Ticker

Yadda Harshe Ke Sarrafa Ɗan-Adam

 This article is published by the Zamfara International Journal of Humanities.

Adamu Rabi’u Bakura
Department of Languages and Cultures, Faculty of Humanities
Federal University Gusau, Zamfara State
arbakura62@gmail.com 08064893336

Tsakure 

Ilimin walwalar harshe, wani  ɓangare ne da ya ke ɓanta da nazarin ilimin harshe, da al’ada da tsarin zamantakewa a tsakanin al’umma. Hasali ma yana bin diddigin halayyar zaman  jama’a  da  harshe  wanda  ya  danganta  da  kimiyyar zamantakewar   ɗan-Adam  musamman  halayyar  zaman   ɗan Adam da ilimin halayyar al’adunsa da kuma ilimin halayyar zaman jama’a. Don haka ne  wannan mu ƙala ta yi  ƙudurin bayyana  irin  rawar  da  harshe  kan  taka  wajen  gudanar  da rayuwar   ɗan-adam.  Da  farko  an  kawo  ma’anar  harshe  da muhimmancin sa ga  ɗan-Adam da kuma irin abubuwan da yake aiwatarwa ga al’umma, har ya sarrafa  ɗan-Adam cikin hul ɗa ko mu’amalarsa ta yau da kullum.

 

A daidai shekarar 1930 ne aka sami wasu masana biyu, Sapir da Whorf da suka bayar da muhimmiyar gudummawa da ke  ƙarfafa hujjar yadda harshe ke sarrafa  ɗan Adam tamkar yadda  ɗan Adam ke sarrafa harshen. A muhawarar da suka gabatar, sun bayar da misali da harshen Indiyawa mazauna Amurka ne, wa ɗanda aka nuna harshensu ne ya haifar da kasancewar ra’ayoyinsu game da halittun duniya suka sha bamban da na sauran jinsin da ke amfani da harshen  ƙasar Turai. Whorf ya yi da’awar cewa, ‘yan  ƙabilar Hopi Idian da ke zaune a yankin Arizona, ya sa sun fahimci halittun duniya akasin da yadda sauran  ƙabilun da ke magana da harshen Ingilishi suka fahimce su. Saboda a tsarin sigar ginin nahawun harshen ‘yan  ƙabilar Hopi an bambanta abu mai rai da maras rai. Har ma sun  ɗauka girgije (cloud) da dutsi (stone) duk abubuwa ne masu rayuwa (living thing), wanda harshensu ne ya sa suka yi amanna da haka. Yayin da tsarin sigar ginin nahawun Ingilishi bai alamta haka ba. Wannan shi ya sa  ɗan asalin harshen Ingilishi bai  ɗauki halittun duniya tamkar yadda ‘yan  ƙabilar Hopi ke kallon su ba. A  ƙarshen hasashen Whorf ya kamala da cewa, “ Mun karkasa halittu a bisa ga tsarin da harshenmu na asali ya tanadar mana (Yule, 1998:247). Wannan wata manuniya ce da ke tabbatar da yadda harshe kan sarrafa  ɗan Adam.

Ma’anar Harshe

 

Masana harshe sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar harshe. Daga cikin ra’ayoyin akwai: Crystal ( 2008 ) ya bayyana cewa, “ Harshe wani tsari ne na furici wanda  ɗan Adam yake amfani da shi don sadarwa tsakaninsa da wani  ɗan Adam  ɗin”. shi kuma Garba, (1984) cewa ya yi : “ Harshe wani tafarki ne na isar da sa ƙwanni dangane da tunani da motsin rai da bukatu, ta hanyar amfani da saututtuka ta fasalin da wata

al’umma ta  ƙayyade, wanda kuma tilas mai amfani da shi ya koya ne, ba an haife shi da fasalin ba ne”.

 

Daga wa ɗannan ma’anoni za a iya fahimtar ma’anar harshe da cewa: Wani tsari ne na sauti da  ɗan Adam ke furtawa wajen isar da sa ƙo tsakanin su, a kan wani  ƙayyadadden fasali da aka amince da shi.

 

Muhimmancin Harshe Ga  Ɗan Adam

 

Sanin kowa ne cewa, harshe ya yi ruwa da tsaki a kusan dukkan al’amurran harkokin rayuwar  ɗan Adam. Saboda irin rawar da yake takawa a al’amurran rayuwa ta yau da kullum, ya kasance mai muhimmanci fiye da kima. Misali, za a tarar cewa da harshe ne  ɗan- Adam ke sa ƙe-sa ƙensa a cikin zuciya, wannan ne ya haifar da kasancewar harshe da tunani tamkar jini ne da tsoka kuma da shi ake  ƙaddamar da tunani. Hasali ma za a tarar cewa ta amfani da harshe ne  ɗan Adam yake bi ya tuno da wani lamarin da ya faru.

 

Wani muhimmin abu kuma shi ne, za a ga cewa, da harshe ne ake  ƙaryata ko gaskata wani abu. Kuma shi ne makamin  ɗan Adam na furuci. Ta amfani da harshe ake samun fahimtar juna a tsakanin al’umma.

 

Har ila yau za a ga cewa da harshe ne ake gabatar da ra’ayoyi da shawarwarin da suka danganci ci-baya ko ci-gaban al’umma. Kuma da shi ake isar da kowane irin sa ƙo. Wa ɗannan ka ɗan ne daga cikin irin ayyukan da  ɗan Adam ke aiwatarwa da harshe.

 

Abubuwan Da Harshe ke Aiwatarwa Ga Al’umma:

 

Idan aka tsaya cikin natsuwa aka yi amfani da idon basira za a tarar cewa, ba  ɗan Adam ne ka ɗai ke sarrafa harshe ba, har shi ma harshen kansa yana sarrafa  ɗan Adam. Akwai hanyoyi da dama wa ɗanda harshe ke sarrafa  ɗan Adam, daga cikin su akwai:

 

Bambanta Mutun Da Dabba

 

Harshe ne ya bambanta mutun da dabba. Wato ya sa mutun ya kasance wata halitta ta musamman daga cikin halittun Ubangiji. Wannan ya faru ne a sakamakon magana da mutun ke yi da harshe.

 

Samar Da Sunaye

 

Babban abu na farko da harshe ya yi wa mutane baya ga fifita su da dabbobi, shi ne ya samar musu da sunaye daban-daban domin kiran abu guda a tsakanin al’ummomi. Misali a harshen Hausa muna da kalmar gya ɗa a nan gida Nijeriya inda za a tarar cewa, a wasu harsuna ba haka ake kiran ta ba. Misali: 

Kasa Al’umma  Ƙabila  Ƙabila

Harshe ne ya karkasa mutane zuwa  ƙabilu daban-daban. Za a iya tantance 

Wannan a tsakanin al’ummomin duniya masu siffa iri  ɗaya, abin da ya bambanta su shi ne harshe. Misali a tsakanin fararen fata, akwai Turawa da Jamusawa da Amurkawa da dai sauransu. Haka kuma idan muka dawo gida Nijeriya za mu tarar cewa akwai al’ummomi da dama wa ɗanda harshe ne ya bambanta su. Misali Hausawa da Fulani da Yarbawa da Ibo da Igala da Nupawa da Gwari da Idoma da Jukun da Angas da Katab da dai sauransu.

 

Bayyana Nahiyar Da Mutun Ya Fito:

 

Baya ga bambanta  ƙabila, za a tarar cewa ko da a cikin  ƙabila guda harshe ne ke bayyana  ɓangaren da mai magana ya ya fito. Misali, idan mutumin Kanada ya yi magana, da jin lafazinsa za a iya tantance cewa ai ga daga nahiyar da ya fito. Wannan yakan faru ne ta hanyar la’akari da Karin harshen mai magana. Wannan lamarin haka yake ko a tsakanin al’ummar Hausawa. Domin kuwa da zarar ka ji mutum y ace: “Bara na rubuta.” Ka san mutumin Kano ne, a daidaitacciyar Hausa cewa za a yi “ Bari in rubut.” Ko kuma ka ji an ce:” Wanda ab Bakura”. Kai da ji ka san mutumin Sakkwato ne ke magana ba ma sai ka tambaye shi ba Karin harshensa ne zai bayyana maka daga shiyar  ƙasar Hausar da ya fito.

 

Bayyana Jinsin Mai Magana:

 

Daga cikin aikin da harshe ke yi wa mutane shi ne, bayyana musu jinsin mai magana ko da kuwa ba su yi ido biyu da mai maganar ba. Da zarar sun ji sautin za su iya tantancewa da lafazin mai maganar mace ce ko namiji. Misali an tabbatar da cewa, muryar ( sautin ) namiji babba ne, yayin da na mace ya kasance mai za ƙi da kuma  ɗaukar hankalin mai sauraro. Haka kuma abu ne tabbatacce cewa harshen mata ya bambanta da na maza domin akwai wasu kalmomi ko lafuzza da mata ka ɗai suka ke ɓanta da amfani da su. Irin wa ɗannan lafuzza ne ake kira da kalmomin  ɓoye ko kuma a kira su da lafuzzan da ake sakayawa. Misali, abubuwa kamar: kunama sukan kira ta da “mai ƙari” maciji kuwa sukan ce “ yagiyar  ƙasa ko maja-ciki”da dai sauran su. Hasali ma mata sun fi ke ɓanta da Karin Magana da habaici da salon Magana. Namijin da akan ji ya yawaita amfani da irin wa ɗannan kalmomi akan  ɗauke shi tamkar  ɗan – daudu.

 

 Ƙarfafa Dan ƙon Dangantaka Da Fahimtar Juna:

 

Wani aiki da harshe ke yi wa al’umma shi ne yana  ƙarfafa dangantaka a tsakanin masu amfani da shi, ta wannan ne har za su fahimci juna. Hasali ma ta yadda jama’a kan fahimci harshen junansu ke haddasa su zama tamkar ‘yan uwan juna, har a samu wata  ƙwa ƙ ƙwarar hul ɗa mai  ƙarfi a tsakanin al’ummar.

 

Ya ɗa Al’adu Da Adana Su:

 

Wani aiki da harshe ke aiwatarwa ga al’umma shi ne ya ɗa al’adunsu da suka shafi rayuwa ta gaba  ɗaya. haka kuma da shi ne ake adana su don kada su salwanta. Wannan yana faruwa ta cikin tatsuniya da almara da hikaya da dai duk wani nau’i na adabin baka.

 

Bayyana Halayya:

 

Harshe wani abu ne da ke bayyana yanayi da halayen al’umma. Domin sau da yawa akan fahimci nagarta ko rashin nagartar mutum ta hanyar lafuzzansa.

 

Fayyace Nau’in Ilimi:

 

Wani aiki da harshe ke yi a tsakanin al’umma shi ne bayyana musu nau’in ilimin da ya yi tasiri a tsakanin al’umma. Misali, mutumin da yake da ilimin Larabci har kuma ya yi tasiri a rayuwarsa za a ji a duk lokacin da yake magana yana amfani da kalmomin larabci fiye da kima, hakan kan wakana ga mutumin da ke da ilimin Turanci ko Faransanci.

 

Siffanta Hoton Rayuwa:

 

Wani aiki da harshe ke yi wa al’umma, shi ne bayyana al’adunsu da hikimominsu da basirarsu ta fuskar siyasarsu da iliminsu da mu’amalarsu da juna. Babu wani abu da za a iya amfani da shi wurin cimma irin wannan nasara in ba da taimakon harshe ba.

 

Bayyana Rukunin Jama’a:

 

Harshe na aiwatar da wani muhimmin aiki a tsakanin al’umma, wannan aiki kuwa shi ne, ta hanyar ba da bayani game da rukunin da mai magana yake ciki. Misali, idan mai magana Basarake ne ko mai mulki, za a tarar cewa harshen da yake amfani da shi yana nuna hakan. Hasali ma lafazin zai nuna isa da mulki wato za a ji yana Magana  ɗaya bayan  ɗaya. Misali sarki ko mai mulki zai dinga amfani da lafuzzan da ke nuna yana wa ƙiltar al’umma ne. Irin wa ɗannan kalmomi sun ha ɗa da:

Kamar yadda muka tanada

Za mu bayar da tallafi.

 

Idan kuwa likita ne ko injiniya za a ji yana saka irin kalmomin da suka shafi aikin da yake gudanarwa.

 

Nuna Dangantaka:

 

Wani muhimmin aiki da harshe ke yi wa al’umma shi ne ya fayyace dangantakar da ke akwai a tsakanin al’umma. Akan gane haka ta hanyar magana. Misali, a  ƙasar Hausa da zarar mutun ya ce wa wani “ Ranka ya da ɗe”, to wannan ya nuna wanda ake gayarwa yana sama da wanda ke gaida shi. Haka idan an ji an ce “ Baba” wato wannan ya nuna wanda ake ambata mahaifi ne ko kuma a matsayin mahaifi yake. Yayin da

 

“ Kawu” ke nuna “Wa” ko “ ƙanin” mahaifiya ko wani daga cikin dagin mahaifiya a nasaba.

 

Idan muka juyo ta la’akari da wayewar kan  ɗan Adam kuma, a nan ma za a fahimci cewa, harshe ne yake sarrafa shi ta yadda za a iya bambance mutumin birni da na  ƙauye. Wato daga lafuzzan da kowane ya furta za a iya fahimtar wayewar kansa. Misali, za tarar  ɗan birni yana hautsuna harshensa da  ƙir ƙirarrun kalmomi da suka wanzu a sakamakon  ɓulluwar wani yananin rayuwar al’mma wanda ya haifar da gudanar da wata haramtacciyar safar don samun na sakawa a bakin salati. Hasali irin wa ɗannan lafuzza an  ƙir ƙire su ne don kauce wa jami’an hukuma. Yayin da mutumin  ƙauye harshensa bai gur ɓata ba. Ta fuskar girma ko  ƙan ƙanta ma, harshe yana yi wa  ɗan Adam jagoranci ko ma ya sarrafa shi, domin idan aka lura da yadda rukunin al’umma ya kasu gida biyu ( yara da manya), za a fahimci cewa kowane rukuni yana magana ne ta irin tanadin da harshe ya yi masa, misali ko da a rubuce ne, a sau ƙƙe za a iya fahimtar wa ɗannan lafuzzan na yara ne ko kuwa na manya ne.

 

Jawabin Kammalawa:

A ta ƙaice dai, wannan mu ƙala, ta yi  ƙƙarin duba irin tasirin da ke ga harshe a kan  ɗan Adam. Nazarin da aka yi ya tabbatar muna da cewa harshe shi ke sarrafa  ɗan Adam ya bambanta shi da wani, ko ma ya yi masa jagoranci wurin gudanar da duk wani lamari na rayuwar duniya. Yanke muna iya cewa, harshe ne ginshi ƙin da ke  ɗauke da rayuwar al’umma domin da shi ne ake sadarwa da fahimtar juna; da shi ake bambanta abubuwa; da shi ake samar da cigaban rayuwa, da dai sauransu. Wato dai rayuwar  ɗan Adam gaba ɗaya ta dogara ne ga irin rawar da harshe yake takawa wurin yi masa jagoranci.

 Manazarta:

Brosnahare, L.F. & Spencer, J.W. (1962) Language and SocietyIbadan: University Press.

Crystal, D. (2008) A Dictionary of Linguistics and PhonoticsHong Kong: Blackwell Publishing.

Garba, C.Y. (1984) Nazarin Hausa, Nelson Publishers.

Jibrin, B. (1985) “Hayayyafar Ra’ayoyi Tun Daga Nahawun Gargajiya Har Zuwa Nahawun Taciya ( Na N. Chomsky)” Kundin digiri na farko Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria.

Jimoh, S.A. (1995) Researcher Methodology in Education: An Interdisciplinary Approach, Ilorin: Intec Printers.

Jinju, M.H. (1990) Garkuwar Hausa Da Tafarkin Ci gaba, Kaduna: Fisbas Media.

Muhammad, Y. M. (2013) Ilimin Harsuna, Zariya: Kamfanin  Ɗab’I na Jami’ar Ahmadu Bello.

Newman, P. (2000) The Hausa Language An Encyclopedic Reference Grammar, New Haven &

London: Yale University Press.

Trudgill,  P.C. ( 1985) Sociolinguistic: An Introduction to Language and Society.

 Whitey, N. (1971), Language Use and Social Change, London: Oxford University Press.

Yakasai, S. A. (2020) Jagoran Ilmin Walwalar Harshe, Amal Printing Press.

Yule, G. (1998) The Study of Language, Cambridge University Press.

Post a Comment

0 Comments