, binciken ya ci
karo da ra’ayoyi da suka haɗa da:
i.
Akwai waɗanda ke da
fahimtar cewa, ummulhaba’isin waɗannan fitintinu shi ne albarkatun ƙasa (musamman
zinare)[18]
da Allah ya azurta ƙasar Zamfara da shi. Hakan ne ta sa ake ta ƙirƙirar tashe-tashen
hankula domin kore mazauna ƙauyuka daga muhallansu. Hakan zai ba da damar haƙar zinaren hankali
kwance.
ii.
Wasu kuwa, musamman malaman addinin Musulunci, na da fahimtar
cewa tashe-tashen hankulan jarabawa ce daga Ubangiji. Suna faruwa ne sakamakon
gurɓacewar halayyar
mutane. Kai tsaye sukan danganta shi da ayyukan tsafe-tsafe da ake gudanarwa,
musamman waɗanda suka shafi
wasa da Alƙur’ani mai tsarki.[19]
Lokacin da
tashe-tashen hankulan suka yi tsamari musamman daga wajajen 2016, mazauna wasu ƙauyuka sun yi
gudun hijira zuwa garuruwan da ke kusa da su. Daga nan ne kuma labaran
tashe-tashen hankulan suka mamaye duniyar intanet. Hotuna da bidiyoyi da
rubutattun labarai game da su, duk suka mamaye kafafen sada zumunta. Ibrahim,
(2019) a hirar da aka yi da shi ya tabbatar da cewa, adadin mutanen da suka yi
gudun hijira na da yawa sosai. Ya ce:
Wasu daga cikinsu
sun samu taimako daga mutanen gari. Wasu sun ɗauki haya. Wasu
kuwa sun zauna a cikin makarantu. Wasu kuma an ba su wurare aro sun zauna. (Ibrahim, 2019)
Hukumomi sun yi ta
bin hanyoyi daban-daban domin shawo kan lamarin. Daga cikin har da ƙoƙarin neman sulhu
da ƙusoshin
tashe-tashen hankulan. A
wajajen ƙarshen 2019 zuwa farkon 2020 ne aka samu sulhun da ya kai ga raguwar
tashe-tashen hankulan. Sulhun ya kasance wani yunƙurin samar da
zaman lafiya na gwamnatin da aka zaɓa a shekarar 2019.
3.0 Gurbin Kafafen Sada Zumunta a
Tashe-Tashen Hankulan Zamfara
Kafafen sada zumunta suna taka rawa iri biyu dangane da
tashe-tashen hankulan jahar Zamfara. A ɓangare guda suna taimakawa ta wasu fuskoki da suka shafi faɗakar da jama’a dangane da abubuwan da ke faruwa tare da
miƙa ƙoƙon bara na neman
addu’o’i daga al’ummu na kusa da na nesa, da makamantansu. A ɗaya ɓangaren kuma,
kafafen sada zumuntar suna ƙara wa wuta karmami. Sukan yi hakan ta fuskar ruruta
zance da yaɗa jita-jitan ƙarya da cusa tsoro
a zukatan mutane.
A gaskiya tasirin
kafafen sada zumunta game da tashe-tashen hankulan zamfara nau’i biyu ne. Suna
amfanarwa a gefe guda. A gefe guda kuwa cutarwa suke yi...[20] (Maikwari, 2019)
A taƙaice dai, kafafen
na sada zumunta sun zama hanjin jimana, wato akwai na ci akwai na zubarwa. An
raba rawar da kafafen sada zumuntar ke takawa dangane da tashe-tashen hankula a
Zamfara zuwa manyan rukune biyar kamar haka:
Jad. 1: Manyan Nau’ukan Tasirin Kafafen
Sada Zumunta a Kan Tashe-Tashen Hankula a Zamfara
|
Masu Kyau |
Marasa Kyau |
1. |
Faɗakarwa |
Ta da Hankali |
2. |
Ƙoƙon Bara |
Yaɗa Ayyukan Ta’addanci |
3. |
Bunƙasa Adabi |
|
3.1 Faɗakarwa
Faɗakarwa kalma ce mai kinin ma’ana da nusarwa ko nusatanwa
ko tunatarwa. Bunza, (2013: 2) ya ba da ma’anar wannan kalma da cewa: “Faɗakarwa hanya ce ta ilmantar da mutane ko yi musu nasiha
da tunatar da su don jan hankalinsu kan wani abu muhimmi na rayuwarsu.”[21]
Kafafen sada zumunta na faɗakar da al’ummomi
na kusa da na nesa dangane da tashe-tashen hankulan jahar Zamfara ta fuskoki
kamar haka:
i.
Bayanai dangane da abubuwan da ke faruwa a daidai wata
rana sannan daidai wani lokaci na saurin watsuwa ta kafafen sada zumunta.
Wannan na taimaka wa al’umma wajen guje wa faɗawa yankunan da abin ya shafa.[22]
ii.
Ana tura nau’ukan faɗakarwa daban-daban na yadda mutane za su guje wa faɗawa cikin tarkon waɗannan masu ta da hankula. Wannan ya shafi labarai na yadda wasu suka faɗa tarkon masu ta da hankulan, wanda hakan na matsayin
hannunka mai sanda da darasi ga mai karanta labarin. Ko da ma dai an ce, “Gani
ga wane ya ishi wane tsoron Allah.” Wasu lokuta kuma kai tsaye ake kawo bayanai
kan abubuwa da ya kamata mutane su kiyaye.
iii.
Akwai faɗakarwa da ta shafi jan hankali al’umma musamman
matasa daga nisanta kansu daga
ire-iren waɗannan tashe-tashen
hankula. Wannan na iya kasancewa ta fuskar wa’azantarwa da nuna illolin shiga
cikin ire-iren ayyukan.
3.2 Ƙoƙon Bara
Ƙoƙon bara salon magana ne da
ke ɗaukar ma’anar miƙa koke domin neman wani
biyan buƙata.[23]
Masana da marubuta daban-daban sun yi rubuce-rubuce kan bara musamman a ƙasar Hausa. Wasu daga
cikinsu sun haɗa da Karofi, (1980) da
Bashir, (1991) da Sarkin Gulbi, (2007).[24]
Ƙoƙon bara a wannan
bincike na nufin kai koke da zimmar neman agaji.
Rubuce-rubuce da
ake ɗorawa dangane da
halin da al’umma kan shiga a lokacin tashe-tashen hankulan na zaman ƙoƙon bara. Mutanen
da ke cin kare da rubuce-rubucen (da ma maganganu da ake turawa ta odiyo), a ƙalla sukan taimaka
da addu’a. A wasu lokutan kuwa, ire-iren rubucen na jefa ɗimbin tausayi a zukatan al’umma. Wannan ya sa masu gudun
hijira daga cikin waɗanda abin ya shafa
sukan samu tallafi a garuruwa da ƙauyukan da suka yi hijirar zuwa gare su. Nau’ukan
tallafin da suke samu sun haɗa da:
i.
Matsuguni
ii.
Abinci
iii.
Tufafi
iv.
Kuɗi
v.
Abubuwan buƙatun yau da kullum kamar sabulu da omo da makamantansu.
Hoto 1: Rubutaccen Labarin Tashe-Tashen Hankulan Jihar Zamfara da kan Waz’af
Madogara: An ɗauko wannan hoto
daga Whatsapp ranar 29 ga watan Disemba, shekarar 2019.
A wajajen watan
Disemba na shekarar 2018, na kasance ganau ba jiyau ba dangane da wannan
lamari. A unguwar Sabon Gari da ke Damɓa a Gusau ta Jahar Zamfara, akwai mutane kimanin 18 da suka taso daga ƙauye bayan zaman
can ya masu tsauri. Mafi
yawansu mata ne da ƙananan yara. Ɗaya daga cikinsu ta san wani dattijo a nan Damɓa. A bisa haka, sai suka tare gidansa. Dattijon mai ƙaramin ƙarfi ne matuƙa. Bisa wannan
dalili, sai ya garzaya masallacin da ke kusa da su ya kai kukansa. Al’ummar
wannan masallacin
ne ta ɗauki nauyin ci da
shansu har ranar da suka bar Damɓa. A kullum liman
na neman taimakon kuɗin abincinsu na
wannan rana. Mu kuma mamu mu bayar.[25]
A hirar da aka yi
da Ibrahim, (2019) da Maikwari, (2019) an samu bayanai dangane da wuraren da
‘yan gudun hijira suka zauna. A yayin zaman nasu, sun samu tallafi da kulawar
jama’a. Wasu daga cikin wuraren su ne:
i.
Makarantun
gwamnati musaman
firamare da sakandare na je-ka-ka-dawo[26]
ii.
Sakateriyoyin wasu ƙananan hukumomi[27]
iii.
Shaguna da rumfuna a kasuwanni
iv.
Tashoshi
v.
Gidajen jama’a
vi.
Masallatai
3.3 Bunƙasa Adabi
Wani abin jan
hankali dangane da adabi shi ne, ba sai yanayin lumana ko yadda zuciya ke so ke
samar masa abinci ba. A maimakon haka, sau da dama mummunan yanayi ko ƙunci ko tashin hankali
ko dai wasu abubuwa na ƙi na samar da tubalan ginin sabbin falsafofi a duniyar adabi. Tashe-tashen hankulan Jahar Zamfara sun taka rawar
gani wajen samar da ƙirƙire-ƙirƙiren adabi da suka
haɗa da waƙoƙi da karuruwan
magana musamman na zamani.[28]
Jad. 2: Waƙoƙi da Aka Samu a Sakamakon Tashe-Tashen
Hankulan Jahar Zamfara
Sunan Waƙa |
Mawaƙi |
Nau’in Waƙa |
Bazamfariya |
Dr. Aliyu U. Tilde |
Rubutacciya |
Waƙar Kidnafas[29] |
Abdulhamid M. Sani |
Rubutacciya |
Yau ga Allah Muka Koma |
|
Waƙar Zamani[30] |
Zamfara Babu Lafiya |
Sagir Yusuf |
Rubutacciya |
Haƙiƙa waɗannan waƙoƙi sun kasance ci gaba ga adabin Hausa musamman ɓangaren waƙa. Ko baya ga haka, sun taimaka wajen jawo hankalin
al’umma musamman domin dogewa bisa addu’o’i da gyara halaye da zamantakewa, duk
dai domin samun sauƙin lamarin.
Jad. 3: Sabbin Karuruwan Magana da Aka Samu a
Sakamakon Tashe-Tashen Hankulan Jahar Zamfara
Sabuwar Karin Magana |
Tsohuwar Karin Magana |
Ba da ni ba, neman aure a Ɗansadau |
Ba da ni ba gaɗa a maƙabarta/hurumi |
Ba kanta, an sace mai garin Ɗansadau |
|
Ana Maiduguri sai ga Zamfara |
Ana kukan targaɗe sai ga karaya |
Ana Boko Haram sai ga kidnafas |
Ana kukan targaɗe sai ga karaya |
Ritaya sa! An tura ɗansanda dejin Ɗansadau |
|
Duk kun raba mini hankali, an ce da ɗansanda ya baro Borno ka koma Ɗansadau |
Duk kun raba mini hankali, an ce da
rago sha hura ka tafi gona |
Ta nan muka
fara, ɗan Borno ya ga Bazamfare |
Ta nan muka
fara, kuturu ya ga mai ƙyasfi |
Madogara: Hirarraki[31]
A jadawali na uku
da ke sama, an ga jerin misalan karuruwan magana da suka samu sakamakon
tashe-tashen hankulan a jahar Zamfara. Wasu daga cikin an yi amfani da tsoffin
karuruwan magana ne wajen samar da su. Wato an kwaikwayi falsafar da ke cikin
tsoffin karin maganar ne domin ƙirƙira su.
3.4 Ta da Hankali
A cikin wannan
bincike, ta da hankali na nufin jefa tsoro ko firgici ga zukatan al’umma.
Binciken ya gano cewa, ɗaya daga cikin
illolin kafafen sada zumunta dangane da tashe-tashen hankulan jahar Zamfara shi
ne jefa tsoro da zaman ɗar-ɗar a zukatan al’umma na kusa da na nesa. Abin lura a an
shi ne, kafafen watsa labarai sukan tace sahihancin labari kafin fitar da shi.
Ko bayan nan ma, sukan ba da labarai ta salo da sigar da ba za su kasance masu
ta da hankalin al’umma ba.
A bangare guda
kuwa, labaran da ake yawo da su ta kafafen sada zumunta ba tatattu ba ne. Wasu
ma na ƙarya ne. Wasu
lokutan jita-jita ce ma tsura ake rurutawa. Saboda haka, labaran da ke fita
daga kafafen sada zumunta sun fi muni da ta da hankali.[32]
Wannan rashin kwanciyar hankali ga masu karanta labaran na faruwa ta fuskoki da
dama. A ƙasa an kawo misalan wasu daga cikin hotuna da aka ci karo da su waɗanda za su iya ta da hankulan masu gani.
Hoto 2: Hoto Mai ta da Hankali da aka Ɗola a Fesbuk
Madogara: An ɗauko wannan hoto daga Fesbuk.[33]
A hirar da aka yi da malaman makarantar da ake ikirarin wannan abu ya faru, sun bayyana cewa labarin ba haka yake ba. Abu makamancin haka ya faru, amma ba yadda aka kawo labarin ba. An kawo wannan labari a Fesbuk cikin sigar da zai iya janyo ƙiyayya da rikici irin na addini. Ko bayan haka, hoton kansa ya kasance mai ta da hankali
Hoto 3: Gawarwarki da yawa da aka jejjera su
cikin rami guda
Hoto 4: Hotunan gawarwaki a kwakkwance
A hirar da aka yi
da Maikwari, (2019) ya bayyana cewa:
A yanzu haka akwai
guruf-guruf da aka buɗe a kafafen sada zumunta musamman
Whatsapp waɗanda suke yaɗa farfagandar ƙarya sakamakon ƙin jinin gwamnati mai ci da suke yi. Kullum sukan ƙago labaran da ke nuna ana samun daɗuwar tashe-tashen
hankula. Yayin da aka bincika, wani lokaci sai a tarar sunayen ƙauyukan da suka zayyana babu su kwata-kwata ma a jahar
Zamfara. (Maikwari, 2019)
Idan kuwa haka ne,
lallai matsalar ta kai inda ta kai. Dole ne kuma gwamnati da sauran hukumomi waɗanda abin ya shafa su tashi tsaye domin daidaita sahun
amfani da kafafen sada zumunta.
3.5 Yaɗa Ayyukan Ta’addanci
A duk lokacin da
mutane (musamman yara) ke kallon ayyukan ta’addanci, zuciyarsu tana ƙara bushewa ne da ƙeƙashewa. Sannu a
hankali tausayin da suke ji zai riƙa raguwa. Za a kai gacin da kwata-kwata nau’ukan
ta’addancin ba sa wani tasiri irin na sanya tausayi ko jin ƙai a zukatansu.
A ɓangare guda kuwa, yana koya wa yara hanyoyin aikata
rashin gaskiya daban-daban. Daga cikin nau’ukan abubuwan da ke ƙunshe a kafafen
sada zumunta waɗanda kuma ke da
alaƙa da ta’addanci
akwai:
i.
Hotuna da bidiyoyi da labarai a kan makamai da yadda ake
sarrafa su.
ii.
Hotuna
da bidiyoyi na makamai da yadda ake safarar su.
iii.
Hotuna da bidiyoyi da labaran kashe-kashe.
iv.
Hotuna da bidiyoyi da labarai game da ayyukan ta’addanci
da aka aikata irin su fashi da makami da sata da garkuwa da mutane da
makamantansu.
A ƙasa an kawo ‘yan
misalai waɗanda aka tattaro
daga kafafen sada zumunta.
Hoto 5: Bindigogi da Alburusai a Fesbuk
Madogara: An ɗauko wannan hoto ranar 2 ga watan Janairu, shekara ta 2020 daga Fesbuk.
A hoto na 5 da ke sama, za a ga hoton bindigogi da kuma alburusai. A ƙasar Hausa an saba ganin yadda yara ke kwaikwayon wasa da bindigogi waɗanda suke haɗawa da kara ko ‘yan itatuwa. Masu wayo daga cikinsu suna amfani da fayif da ƙaramin katako ko falanki da ashana domin yin bindigar wasa wadda take ƙara. Duka waɗanan na faruwa ne sakamakon kallace-kallacen hotuna da bidiyoyin nau’ukan bindigogin da kuma yadda ake sarrafa su. A bisa wannan dalilai, kai tsaye ire-iren hotunan nan na da tasiri a kan tarbiyya da falsafar yara masu tasowa.
Hoto 6: ‘Yan Bindiga na Shirin Kai Hari
Madogara: An ɗauko wannan bidiyo ranar 2 ga watan Janairu, shekara ta 2020 daga Fesbuk.
An sanya wannan
bidiyo ne da sunan ‘yan bindigar Jahar Zamfara ne ke shirin kai hari. Sai dai
bincike ya nuna cewa, labarin ba gaskiya ba ne. Hasali ma, ba a Nijeriya aka ɗauki wannan bidiyo ba.
4.0 Sakamakon
Bincike da Shawarwari
Tun wajajen shekarar
2008 aka fara samun ƙaruwar tashe-tashen hankula a Jahar Zamfara. A lokacin
bai yi ƙamari ba, domin bai wuce faɗa tsakanin zauna-gari-banza na unguwanni da
kuma sace-sace ba. Ƙaruwar fashi da makami da satar shanu ya buɗe wani sabon
babin tashe-tashen hankulan. A wajajen shekarar 2012 zuwa 2013 ne lamarin ya yi
ƙamari sosai musamman bayan ƙaruwar garkuwa da mutane da kuma hare-hare da ‘yan
bindiga ke kai wa ƙauyuka.
A ɓangare guda kuwa, wannan bincike ya gano cewa, kafafen
sada zumunta sun kasance ruwa biyu dangane da tashe-tashen hankulan jahar
Zamfara. Kai tsaye alfanunsu sun haɗa da:
i.
Faɗakar da al’umma domin su farga tare da guje wa faɗawa cikin tashe-tashen hankulan ta kowace fuska. Wannan
ya haɗa da ɗaukar makami, ko kuma garaje da rayuwa wajen faɗawa cikin haɗarin tashe-tashen
hankulan.
ii.
Taimakawa wajen
neman tallafin addu’o’in samun zaman lafiya da ma samun tallafi nau’uka
daban-daban kamar yadda aka lissafa a ƙarƙashin 3.2 da ke sama.
iii.
Suna kuma taimakawa wajen bunƙasa adabin Hausawa
musamman abin da ya shafi waƙoƙi da karuruwan magangannu.
A ɓangare guda kuwa, kafafen na sada zumunta suna da illolin
da suka haɗa da:
i.
Ta hanyarsu ne ake yaɗa jita-jita da labaran ƙarya marasa tushe.
Wasu labaran na ƙara ruruta lamari tare da jefa ƙiyayya da gaba da rikicin addini da ƙabilanci a zukatan
al’umma.
ii.
Labarai da bidiyoyi da hotuna da ake sanyawa na sukan
kasance masu ta da hankalin al’umma. Wannan na faruwa musamman da yake ba
tacewa ake yi ba ballantana a yi tunanin waɗanda suka dace a sanya da waɗanda ba su dace ba.
Dangane da waɗannan, binciken an ba da shawarar cewa:
a.
Gwamnati ta tashi tsaye tare da fitar da wasu tsare-tsare
da dokoki na musamman da za su lura da yadda ake tafiyar da al’amuran kafafen
sada zumunta a Nijeriya. Wannan na iya kasancewa ta sigar samar da yarjejeniya
ta musamman da kamfanonin da hukumomin da ke lura da kafafen sada zumuntar. Za
a iya bin matakan rufe asusu da ma bin wasu hanyoyin hukunci na daban ga masu
yaɗa labaran ƙarya, musamman waɗanda ke ta da hankula.
b.
Malaman addini da na makarantun boko su rinƙa faɗakarwa game da illolin yaɗa labaran ƙarya da ta da hankula da kuma jefa ƙiyayya tsakanin ‘yan
ƙasa.
c.
A samu tarurrukan ƙara wa juna sani a matakai daban-daban da za a tattauna
tare da samun gudummuwar malaman ilmi da manazarta game da hanyoyi da matakan
da za a tunkari matsalar. Gwamnati a matakai daban-daban tare da haɗin guiwar makarantu (musamman jami’o’i) su jagoranci
tafiyar.
5.0 Kammalawa
Tunanin Bahaushe
na “kowane allazi da nasa amanu” na ƙunshe da ƙamshin gaskiya. Binciken nan ya ci karo da hakan yayin da
ya ci karo da amfani da kuma illolin kafafen sada zumunta yayin da yake
nazartar tasirin kafafen ga tashe-tashen hankulan jahar Zamfara. Matsayin
kafafen sada zumuntan sun
kasance hanjin
jimana, wato “akwai na ci, akwai na zubarwa.” Ya rage ga mahukunta da
gwamnatoci da sauran waɗanda abin ya shafa, da su yi wata huɓɓasa domin amfanuwa da kyawawan manufofin kafafen, tare da samar
da matakai da hanyoyin da za a zage tsirin illolinsu.
Manazarta
Bashir, L. (1991). “Bara a Ƙasar Hausa.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano.
Clement,
J. (2019). Daily active users of WhatsApp Status 2019. Retrieved on 3rd
January, 2020 from: https://www.statista.com/statistics/730306/whatsapp-status-dau/.
Jayasekara, A. H. D. (2015). Facebook users and undergraduates (Specially
reference to Selected Universities in Sri Lanka ). In the International
Journal of Scientific Research and Innovative Technology, Vol. 2, No. 5 ,
Pp. 78-85. ISSN: 2313-3759.
Karofi, D. S. (1980). “Mabarata:
Tasirinsu da Gudummawarsu a Kan Adabin Hausa.” Kundin digiri na
(nawa?) wanda aka gabatar a Sashen Nazarin
Harsuna da Al’adu, Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
Korkmaz, M., Celebi, N. & Yucel, A.
S. (2014). Practical review of the place of social networks in our daily life
and their effect on today’s youth. International Journal of Academic
Research Part B; 6(1), Pp. 250-261. DOI: 10.7813/2075-4124.2014/6-1/B.35.
Owusu-Acheaw, M. & Larson, A. G.
(2015). Use of Social Media and its Impact on Academic Performance of Tertiary
Institution Students: A Study of Students of Koforidua Polytechnic, Ghana. In Journal
of Education and Practice. Vol. 6, No. 6, 2015 ISSN 2222-1735 (Paper), ISSN
2222-288X (Online), Pp. 94-101.
Sarkin Gulbi, A. (2007). “Nazari Kan
Al’adar Bara a Ƙasar Sakwkato.” Kundin digiri na biyu wanda aka
gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Siddiqui, S. & Singh, T.
(2016).Social Media its Impact with Positive and Negative Aspects. In International
Journal of Computer Applications Technology and Research. Vol. 5, Issue 2,
Pp. 71 - 75, ISSN:- 2319–8656.
Umar, A. B. (2013). Waiwaye Adon
Tafiya: Faɗakarwa a Cikin Ƙagaggun Labaran Hausa. An cirato ranar
28 ga watan Disamba, 2019 daga: https://www.amsoshi.com/
2018/03/waiwaye-adon-tafiya-fadakarwa-cikin.html.
Kafafen Intanet da Aka
Ziyarta
https://www.statista.com/statistics/273563/number-of-facebook-employees/
Waɗanda Aka Yi Hira da Su
Suna |
Wurin Zama |
Sana’a |
Ƙiyasin Shekaru |
Almustapha, Aliyu |
Gusau |
Aikin Gwamnati |
50 - 60 |
Aminu, Ibrahim |
Gusau |
Aikin Kamfani |
40 - 50 |
Ɗandare, Sa’adatu
Umar |
Kebbi |
Sayar da
atamfofi
(Kasuwanci) |
20 - 30 |
Gobir, Yakubu
Aliyu (Ph. D) |
Sakkwato |
Koyarwa a jami’a |
50 - 60 |
Hassan, Nasiru |
Gusau |
Koyarwa a
sakandare |
40 – 50 |
Ibrahim, Aliyu |
Gusau |
Aikin Gwamnati |
50 - 60 |
Ibrahim, Faruk |
Gusau |
Kasuwancin man
fetur da gas
(Manajan gidan man fetur na Zayaz Resource) |
30 - 40 |
Maikwari, Haruna
Umar |
Gusau |
Koyarwa a
kwaleji |
30 - 40 |
Zulyadain,
Muhammad |
Kano |
Kasuwancin
tufafi da kayan kwalliya |
20 - 30 |
Rataye
Bazamfariya ta Dr. Aliyu U. Tilde
Ta’ala mun kira
ka,
Gida Naija da
Makka,
Na bene har na
bukka,
Yakini babu
shakka,
Ga komi kai iyawa.
Ka shaida mun
bara'a,
Ga duk wani mun yi
a'a,
A saɓo ba mu ɗa'a,
Muna roƙonka sa'a,
Gabanin mui cikawa.
Tsaro yau yai
gazawa,
A Hausa da
tausayawa,
A kullum ba
lafawa,
Da yaɗon ɗan kabewa,
Da sauri ba tsayawa.
A Zamfara anka
fara,
Abin sanda da
gora,
Ya ƙarfafa babu lura,
Da iska har da ƙura,
Ya kai kan Sakkwatawa.
Ƙasar Gandi da Isa,
Da ke da natso da
hirsa,
A yau an tashi
rusa,
Ginin Usumanu ƙusa,
Da Gwamna Bafarawa.
Suna nan
yammacinmu,
A Birnin Gwari
namu,
Zubairu yana
kiranmu,
Mu kai ɗauki dukkanmu,
Da sauri ba tsayawa.
Kasar Dikko ya
jawo,
Ta'adda na ta
yawo,
A ɗauke mutum a kawo,
Kuɗaɗe kan ya dawo,
Ga dangi ba ragawa.
A Daura sunka
sabka,
Magaji yana a
garka,
Da ƙarfi sunka ɗauka,
Ya sa Sarki ya
koka,
A tashi a zam kulawa.
Bare hanyar Abuja,
Farin kaya da
soja,
Da manya masu
maja,
A tsorace babu ko
ja,
A jirgi za su zowa.
Muhammadu sai ka
miƙe,
Ka ɗau ɗamara ka tamke,
Da R.P.G. da
sulke,
Ta'adda duk ka
banke,
Ka himmata ba gazawa.
Nasiha ce na ba
shi,
Da A'i uwargidan
shi,
Su ɗau kibiya da
mashi,
A kullum babu
fashi,
Ka dage gun matsawa.
Burutai kar ka
zauna,
Ka ɗauki igwa ka auna,
Ga tungar masu ɓarna,
Ka watse duk ka ƙona,
Su tuba su bar mayawa.
Sa'an nan ga Sadiƙu,
Yana ta jiran
kiranku,
Ya ɗau jirgi ya bi ku,
Ya ba ku tsaro
samanku,
Da bom ba dakatawa.
Na bi ku ina
kirari,
Ina baiti da
sauri,
Kumama babu ƙwari,
Da daji ya yi ƙauri,
Na kwanta ban ɗagawa.
Da malammai a
baya,
Tsayayyu masu
raya,
Dare duka ba
ritaya,
Da farko har
nihaya,
Ijaba sui biɗowa.
Arewa ina kiranmu,
Mu taru a dunƙulenmu,
Mu nemi tsaron ƙasarmu,
Amana har da ilmu,
Sana'a sai yabawa.
Talauci bai yi
kyau ba,
Yana kawo musiba,
Da kunci ga anoba,
Da jari babu riba,
Kasa duk tai
macewa.
Talauci in ya
zauna,
Da kafirci da ɓarna,
Suna biye ba
lumana,
Ɗabi’u duk su ƙona,
Mutunci yai ficewa.
Ƙalau muke ko husuma,
A jaki ko a Homa,
Idan an ce mu
koma,
Ka sa mu tuna da
Kalma,
Mu yi ta wajen cikawa.
Salamatun da
tsira,
Ga Annabi sa ka ƙara,
Iyaye duk ka tara,
A haula har mu
dara,
Dawaman ba gushewa.
Da tammat zan tiƙe ta,
Bazamfariya kiran
ta,
Watan azumi na yi
ta,
Da fuska biyu gare
ta,
Wajen mai bincikawa.
Dr. Aliyu U. Tilde
19 May 2019
WAƘAR KIDNAFAS
Abddulhamid M.
Sani
(Malumman Matazu)
Allah da sunanka
nake farawa,
Kai kay yi loto
kullum yake juyawa,
Kai ne ka raya
Allahu kai ka matarwa,
Ka halicci fajir sannan
kayo Mumnawa,
Zan so ku ji ni ya
al'umarmu mutane.
Kafin na fara na yo
salati farko,
Wurinsa Manzo
Shalele da aka aiko,
Duk Annabawa shi ne ya zam cikamakko,
Sannan iyalai
sahabihi nai anko,
Ban ƙin na sanya nagargaru a mutane.
Yau firgici ne ya mamaye
yankinmu,
Tsoro a kullum daɗo yake jama'armu,
An sace mata an
sace har yaranmu,
Masu kuɗinmu an sace
sarakanmu,
Abin takaicin wai
gwamnatin jama'a ne.
Cikin gidanka a zo
a ɗau maka mata,
Koko ɗiyanka a bi su har
makaranta,
Waninmu fasinja
yana kan mota,
Yau al'umarmu muna
cikin firgitta,
Halin ƙasarmu na garkuwa da mutane.
Sam baabu imani
wurin kidifawa,
In sunka sata wasu
waya suka yowa,
Kuɗi miliyya su ce
abin fansowa,
Allah tsare mu
kaidinsu mun roƙawa,
Su al'umar da ke
garkuwa da mutane.
Wasu cikinmu in
sun yi garkuwa das su,
Nau'i da nau'i
azaba suke gunsu,
Duka da yunwa su
gaggalabaita su,
Har izgilanci
kidifawa ke yi gunsu,
Sharri gare su
'yan garkuwa da mutane.
Daji su ɗaure ruwa ya ƙare kansu,
Sanyi na hunturu a
kai na wasunsu,
Can daga baya za
su kira ikhwansu,
Kuɗi a kawo koko su
hallaka su,
Wayyo ni wayyo wai gwamnatin jama'a ne!
Kare suke ci ba
babbaka yankinmu,
Abin takaici wai
shugaba kuma ɗanmu,
Mun raina himmar da ake wurin kare mu,
Wai sulhu za ai da
masu kakkashe mu!
Anya hukuma
aikinta kare mutane?
Abin takaici ne ƙwarai kui duba,
Wai a hakan ne ake
faɗin ci gaba,
Ƙalubale ne gare mu wannan babba,
Dukkan musifa yaye
mana Wahhaba,
Duk kar ka ware har garkuwa da mutane.
Ni sha'írin nan
'yar shawarata ga ta,
Wurin hukuma ni ma
gudummuwata,
Tsayin daka ku yi
don kare al'ummata,
Jami'an tsaronmu
ciki da maha'inta,
Ku sanya lura
cikinsu kun gaggane.
Bora da mowa kul
kar ku wawware su,
In kun ka gano
tabbas ku hukunta su,
Wurin hukuncin kul
kar ku bambanta su,
'Yar shawarata ƙin garkuwa da mutane.
A sa idanu sosai
ga infomansu,
Jami'an tsaro na
sirri a alkinta su,
Dama cikakka a ba su
sui aikinsu,
'Yan sanda soji a
ba su duk ƙarfinsu,
Don daƙilewar 'yan garkuwa da mutane.
Mu 'yan ƙasa kau gare mu shawarata,
Aikin alkhairi mu yi
mu nuna a yi ta,
Har addu'o'i mu
rinƙa yi gun bauta,
Kamun ƙafa na duk matsalar Allah kyauta,
Babbar musifa ta
garkuwa da mutane.
Ko ƙyas bayani in mun ji kar mu rufe ta,
Mu kai rahoto ga
jami'ai su bahasta,
In mun yi wannan
Allahu za ya tsayatta,
Allahu amsa duk
matsalar ga ta kwanta,
Babbar musifa da
ta damu dukka mutane.
Ashirin da biyu "Two thousand
eighteen" yin ta,
A shekarar da
"Musabbabi" ma nai ta,
Wata na Maris don
ba ni son in manta,
A tsakkiyar da
muke cikin firgitta,
Birni da ƙauye yin garkuwa da mutane.
Ni wanda nai ta
Abdulhamid Malumma,
Abba ga Hafsat ni
ne Uban Fatimma,
Jihar Katsina
birninmu mai alfarma,
Garin Matazu a nan
kuma nake zamma,
Allah taƙaita a daina kama Mutane.
A
LHAMDULILLAH
[1] Allah wadaran mai tado ta,
Da waɗanda suke
daɗa jawota,
Allah ka hane mu
da tashin ta...
(Abubakar Ladan
Zariya, Waƙar Haɗin Kan Afirka)
[2] Wannan ba ya nuna
cea ba za a samu wasu ƙabilu na daban
bayan Hausawa ba. Abin da kawai ake nufi shi ne, mafi rinjayen al’umma da al’adu da
cikar tarihi na garin duk na Hausa da Hausawa ne.
[3] Waɗannan sun
haɗa da wayoyin salula da kwamfutoci da ababen hawa da makamai da
makamantansu.
[4] Farfesa Aliyu
Muhammad Bunza na da wannan ra’ayi. Ya kafa hujja da cewa, duk yankin da mawaƙa da sauran masu zalaƙar harshe suka yawaita, to zai iya kasancewa tushen wannan harshe a
tarihance. Ya bayyana haka a hirar da aka yi da shi a gidan rediyon FM Zamfara,
a watan Oktoba, shekarar 2019.
[5] Wato ana ƙara tabbatar da bayanan da aka samu daga wani mutum ko
wasu mutane ta hanyar tambayar wasu mutane na daban.
[6]
A shekarar 2019, kafar intanet ɗin nan mai suna
Sitatista da ke adana bayanai dangane da kafafen intanet ya fitar da ƙididdigar ma’aikatan Facebook.
Ya bayyana cewa, a shekarar 2018, ma’aikatan sun kai
dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya da biyar (25,105).
[7] Wasu daga cikin
rubuce-rubucen sun haɗa da na Baruah, (2012) da
Korkmaz, Celebe & Yucel, (2014) da OwusuAcheaw & Larson, (2015) da
Siddiqui & Singh, (2016).
[8] Makarantun da
suka fara amfani da kafar sun haɗa da Columbia da Yale da Stanford (Clement, 2019: 2).
[9] Kamfani ne da ya
shahara wajen ayyukan fassara da tafintanci da bincike (da makamantansu) cikin
harsuna da al’adun Afirka. Don ƙarin bayani, a
duba https://www.amsoshidigitalservices.com/
[10] Shi ne ke da
kamfanin Dayn’s Collection.
[11] “Toh gaskiya yanzu kusan za
a iya cewa kafar sadarwa ta zamo wani sashi na rayuwa. Kamar yadda muka sani cewa
rayuwa yanzu ba za ta
yiwu babu ita ba.” (Zulyadain, 2019)
[12] A lokacin babu tashe-tashen
hankula da suka shafi garkuwa da mutane da salwantar rayuwa da dukiyoyi.
[13] An kira su ƙanana ne kasancewar ba sa cikin nau’ukan miyagun ayyuka
da ke ta da hankalin al’umma da jan hankalin duniya (musamman idan ba su
yawaita ba).
[14] Ya faɗi haka a
hirar da aka yi da shi ranar Alhamis, 23 ga watan Fabarairu, shekara ta 2020 a ƙofar gidansa.
[15] A hirarraki da
aka yi da su, duk sun tabbatar da wannan batu.
[16] Burtali na nufi
hanyar da ake bi da dabbobi musamman zuwa kiwo. Takan kasance marar ciyawa
saboda tattakawa da dabbobi ke yi yau da gobe.
[17][17] Ɗaya ɓangaren tushen tattalin arzikin nasu shi ne noma.
[18] Akwai albarkatun
zinari a yankunan ƙananan hukumomin
Maru da Zurmi da Maradun. An fi samun sa ƙaramar
hukumar Maru, musamman yankin Ɗansadau.
[19] Daga kimanin
shekarar 2017 zuwa 2019 an tsinci Alƙur’anai
da aka jefa a masai kimanin kashi huɗu ko sama da
haka.
[20] Daga cikin
amfanin kafafen na sada zumunta da ya lissafo akwai: (i) Samar da bayanai da
(ii) Neman addu’a daga al’umma da (iii) Neman agaji daga al’umma da kuma (iv)
Sanar da duniya abin da ake ciki wanda hakan ke sanya gwamnati ƙara mayar da hankali kan lamarin. Ya kuma bayyana rashin
alfanunsu da suka haɗa da: (i) Yaɗa labaran ƙarya da (ii) Ta
da hankalin al’umma,
[21] Za a iya samun ƙarin bayani dangane da ma’anar faɗakarwa cikin ayyukan Gusau, (2008) da Usman, (2008).
[22] Gobir, (2019) ya
labarta yadda wata ‘yar uwarsa ta so kawo ziyara tare da halartar buki daga
Adamawa zuwa Sakkwato. Yayin wannan tafiya, dole sai an wuce ta cikin jahar Zamfara.
Kasancewar ta samu bayanai game da tashe-tashen hankulan, cikin sauƙi suka yanke shawarar rashin zuwanta shi ya fi kwanciyar
hankali.
[23] An gina wannan
salon magana daga ƙoƙon bara na ainihi wanda shi ne mai bara ke miƙawa domin karɓar abin sadaka.
[24] Sarkin Gulbi,
(2007: 23) ya bayyana ma’anar bara da cewa: “... wata hanya ce ta roƙon jama’a da wasu
mutane kan bi bisa waɗansu dalilai don neman abin da suka ci ko suka sha ko
suka yi sutura ko ma suka ajiye don biyan wasu buƙatu na rayuwa.
[25] A wancan lokaci,
babban abin da ya ba ni ƙarfin guiwa tare
da karkata zuciyata wajen mayar da hankali kan wannan taimako shi ne labaran waɗannan
tashe-tashen hankula da nake karantawa a waya. Duk da a cikin mamun akwai
dattawa da suke ta’ammuli da rediyo, matasa irina na da yawa, waɗanda kuma
wayoyin hannunmu su ke matsayin rediyonmu. A intanet muke samun labaran yau da
kullum.
[26] Misali,
Government Girls Secondary School Kotorkoshi da Government Day Secondary School
Mada da sauransu.
[27] Misali,
Sakateriyar ƙaramar hukumar Tsafe
[28] Karin maganar
zamani shi ne nau’in karin maganar da ake ƙirƙira a zamanin yau. Mafiya yawancin ire-iren karuruwan
maganar suna da tsoffin karuruwan magana makamantansu.
[29] A wasu baitukan
waƙar, sha’irin ya
ba da shawara ga hukuma da sauran al’umma baki ɗaya dangane da yadda za a shawo matsalar waɗannan
tashe-tashen hankula. Yana cewa:
Ni sha'írin nan 'yar shawarata ga ta,
Wurin hukuma ni ma gudummuwata,
Tsayin daka ku yi don kare al'ummata,
Jami'an tsaronmu ciki da maha'inta,
Ku sanya lura cikinsu kun gaggane.
Bora da mowa kul kar ku wawware su,
In kun ka gano tabbas ku hukunta su,
Wurin hukuncin kul kar ku bambanta su,
'Yar shawarata ƙin
garkuwa da mutane.
A sa idanu sosai ga infomansu,
Jami'an tsaro na sirri a alkinta su,
Dama cikakka a ba su sui aikinsu,
'Yan sanda soji a ba su duk ƙarfinsu,
Don daƙilewar 'yan
garkuwa da mutane.
Mu 'yan ƙasa kau gare mu
shawarata,
Aikin alkhairi mu yi mu nuna a yi ta,
Har addu'o'i mu rinƙa yi gun
bauta,
Kamun ƙafa na duk matsalar
Allah kyauta,
Babbar musifa ta garkuwa da mutane.
Ko ƙyas bayani in mun
ji kar mu rufe ta,
Mu kai rahoto ga jami'ai su bahasta,
In mun yi wannan Allahu za ya tsayatta,
Allahu amsa duk matsalar ga ta kwanta,
Babbar musifa da ta damu dukka mutane.
[30] A nan ana nufin
waƙar da aka rera a situdiyo.
[31] An samu waɗannan
bayanai sakamakon hirarraki da aka yi da Aminu, (2019), Almustapha, (2019) da
Hassan, (2019).
[32] Babban misali a
nan shi ne, ko da ayyukan ta’addanci kafefen watsa labarai za su nuna, sukan
tabbatar da cewa sun kauce nuna wasu ɓangarororin. A
kafafen sada zumunta kuwa, akan sanya kowane irin labari ko odiyo ko bidiyo.
Sau da dama akan ci kawo da bidiyo na yadda ake yanka mutane ƙarara, ko kuma ake sassara su gunduwa-gunduwa. Akan samu
lokuta da kamfanin Fesbuk ke bayyana wasu daga cikin bidiyoyi ko hotuna da ake ɗorawa a
matsayin masu ta da hankali (violent). Wani lokaci har takan cire su. Misali,
akwai bidiyon da aka ɗora ɗauke da bayani a sama (wanda wannan bincike ba zai kawo
bayani ko bidiyon ba saboda dalilai na tsaro) inda wanda ya ɗora
bidiyon da kansa yake nuna ba kowa zai iya kallo ba “Amma fa sai mai ƙarfin zuciya.”
[33] An ɗauko shi
ranar 29 ga watan 12, shekarar 2019. https://www.facebook.com/search/photos/?q=killings%20in%20zamfara&epa=SERP_TAB
[34]An ɗauko shi
ranar 29 ga watan 12, shekarar 2019.
DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.011
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.