Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Jagora: Ya Allah ka ba mu sa’a,
Yara:
Amin saboda Alƙur’ani,
Don Nabiyu Ama.
Jagora: Ya
Allah ka ba mu sa’a,
Yara:
Amin saboda Alƙur’ani,
Don Nabiyu Ama.
Jagora: Ya
Allah ka taimake mu,
Yara:
Amin saboda Alƙur’ani,
Don Nabiyu Ama.
Jagora: Ya
Allah shi sa mu dace,
Yara:
Amin saboda Alƙur’ani,
Don Nabiyu Ama.
Jagora: Mai
halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Yara : Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Kai
ɗauko
garkuwa da takobi,
Ka zo da bindiga.
Yara: Kan
ka zo maza su jira,
Gwamna mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkoto,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Sarkin Yamma,
Mai halin a yaba,
Yara: Ali
jarumi kake.
Jagora:
Sarkin Yamma,
Mai halin a yaba,
Yara: Ali
jarumi kake.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkoto,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Ku ɗauko
tafashe mu zo,
Yara: A
kai ku ga babbab uwa,
Sakkwato babbab uwa,
Wadda ka renon ɗiya,
Ba ta gazawa da ɗanta,
Babban birnin ta jallo,
Mai da ƙasari
zuma,
Akwai naira sakkwato,
Akwai ilmi Sakkwato,
Akwai milki Sakkwato,
Akwai yaƙi
Sakkwato,
Ko da wace kat taho,
Za ka iske sun shira,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Kai
ɗauko
garkuwa da takobi,
Ka zo da bindiga.
Yara: Kan
da duk maza su shira,
Gwamna Ali ya shira
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkoto,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Tai
ɗauko
garkuwa da takobi,
Ka zo da bindiga.
Yara: Kan
da duk maza su shira,
Gwamna Ali ya shira.
Jagora: Tai
ɗauko
garkuwa da takobi,
Ka zo da bindiga.
Yara: Kan
da duk maza su shira,
Gwamna Ali ya shira.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora: Na
ji gwamna Ali yai kira,
Ya ce “Yan adawa,
Kowa shi daina hassada.
Yara: Kai
ku zo mu raya jaha,
Yadda gwamna yaf faɗi,
Ku ɗo a raya jaha,
Yadda gwamna yaf faɗi,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Na
ji gwamna Ali yai kira,
Ya ce “Yan adawa,
Kowa shi daina hassada.
Yara: Kai
ku zo mu raya jaha,
Yadda gwamna yaf faɗi,
Ku ɗo a raya jaha,
Yadda gwamna yaf faɗi,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Na
Bello minista,
Bajinin kwamishina Kilgore,
Yara: Yau
‘yam maza su saki,
Tun da ba su I maka.
Jagora: Na
Bello minista,
Bajinin kwamishina Kilgore,
Yara: Yau
‘yam maza su saki,
Tun da ba su i maka.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Na
Bello minista,
Bajinin kwamishina Kilgore,
Yara: Yau
‘yam maza su saki,
Tun da ba su i maka.
Jagora: Ko
wa ka kama kura,
Ya caɓe ta inda yaƙ iya,
Yara: Don
yana faɗa da
kare,
Ba a tausaya mashi,
Don hakan ga mai akuya,
Sai ka ja da hattara.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora: Ko
wa ka kama kura,
Ya caɓe ta inda yaƙ iya,
Yara; Don yana faɗa da
kare,
Ba a tausaya mashi,
Don hakan ga mai akuya,
Sai ka ja da hattara.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora:
Noma a cikin ruwa,
Yara: Ko
da ya yi tsambare,
Mamman ba a gane ya yi shi.
Jagora: Mai
noma a cikin ruwa,
Yara: Ko
da ya yi tsambare,
Mamman ba a gane ya yi shi.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Masoyin Arzika Tureta,
Kwamishinan ilimi,
Yara: Yau
ko ‘yam maza su saki,
Tun da ba su i maka.
Jagora:
Masoyin Arzika Tureta,
Kwamishinan ilimi,
Yara: Yau
ko ‘yam maza su saki,
Tun da ba su i maka.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora:
Abin dik ka kai duniya,
Ka yi abin da yah hi kyau.
Yara:
Yadda duk ka kai,
Malam ba ka im ma duniya.
Jagora:
Abin dik ka kai duniya,
Ka yi abin da yah hi kyau.
Yara: Yadda
duk ka kai,
Malam ba ka im ma duniya.
Jagora: Ka
san yau da gobe,
Sai Allah,
Yara:
Maganin mutum takai.
Jagora: Ka
san yau da gobe,
Sai Allah,
Yara:
Maganin mutum takai.
Jagora: Yau
ka kwana lafiya,
Yara:
Kuma ka tashi lafiya.
Jagora: Yau
ka kwana lafiya,
Yara:
Kuma ka tashi lafiya.
Jagora:
Gobe ka kwana lafiya,
Yara:
Kuma ka tashi lafiya.
Jagora:
Jibi ka kwana lafiya,
Yara:
Kuma ka tashi lafiya,
In dai ana haka,
Sai an biɗe ka an rasa,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ha maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Je ɗauko
garkuwa da takobi,
Ka zo da bindiga,
Yara: Kan
da duk maza su shira,
Gwamna Ali ya shira.
Jagora: In
za aka ba ni mota,
Na so ka ba ni tsadadda,
Wanda za a garda.
Yara: Da
na shigo ta na hurce,
Sai a ɗora gardama,
Waɗansu su ce Sani na,
Waɗansu su ce kwamishina,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: In
za aka ba ni mota,
Na so ka ba ni tsadadda,
Wanda za a garda.
Yara: Da
na shigo ta na hurce,
Sai a ɗora gardama,
Waɗansu su ce Sani na,
Waɗansu su ce kwamishina,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Sarkin Yamma mai halin a yaba,
Yara: Ali
jarumi kake.
Jagora:
Sarkin Yamma mai halin a yaba,
Yara: Ali
jarumi kake.
Jagora:
Sarkin Yamma dangane jama’a,
Yara: Ali
jarumi kake.
Jagora:
Danganin talakawa,
Yara: Ali
jarumi kake.
Jagora:
Danganin talakawa,
Yara: Ali
jarumi kake,
Mai halin mazan jiya.
Jagora:
Akwai wata magana,
Malam ya faɗe ta
nij jiya,
Allah ka ba da mulki,
In da ya nufa duka,
Kuma shi ƙwace
mulkin nan,
In da yan nufa duka,
Don haaka Sarkin Yamma,
Allah yai maka,
Ku masu jayayya,
Duk ku daina hasada,
Ku yadda da nufin Allah,
Shi yan nufa haka.
Yara: Mai
halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali ma a ja maka.
Jagora:
Akwai wata magana,
Malam yaf faɗe ta
nij jiya,
Allah ka cire mulki nai,
Inda yan nufa duka,
Kuma shi ba da mulkin nan,
Inda yan nufa duka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Jalla yan naɗa,
Don haka mai jayayya,
Ka daina hasada.
Yara: Ka
yarda da Allah,
Shi yan nufa ya zan haka,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Ya
Allah ka ba mu sa’a,
Yara:
Amin saboda Alkur’ani,
Don Nabiyu Ahamadu,
Jagora: Ya
Allah ka ba mu sa’a,
Yara:
Amin saboda Alkur’ani,
Don Nabiyu Ahamadu,
Jagora: Ya
Allah ka taimake mu,
Yara:
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Ahamadu.
Jagora: Ya
Allah ya sa mu dace,
Yara:
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Ahamadu.
Jagora: Ya
Allah ya sa mu dace,
Yara:
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Amadu.
Jagora: Kai
ɗauko
garjuwa da takobi
Ka zo da bindiga,
Yara: Kan
da duk maza su shira,
Gwamna Ali ya shira,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora:
Ranar da zai shiga ofis,
Ya tara mutane,
Na ji yai jawabi,
Yadda nij ji gwamna ya faɗi,
Wanda yake PDP,
Da wanda yake DPP,
Ko ɗan ANPP,
Yanzu babu wani banci,
Duk mutum guda ake,
Ku zo a wa jaha aiki.
Yara: Don
ta ƙara haskaka.
Jagora: Ku
zo a wa jaha aiki,
Yara: Don
ta ƙara haskaka.
Jagora: Ku
zo a wa jaha aiki,
Yara: Don
ta ƙara haskaka.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane ko’ina suke.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Jagora:
Wannan gwamna zarumi ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Jagora: Zan
taɓo
sashen gona,
Don mu tabbata maku,
Yara:
Zamanin Alu,
Taki ya wadata mun sani,
Yanzu kan talakawa,
Sai ku tashi harƙaƙai,
Wanda ke dame hamsin,
Sai batun ɗari
ya kai,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Zan
taɓo
sashen gona,
Don mu tabbata maku,
Yara:
Zamanin Alu,
Taki ya wadata mun sani,
Yanzu kan talakawa,
Sai ku tashi harƙaƙai,
Wanda ke dame hamsin,
Sai batun ɗari
ya kai,
Jagora:
Motoci irin na noma,
Ya rarraba su ko’ina,
Yara: Don
a samu sauƙin noma,
A ko’ina jaha.
Jagora:
Motoci irin na noma,
Ya rarraba su ko’ina,
Yara: Don
a samu sauƙin noma,
A ko’ina jaha.
Mai halin mazn jiya.
Jagora:
Kuma galmuna da shanu,
Ya rarraba su ko’ina,
Yara: Don
a samu sauƙin noma,
A ko’ina jaha.
Jagora:
Kuma galmuna da shanu,
Ya rarraba su ko’ina,
Yara: Don
a samu sauƙin noma,
A ko’ina jaha.
Jagora: Ga
kuma magani na ƙwari,
Ya rarraba shi ko’ina,
Yara: Don
a samu sauƙin noma,
A ko’ina jaha.
Jagora: Ga
kuma magani na ƙwari,
Ya rarraba shi ko’ina,
Yara: Don
a samu sauƙin noma,
A ko’ina jaha.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karakara,
Da birane a ko’ina suke.
Jagora:
Wannan gwamna muumini ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora:
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali ɗan Muhammadu,
Jikan Barade bajimin,
Hajji Bello mai wuyak karo,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a a maka,
Yara:
Jikan Barde bajinin,
Haji Bello mai wuyak karo.
Jagora:
Jikan Barade,
Yara:
Bajinin Bello mai wuyak karo,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Zan
taɓo
sashen ilimi,
Don mu tabbata maku.
Yara:
Ko’ina akwai makarantu,
Da gwamna yag gina,
Ga albashi ko’ina ga maluma,
Mai halin mazan jiya.
Jagora: Zan
taɓo
sashen ilimi,
Don mu tabbata maku.
Yara:
Ko’ina akwai makarantu,
Da gwamna yag gina,
Ga albashi ko’ina ga maluma,
Mai halin mazan jiya.
Jarumi: Wannan gwamna adili
ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Jagora:
Wannan gweamna zarumi ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamma Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke,
Mai halin mazan jiya.
Jagora:
Wajjen lafiyat talakawa,
Gwamna Ali ya kula,
Yara:
Ko’ina akwai asibiti,
Wadda gwamna yash shira,
Mai halin mazanjiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora:
Wajjen lafiyat talakawa,
Gwamna Ali ya kula,
Yara:
Ko’ina akwai asibiti,
Wadda gwamna yash shira,
Jagora: Ga
magani isasshe,
Yara: Ko
yaushe ba ya ƙarewa,
Sai a koma kai maku.
Jagora: Ga
magani isasshe,
Yara: Ko
yaushe ba ya ƙarewa,
Sai a koma kai maku.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: A
sun yi ɗunguzad
dutsi,
Sun yi birkiɗad
dutsi,
Yara: Sun
ji ba su i mai,
Sai hannuwansu sun gaza.
Jagora: To
daɗa,
Yara: Sun
ji ba su i mai,
Sai hannuwansu sun gaza,
Mai halin mazan jiya.
Jagora: Ku
kun ka gadi kyautar kuɗɗi,
Da rigunan ƙawa,
Kun ka gadi kyautar mota,
Da jikkunan kuɗi,
Kun ka gadi kyautar mota,
Da dokunan hawa,
Kun ka gadi ba da kujera,
Mutum ya zo haji,
Don hakan ga,
Ga wani koke da Daudu uai maka,
Sai ka sai ma Sani motar da,
Zai shiga ba,
Mu kuma yaran Sani,
Duk ka ba mu hondodi,
Tunda ka fi ƙarfin
haka,
Kar ka barkace muna,
Ɗan
sarki jikan sarki,
Ka taimaka mana.
Yara: Mai
halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora: To
tun da ka fi ƙarfin haka,
Kar ka barkace muna,
Ɗan
sarki jikan sarki,
Ka taimaka mana.
Yara: Mai
halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Mai halin mazan jiya,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karka,
Da birane a ko’ina suke.
Jagora:
Wannan gwamna mumini ne,
Yara: Ya
raya karka,
Da birane a ko’ina suke.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora: Ƙungiyar samari ya ce a taimaka masu,
Yara:
Gwamna Alu ya rantse,
Ba a ko ‘yan daba,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka..
Jagora: Ƙungiyan matasa ya ce a taimaka masu,
Yara:
Gwamna Alu ya rantse,
Ba a ko ‘yan daba,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka..
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Jagora:
Wannan gwamna mumini na,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Tai
ɗauko
garkuwa da takobi
Ka zo da bindiga,
Yara: Kan
da duk maza su shira,
Gwamna Ali ya shira.
Jagora:
Kowa ka ka ma kura,
Ya ce caɓe ta in da yah hi so,
Yara: Don
yana faca a kare,
Ba a tausaya ma shi,
Don hakan ga mai Akuya,
Sai ka ja da hattara.
Jagora: Mai
noma cikin ruwa,
Yara: Ko
da ya yi tsambure,
Mamman ba a gane ya yi shi.
Jagora: Mai
noma cikin ruwa,
Yara: Ko
da ya yi tsumbare,
Amman ba a gane ya yi shi,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Allah shi ba mu sa’a,
Yara:
Amin Saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Ahamu.
Jagora:
Allahu ya sa mu dace,
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Ahmadu.
Jagora:
Allah ya sa mu dace,
Yara:
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Ahamadu,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Turakin Gobir Surajo Marafa Gatawa,
Na yaba mai.
Yara:
Sani ya yaba mai,
Albarkacinka yai muna.
Jagora:
Turakin Gobir Surajo Marafa Gatawa,
Na yaba mai.
Yara:
Sani ya yaba mai,
Albarkacinka yai muna.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Ibrahim Kebbe mu gaishe shi,
Yara:
Albarkacinka yai muna.
Jagora:
Ibrahim Kebbe mu gaishe shi,
Yara:
Albarkacinka yai mana,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Muktari Shehu Shagari,
Mataimaki na gwamna,
Yara:
Albarkacin ka yai mana,
Mai halin mazan jiya.
Jagora:
Muktari Shehu Shagari,
Mataimaki na gwamna,
Yara:
Albarkacin ka yai mana,
Jagora:
Muktari Shehu Shagari,
Mataimakin ka gwamna,
Yara:
Albarkacinka yai mana,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora:
Bala Ciyama,
Wanda ag garin Keɓɓe,
Yara: Albarkacinka
yai mana.
Jagora:
Bala Ciyama,
Wanda ag garin Keɓɓe,
Yara:
Albarkacinka yai mana.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Ɗanladi Cindo na gode,
Yara:
Albarkacinka yai mana.
Jagora: Ɗanladi Cindo na gode,
Yara:
Albarkacinka yai mana.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora: A Bello minista ya bai,
Yara:
Albarkacinka yai mana.
Jagora: A Bello minista ya bai,
Yara:
Albarkacinka gwamna yai mana.
Jagora: A Bello minista ya bai,
Yara: Don
ka gwamna yai mana,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Kwamishinanmu Baba Kilgori,
Yara: Don
ka gwamna yai mana.
Jagora:
Baba Jaɓɓi
Kilgori,
Yara: Don
ka gwamna yai mana,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora: Eh
Baba Jaɓɓi
Kilgori,
Yara: Don
ka gwamna yai mana,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora:
Kowa ka kama kura,
Shi ceɓeta inda yah hi so,
Yara: Don
yana faɗa da
kare,
Ba a tausaya masa,
Don hakan ga mai akuya,
Sai ka ja da hattara,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: A
zamanin Alu gwamna,
Ko’ina akwai famfo.
Yara:
Dukka gwamna yai mana,
Jagora: A
zamanin Alu gwamna,
Ko’ina akwai famfo.
Yara:
Dukka gwamna yai mana,
Mai halin mazan jiya,
Jagora:
Zamanin Alu gwamna,
Ko’ina akwai famfo.
Yara:
Dukka gwamna yai mana,
Jagora:
Ko’ina akwai famfo,
Yara: Har
inda burtali yake,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora: Eh
zamanin Alu gwamna,
Ko’ina akwai asibiti,
Yara:
Inda duk gari yake.
Jagora:
Ko’ina akwai asibiti,
Yara:
Inda duk gari yake.
Jagora:
Ko’ina akwai titi,
Yara:
Inda duk gari yake.
Jagora:
Ko’ina akwai titi,
Yara:
Inda duk gari yake.
Jagora: Eh
Sani na ga lantarki,
Yara:
Inda duk gari yake.
Jagora:
Sani na ga lantarki,
Yara:
Inda duk gari yake,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka.
Jagora:
Ko’ina akwai makarantu,
Yara: Da
gwamna yai mana.
Jagora:
Ko’ina akwai makarantu,
Yara: Da
gwamna yai mana.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Jagora:
Wannan gwamna adili ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Jagora:
Wannan gwamna Zarumi ne,
Yara: Ya
raya karkara,
Da birane a ko’ina suke.
Mai halin mazan jiya.
Jagora: In
za ka ba ni mota,
Na so ka ba ni tsadadda,
Wadda za a gardama.
Yara: Da
na shigo ta na hurce,
Sai a ɗora gardama,
Waɗansu su ce Sani,
Waɗansu su ce kwamishina,
Mai halin mazan jiya.
Jagora: Waɗansu
su ce Sani ne,
Yara: Waɗansu
su ce kwamishina,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Allah shi ba mu sa’a,
Yara:
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Amadu.
Jagora:
Allah ya taimake mu,
Yara:
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Amadu,
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato.
Jagora:
Gwamna ba a ja maka,
Yara: Mai
halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato,
Ali mai wuyak karo.
Jagora: Ya
Allah ka taimake mu,
Yara:
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Ahamadu.
Jagora: Ya
Allah ka ba mu sa’a,
Yara:
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Ahamadu.
Ya Allah ka sa mu dace,
Yara:
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Ahamadu.
Jagora: Ya
Allah ya sa mu dace,
Yara:
Amin saboda Kur’ani,
Don Nabiyu Ahamadu.
Mai halin mazan jiya,
Gwamna ba a ja maka,
Sarkin Yamman Sakkwato
Ali mai wuyak karo.
Jagora:
Kura uwak kare ta,
Yara:
Kuma inda duk kare yake.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.