Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Jagora:
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato,
Ɗan
Barade Jikan Umaru.
Yara:
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato,
Ɗan
Barade Jikan Umaru.
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.
Jagora:
Gwamna mai faɗa da cikawa,
Yara:
Birni da ƙauye,
An ce ka yi ɗa.
Jagora:
Gwamna mai faɗa da cikawa,
Birni da ƙauye,
An ce ka yi ɗa,
Ɗan
Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ka
rai babban kada,
Uban Lamiɗo.
Yara:
Kwaj ja da kai,
Ka karya mai tsara,
Ɗan
Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ka
rai babban kada,
Uban Lamiɗo.
Yara:
Kwaj ja da kai,
Ka karya mai tsara,
Ɗan
Barade jikan Umar,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkawato.
Jagora:
Gwamnan da yah hi kowa aiki,
Yara:
Birni da ƙauce,
An ce ka ka yi ɗa.
Jagora:
Gwamnan da yah hi kowa aiki,
Yara:
Birni da ƙauce,
An ce ka ka yi ɗa.
Jaora: Don ka yi gwamna,
Ka ba she haushi.
Yara: Ka
bar su wane,
Sai korar fage.
Jaora: Don ka yi gwamna,
Ka ba she haushi.
Yara: Ka
bar su wane,
Sai korar fage.
Jagora: 2007
ka yi gwamna,
2008 ma ya yi gwamna,
2011 ta danno,
Yara: Kai
za a baiwa,
Gwamnan Sakkwato.
Jagora:
Aliyu,
Yara: Kai
za a baiwa,
Gwamnan Sakkwato,
Ɗan
Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu Gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ya
Rabbana, ya kama ma dawa,
Yara:
Rabbana ya kama ma.
Jagora:
Aliyu Rabbana ya kama ma dawa,
Yara:
Rabbana ya kama ma,
Ɗan
Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.
Jagora:
Gwamna mai faɗa da cikawa,
Yara:
Birni da ƙauye,
An ce ka yi ɗa.
Ɗan
Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.
Jagora: Da
birbiri da jemage,
Bana sun tura gar,
Biɗan wauta,
Wani na kun san shi,
Yara: Mai
Rodu ɗan
tsiya,
Mai tsintsiya,
Ɗan
Barade jikan Umaru,
Haji Aliyu gwamnan Sakkwato,
Ɗan
Barade jikan Umaru.
Jagora: Ɗan Barade jikan Umaru,
Aha Ɗan
Barade jikan Umaru.
Yara: Ya
Rabbana ya kama ma kwarai,
Ɗan
Barade jikan Umaru,
Haji Aliyu gwamnan Sakkwato.
Jagora: In
ka ga alfijir ya ɓullo,
Rana kaɗan ka ɓullo
wa ciki.
Yara: Ai
hannu ba za ya karekke ta ba,
Ɗan
Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu Sakwato.
Jagora:
Gwamna mai faɗa da cikawa,
Yara:
Birni da ƙauye an ce ka yi ɗa,
Ɗan
Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.
Jagora: In
ka ga alfijir ya ɓullo,
Rana kaɗan ka ɓullowa
ciki,
Aradu ko ta ɓullo,
Yara:
Hannu ba za ya karekke ta ba,
Ɗan
Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.
Jagora:
Gwamna mai faɗa da cikawa,
Yara:
Birni da ƙauye,
An ce ka yi ɗa.
Ɗan
Barade jikan Umar,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.
Jagora:
Toron giwa Alu uban tafiya,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora:
Gwamna Alu uban tafiya,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora:
Aliyu uban tafiya,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora: Mu
bugti tamburran gwamna,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora:
Aliyu ag gwamna,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa,
Riƙa ƙwarai gwamna,
Mai gaskiya da adalci ne,
Ɗan
Barade Wamakko,
Ali Sarkin Yamma.
Jagora:
Gwamna Aliyu yai aiki,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora:
Gwamna Aliyu yau aiki,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora:
Gwamna Aliyu ya gyara,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora:
Birni da ƙauye yai aiki,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora: Ya
saki kaya,
A ba talakkawa,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora:
wasu shaggu,
Sai su ɓoye kayansu,
Yara: Duk
saboda sarkin Yamma.
Jagora:
Shaggu da su da matansu,
Yara: Duk
saboda sarkin Yamma,
Riƙa ƙwarai gwamna,
Mai gaskiya da adalci ne,
Ɗan
Baraden Wamakko,
Ali Sarkin Yamma.
Jagora:
Allah shi maka jagora,
Yara: Ya
Wahabu.
Jagora: Ya
sa ka gama lafiya cikin mulkin,
Yara: Ya
wahhabu shi nir roƙa.
Jagora:
Gwamna Aliyu mai daraja,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora:
Gwamna Aliyu mai daraja,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora:
Sakkwato mun samu,
Gwamna mai ilimi,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai
ka iyawa.
Jagora: Mun
ɗeɓe
zamarke,
Mun ka sa gwaiba.
Yara: In
tai ɗiyanta
sai mun ƙoshi.
Jagora: Kai
munahukin Allan nan,
Da yai yi makircin,
Yara: To
fa gwamna ya rantse,
Bai barin shi,
Sai ya ɗaurai,
Riƙa ƙwarai gwamna,
Mai gaskiya da adali ne,
Ɗan
Baraden Wamakko,
Ali Sarkin Yamma.
Jagora:
Wane munahukin Allah,
Yara: Ɗan Ubayyu,
Ɗan
shi’a ne,
Riƙa ƙwarai gwamna,
Mai gaskiya da adalci ne,
Ɗan
Baraden Wamakko,
Ali sarkin Yamma.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.