"Wanda Yah Hi Gaban Tsoro" ta Sani Sabo - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

    Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

    Jagora: Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna marinjayi,

                Wamakko.

    Yara: Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna marinjayi,

                Wamakko.

     

    Jagora: Bangon Tama buwayi maƙiya,

                Koyaushe sun yi sun yi,

                Sun gaza ture ka.

    Yara: Maƙiyan Alu ku dangana,

                Ad daidai,

                Kun san Aliyu ikon Allah ne,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro.

     

    Jagora: Bangon Tama buwayi maƙiya,

                Koyaushe sun yi sun yi,

                Sun gaza ture ka.

    Yara: Maƙiyan Alu ku dangana,

                Ad daidai,

                Kun san Aliyu ikon Allah ne,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro.

     

    Jagora: Na san farin wata,

                In yah hudo,

                Hannun mutum guda,

                Bai kare shi,

                Na san rafin wata,

                In yah hudo,

                Hannun mutum guda,

                Bai kare shi.

                Maƙiya gwamna sun yi tuwon tulu,

                Har sun gama shi sun gaza kwashewa.

    Yara: Shirin da duk su kai ma Alu,

                Sun yo kuma sun yi addu’a,

                Ba ta kama ba,

                Wamakko wanda yah hi gaban tsoro.

     

    Jagora: Ashe jimilmili,

                Akwai ƙwazon nuta,

                Daga baya kihi sai kwaɗɗi,

                Na san jimilmili,

                Akwai ƙwazon nuta,

                Daga baya kama  kihi,

                Sai kwaɗɗi Wamakko.

    Yara: Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna marinjayi,

                Wamakko.

     

    Jagora: Aminu Dikko Famsin ɗan Dikko,

                Aminu Dikko Famsin ɗan Dikko,

                Aminu Dikko ni ban raina ba,

                Da yag gane ni duk ya ban kuɗɗi,

                Saboda gwamna,

                Dole mu shaida mai Wamakko,

    Yara: Wanda yah hi gaban tsoro.

     

    Jagora: Ashe Aminu Dikko Famsin,

                Ɗan Dikko,

                Aminu Dikko mata yab ba ni,

    Yara: Saboda gwamna dole mu shaida mai.

     

    Jagora: Na gode Aminu Dikko,

                Mota yab ba ni,

                Saboda gwamna,

                Dole mu shaida mai Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna marinjayi,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro.

     

    Jagora: Abubakar ɗan Uamaru na gode,

                Abubakar Ɗan Umaru na gode,

    Ɗan Lawan na Tambuwal na gode mai.

    Yara: Saboda gwamna,

                Yai muna umfani Wamakko.

     

    Jagora: Abu Ummaru Alhaji ya gode,

                Ɗan lLawan na Tambuwal,

                Na gode mai.

    Yara: Saboda gwamna,

                Yai muna umfani.

     

    Jagora: Abu Umman Alhaji ya gode,

                Ɗan Lawan Tambuwal,

                Na gode.

    Yara: Saboda gwamna yai muna umfani,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna,

                Marinjayi Wamakko.

     

    Jagora: Na san farin maciji,

                Cizo nai,

                Na san farin maciji,

                Cizo nai,

                Ai bai kashin mutum,

                In ga Gumba.

    Yara: Amma takwasara,

                In tac ciza ka,

                Ƙila sai da ƙyar,

                Kaka kai gobe.

     

    Jagora: Na san farin maciji,

                Cizo nai,

                Na san farin maciji,

                Cizo nai,

                Ai bai kashin mutum,

                In ga Gumba.

    Yara: Amma takwasara,

                In tac ciza ka,

                Ƙila sai da ƙyar,

                Kaka kai gobe Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna marinjayi,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro.

     

    Jagora: Ina zanka-zolagi,

                Sani ina Zanka-zolagi,

                Ni ban ga abin wane,

                Yar rufa ga siyasa ba,

                ‘Yan tsohuwar siyasa sun kore shi,

                Tunda sun ga ba ya da amfani,

                Don wane an faɗa muna,

                Ko matan da ag gidansu,

                Bai iya kawowa,

                To yanzu ko Aliyu ka mulkin mu,

                Ya gane ba ka so nai son ka,

    Yara: Ba don da kay yi wa ka dubara ba,

                Da ba ka koma kwancin,

                Garkal la ka ƙaƙire,

                Ka kwashi miyar sure Wamakko.

                Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna,

                Marinjayi Wamakko.

     

    Jagora: Ban koma cin tuwo da miyar bara,

                Ban sake cin tuwo da miyar bara,

                Na gane wane ba na ƙwarai na ba,

                Mulkin da yai yi ba ya da amfani,

                Ban cin mutum guda,

                Wa yaƙ ƙaru Wamakko,

    Yara: Wanda yah hi gaban tsoro.

     

    Jagora: Haji Sani ban koma,

                Cin tuwo da miyab bara,

                Ban sake cin tuwo da miyab bara,

                Na gane wane ba na ƙwarai na ba.

    Yara: Mulkin da yai yi ba ya da amfani,

                Bancin mutum guda wa yaƙ ƙaru,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna,

                Marinjayi Wamakko.

     

    Jagora: Karen gida ka bas son jan kura,

                Karen gida bas son jan kura,

                Don na sani faɗanku azajje ne,

                Ko yaushe kag gane ta kana habshi.

    Yara: To wata rana kuna haɗuwa daji,

                Ka so zuwa gida ba ka koma ba,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro.

     

    Jagora: Ashe karen gida bas son jan kura,

                Don na so ni faɗanku azajje na,

                Ko yaushe kag gane ta kana hafshi,

    Yara: To wata ran kuna haɗuwa daji,

                Ka so zuwa gida,

                Ba ka koma ba Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro.

     

    Jagora: Ashe karen gida bas son jan kura,

                Don na so ni faɗanku azajje na,

                Ko yaushe kag gane ta kana hafshi,

    Yara: To wata ran kuna haɗuwa daji,

                Ka so zuwa gida,

                Ba ka koma ba Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro.

                Magatakadda gwamna,

                Marinjayi Wamakko,

     

    Magana: Ka tuna da Umaru ɗan Ama!

     

    Jagora: Ciyaman na maroƙa,

                Sakkwato sitet,

                Haji Umaru ɗan Ama,

                Madawaki Alhaji ya kyauta,

    Yara: Saboda gwamna yai muna amfani.

     

    Jagora: Umaru Madawaki Umaru ɗan Ama,

    Yara: Saboda gwamna yai muna amfani.

     

    Jagora: Kantoma Sambo Maɗaba gode mai,

    Yara: Saboda gwamna yai muna amfani.

     

    Jagora: Kantoma Sambo Maɗaba gode mai,

    Yara: Saboda gwamna yai muna amfani,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna,

                Marinjayi Wamakko.

     

    Jagora: Alhaji komi yana da ƙarshe,

                Alhaji komi yana da farko,

                Amma ikon Ubangiji bai ƙarewa,

                Duk wanda an ka ce maka shi na,

                Wata ran ana faɗin ba shi na ba.

    Yara: Karen da duk ƙashi yak kucce mai,

                Ya faɗi yai biɗa bai gane ba,

                An bar shi nan yana lasar baki Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna,

                Marinjayi Wamakko.

     

    Jagora: Tun ran da Jallo yai yini Sani,

                Tun ran da Jallo yai yini,

                Har yau ko keke ban riƙa ta siyasa ba,

                Balle a ba ni mota ko mashin,

                Sai gwamnatin Alu mai adilci,

                Kai sai gwamnatin Alu mai adilci,

                Lokacinku na mun ka ji daɗi.

    Yara: Birni da ƙauye kowa ya ƙaru,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro Wamakko.

     

    Jagora: Kai nan na Aminu Dikko mota yab ba ni,

    Yara: Saboda gwamna dole mu shaida mai,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna,

                Marinjayi Wamakko.

     

    Jagora: A ban sake cin tuwo da miyab bara,

                Na gane wane ba na ƙwarai na ba,

    Yara: Mulkin da yai yi ba ya da amfani,

                Ban cin mutum guda wa yaƙ ƙaru,

                Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro,

                Magatakadda gwamna,

                Marinjayi Wamakko.

     

    Magana: A tuna da Alhaji Sani Daure!

     

    Jagora: Na san farin maciji cizo nai,

                Na san farin maciji cizo nai,

                Ai bai kashin mutum in ga Gumba.

    Yara: Amma takwasara in tac cije ka,

                Ƙila sai da ƙyar kaka kai gobe,

                Wanda yah hi gban tsoro,

                Magatakadda gwamna,

                Marinjayi Wamakko,

                Wanda yah hi gaban tsoro.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.