"Alu Magatakadda" ta Audu Stem - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

    Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

    Jagora: Alu magatakadda,

                Difiti gwamna,

                Ɗan Baraden Wamakko.

    Yara: Alu Magatakadda,

                Difiti gwamna,

                Ɗan Baraden Wamakko.

     

    Jagora: Alu magatakadda,

                Difiti gwamna,

                Ɗan Baraden Wamakko.

    Yara: Alu Magatakadda,

                Difiti gwamna,

                Ɗan Baraden Wamakko.

     

    Jagora: Ya Allah Ubangiji Allah,

                Taimako Ali ɗan Barade,

                Mai raba ƙarya da gaskiya,

                Gwarzon Arziki,

                Maigidansu Murja dattijo.

    Yara: (Amshi)

     

    Ya Allah Ubangiji Allah,

                Taimako Ali ɗan Barade,

                Mai raba ƙarya da gaskiya,

                Gwarzon Arziki,

                Maigidansu Murja dattijo.

    Yara: (Amshi)

     

    Jagora: Alu Magatakadda,

                Difiti gwamna

                Ɗan Barade a gaishe ka.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Baba Ubandawaki

                Kai da Muhammadu,

                Ɗan Gwaggo kun yi baƙo,

                Baba Uban dawaki,

                Kai da Muhammadu,

                Ɗan Gwaggo kun yi baƙo,

                Ina neman iso gare ku,

                A kai waƙata ga ɗan Baraden Wamakko.

     

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Ga fara’a da tausan talakawa,

                Shi ba haushi ya kai ba,

                Kowa kai yake buƙatar ya gani,

                Aljanna mai masoya.

                Ya Allan nufa ka gadi gidanku,

                Ni addu’a nikai ma,

                In dai ka kai Baraden Wamakko,

                Sitimu ina da raina,

                In sha daula.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Ga fara’a da tausan talakawa,

                Shi ba haushi ya kai ba,

                Kowa kai yake buƙatar ya gani,

                Aljanna mai masoya.

                Ya Allan nufa ka gadi gidanku,

                Ni addu’a nikai ma,

                In dai ka kai Baraden Wamakko,

                Sitimu ina da raina,

                In sha daula.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Can lokacin da babu siyasa,

                Marafa ya faɗa min,

                Kuma can lokacin da babu siyada,

                Ɗan gwaggo ya gaya min,

                Ali Magatakadda ya riƙa jamaa,

                Waɗan gari da baƙo

                Kuma duk ya riƙa mu,

                Hannu biyu mun ya gami da yara,

                In bai taimake ka ba,

                Ya bai wa ubanka ko ƙaninka,

                In da za a samu tamkarka,

                A Sakkwato da talakka,

                Ba shi gamin tasko,

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Alu Magatakadda,

                Difiti gwamna Ɗan Barade a gaishe ka.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Baba Alu mataimakin gwamna,

                Na Arziki yanzu ba irinka,

                Kuma ko da akwai kamar kai,

                A Sakkwato, Abdu ban sani ba,

                Baban Fodiyo in ko akwai wane na?

                Kwas sa ba da kai,

                Yana ram ma gwaninsa,

                Ali Ɗan Barade na Wamakko.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Kowa Allah ka wa faɗa,

                Ba shi faɗa Ali,

                Kak ka ɓata ranka,

                Duk maƙiyanka ba su kai,

                Yadda kak kai,

                Bari su yi ta hasadar ka,

                Duk yadda bunsuru yak kai da ƙahoni,

                Tozonsa bai hitowa,

                In dan sara da sassaƙa,

                Bai hana gamji yaɗuwa,

                Da toho mun shaida.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Duk yadda ba su so,

                Ka kai sai ka kai,

                Gaba dai mijin su Murja,

                Mafarauta sun yi sake da zaki,

                Ya girma sai ku sa idanu,

                To ya za su yi da kai,

                Jikan Ummar,

                Ɗan Barade Jaɓɓi na Wamakko.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Duk yadda ba su so,

                Ka kai sai ka kai,

                Gaba dai mijin su Murja,

                Mafarauta sun yi sake da zaki,

                Ya girma sai ku sa idanu,

                To ya za su yi da kai,

                Jikan Umaru,

                Ɗan Barade Jaɓɓi na Wamakko.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Ni da yaƙi a kai yawo,

                Da takobi in za a,

                Koma zaɓe da na bi ka Ali wajjen yaƙi,

                Don kai na ba da raina,

                Domin ƙoƙarin da ganin,

     Yadda kaka wa al’ummar Musulmi,

    In ba da rayuwa don kai dibiti,

    Gwamna ya yi kyau baban Hindu.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Gagari gasar mahassada,

                Jikan Umaru,

                Ɗan Barade Jaɓɓi,

                Kuma Ɗa mai kamar uba,

                Kod gani kai ab Barade,

                Jaɓɓi na Wamakko.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Gagari gasar mahassada,

                Jikan Umaru,

                Ɗan Barade Jaɓɓi,

                Kuma Ɗa mai kamar uba,

                Kod gani kai ab Barade,

                Jaɓɓi na Wamakko.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Ko can lokacin zuwan Usmanu,

                Nan Hausa ɗan Barade,

                Kakanka na cikin sadaukan Usmanu,

                Waɗanda am mayaƙa,

                Mi kaka sauna Alu gidan yaƙi kake,

                Ba ka sha ruwan gudu ba,

                Nuna mini martabag gidanku,

                Alu duk manufad da ag ga raina,

                Ka san ta.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Ni na ga kwaram,

                Ga lokacin nan kuma,

                Ba ɗaukak kwaram ni kai ba,

                Akwai magana ga zuciyata,

                Kuma kar na faɗe ta in yi laifi,

                Amma babu arashi ba ƙazahi,

                A cikinta babu zambo,

                Magana ta wadda ad da,

                Kyau masu tunani sai ku yo tunani,

                Na zo diɓar wuta maƙera,

                Ban samo ba nai masaƙa,

                Can ni same ta niw wadatu,

                In an ƙi ni nan da ɗa,

                Ga jika na ƙwarai,

                Ubangiji na ya ba ni.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Alu Magatakadda,

                Difiti gwamna,

                Ɗan Barade a gaishe ka.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora; Ali Magatakadda,

                Komi nic ce maka an riga ni cewa,

                Duh hikimar da za ni yi ta yabo,

                Wasu sun yo ta tun daɗewa,

                Amma Rabbana ka sa in samo,

                Yardak ka ni da yaranga,

                Mu huta.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Wayyo Ali ka tallabe mu hannu biyu-biyu,

                Garinga ban da mai mani bayanka,

    Yara (Amshi)

     

    Jagora; Na so Ali ka tallabe mu,

                Hannu biyu-biyu,

                Garinga ban da mai mani,

                Sai Allah.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Na Audu hanyar gona,

                Ɗan Barade Jaɓɓi,

    Yara: Ya Allah ya tsare,

                Magatakadda.

     

    Jagora: Na Audu hanyar gona,

                Ɗan Barade Jaɓɓi,

    Yara: Ya Allah ya tsare,

                Magatakadda.

     

    Jagora: Allah ya tsare na Ali baba,

    Yara: Allah ya tsare,

                Magatakadda.

     

    Jagora: Baba kai aka sauna,

                Me kake ma tsoro?

    Yara: Ya Allah ya tsare Magatakadda.

     

    Jagora: Ga ka kai difiti gwamna,

                Mijin su Murja,

    Yara: Ya Allah ya tsare Magatakadda.

     

    Jagora: Na Abdu kai mana gwamna,

                Ɗan Barade Jaɓɓi,

    Yara: Ya Allah ya tsare Magatakadda.

     

    Jagora: A yanzu ka zama sanata,

                Me kake ma tsoro?

    Yara: Ya Allah ya tsare Magatakadda.

     

    Jagora: Mai kujera ukku Ɗan Barade,

    Yara: Ya Allah ya tsare Magatakadda.

     

    Jagora: Mai kujera huɗu ɗan Barade,

    Yara: Ya Allah ya tsare Magatakadda.

     

    Jagora: Kai huɗu san huɗu Ali ɗan Barade,

    Yara: Ya Allah ya tsare Magatakadda.

     

    Jagora: Ka ƙara yin huɗu san huɗu,

                Mi ka kai ma tsoro?

    Yara: Ya Allah ya tsare Magatakadda.

     

    Jagora: Ga gwarzon gwamna,

                Sanata kuma dattijo.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Yayan Ahmed da Salihu uban Sadiya,

                Ka buwayi gasa,

                Don kai kaɗ ɗaramm wa,

                Kah hi ƙane,

                Hikimak ka mai yawa ta,

                Difiti gwamna sahibin Umam,

                Mai gona uban giji ya biyashe ka.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Babban kandami,

                A sha a yi wanka,

                Ahmad Aliyu kenan,

                Ga babban kandami,

                A sha a yi wanka,

                Na Alu Magatakadda,

                Da na ce mai magatakadda,

                Da na kira ɗan Barade Jaɓɓi,

                Shi ba jimin taɓi ya kai ba,

                Ya motsa.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Muhtari ɗan gidan maigona,

                Allah ƙara taimakak ka,

                Muhtari ɗan gidan mai gona,

                Na Alu Barade Jaɓɓi na gode.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Niy godiya ga Audu Sifaka,

                Allah ƙara taimaka tai,

                Babban kandami,

                Mu gai da sifika,

                Allah ƙara taimaka,

                Audu sifika,

    Yara (Amshi)

     

    Jaogra: Buhari na yaba na gode,

                Allah ƙara taimakak ka,

                Buhari na yaba ma firesiden,

                Na al’umma na Alu Magatakadda,

                Sarkin yaƙi za ni ce maka,

                Koko majiɗaɗi za ni ce ma?

                Kowane nik kira ka Audu,

                Na ga ya dace.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Bello Halliru na gode ma,

                Allah ƙara taimaka tai,

                Alhaji Bello ya yi man,

                Ba ƙarya ba.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Zayyanu Bello Gandhi yai,

                Ɗa ban raina taimaka ba,

                Ya ba ni.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Muhtari Mafiya mai mota,

                Ni godiya nake yi,

                Muhtari Mafiya na gode,

                Allah ya ƙara taimaka tai,

                Ya kyauta.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Yarana na yi godiya ga Itali,

                Shugaban matasa,

                Yara na yi godiya ga Itali,

                Allah ƙara taimakar ka baba Itali.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Na yi godiya Mu’azu Zabira,

                Allah ya ƙara taimaka tai,

                Mu’azu Zabira Audu ni na gode,

                Ban raina yadda yai mani ya kyauta.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Kabiru Halliru na gode,

                Ya Allah ƙara taimaka tai,

                Kabiru Hli ubana ne,

                Domin Ali ɗan Barade,

                Ya kyauta.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: ACY mu ƙara gai da Aminu,

                Allah ƙara taimakar ACY

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Yarana ni na yi godiya,

                Ga Matawalle Aminu,

                Na yaba gwamna,

                Na tan yau.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Yarana na yi godiya maitumbi,

                Abubakar yana yi mana hairan,

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Mai Lato Gumbi ni na gode,

                Allah ƙara taimakak ka,

                Mai lato Gumbi ni na gode,

                Na alu magatakadda,

                Ya kyauta.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Alu Magatakadda,

                Difiti gwamna,

                Ɗan Barade uban Hindu.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Bello Koc Bello na gode,

                Ɗan ɗan Magatakadda,

                Alhaji Bello Koc mu gai sai,

                Ya ban domin Magatakadda,

                Uban Hindu.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Alu Magatakadda,

                Difiti gwamna,

                Ɗan Barade a gaishe ka.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Jirgi mai hoto Jirgi na gode,

                Allah ƙara taimaka tai,

                Jirgi mai hoto jirgi na gode,

                Na Alu magatakadda ya kyauta.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Yarana ina Bala Yakubu,

                Na Alu Magatakadda,

                Kyaftin na yi godiya,

                Na gode Allah ƙara taimaka tai,

                Ya ba ni.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Yarana Murtala Arkilla,

                Allah ƙara taimaka tai,

                Yarana Murtala Arkilla,

                Ɗan ɗan Magatakadda,

                Ya kyauta.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora; Alhaji Lema garin Wamakko,

                Na Alun Barade Jaɓɓi,

                Alhaji Lema ɗan garin Wamakko,

                Ni godiya ni kai mai ya kyauta.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Alun Magatakadda,

                Difiti gwamna,

                Ɗan Barade a gaishe ka.

    Yara (Amshi)

     

    Jagora: Alun Magatakadda,

                Difiti gwamna,

                Ɗan Barade a gaishe ka.

    Yara (Amshi)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.