Ticker

Akwai Firgitarwa A Labarin Nan

Akwai wata Yarinya Amina, 'yar Makaranta ce, tana da mai da Hankali sosai. Wata rana a kan hanyarta ta zuwa makaranta Wani mai Babur ya bugeta  da mashin ɗinsa.

Nan ba a zarce da ita koina ba sai Asibiti don kula da lafiyarta. A wannan daren da aka kai Amina asibiti, sai ta yi mafarkin wata Tsohuwa, Tsohuwar ta ce mata  "AMINA IDAN AN SALLAME KI DAGA ASIBITIN NAN KI TABBATAR KIN WANKE JININ DA KE  KAYAN DA MAI BABUR DIN NAN YA KADÉ KI, IDAN BA HAKA BA, ZA KI SHIGA CIKIN WANI MUMMUNAN YANAYI"

Amina hankalinta ya tashi, sai kawai ta fadá ma mahaifiyarta abin da Wannan mata ta fadá mata.

Ai Kuwa sai Mahaifiyarta ta ce ba damuwa ki yi hakan, ai kuwa a wannan daren shi ma Amina ta ƙara irin wannan mafarkin, da Wannan umarnin da wannan mata ta bata. Washe gari aka sallame su daga Asibiti, sai suka dawo gida, sai Amina ta dauko Wannan kayan da mai Babur ya kade ta da su ta fara wanki, har sai da ta wanke jinin nan saura dan kadan ya rage, sai taje ta shanya kayan.

Ai kuwa cikin dare ta kwanta sai ta ƙara mafarkin wannan Tsohuwar ta ce mata 

"AMINA KI TASHI KI WANKE SAURAN JININ NAN DA YA RAGE A RIGAR NAN DA KI KA YI HADÁRI DA ITA, IDAN BA HAKA BA ZA KI GA ABIN DA ZAI FARU DA KE"

Ai kuwa hankalin Amina ya tashi, ga shi cikin kurmusun dare ne a lokacin karfe hudu na dare, ai kuwa Amina ta yi Karfin hali ta tashi, duk da tsoron da take ji sai ta ga cewa ai tsoron abin da tsohuwar nan ta faɗá zai same ta, ya fi zama Abu Mai Tsoratarwa.

A haka dai ta ci gaba da wanki cikin dare, tana gurzar rigar nan amma ta ki wankuwa, ta yi ta yi har ta gaji amma jinin ya ƙi fita daga rigar, sai ta Fara kuka saboda gajiya da Kuma tunanin bala'in da zai same ta.

Can sai ta ji an taɓà ta, tana waigowa sai taga Wannan Tsohuwar ce,

Sai Tsohuwar ta ce Amina "ga Omo VIVA ki yi Amfani da shi Wajen Wanke Wannan datti da ya tsaya a tufafin ki, saboda yana kashe kwayoyin cuta sannan Kuma baya ƙarni a tufafi." Wannan post ɗin Tallan VIVA ne 😂

Post a Comment

0 Comments