𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum mlm barka da asuba ya kokarin don Allah mlm ina da tambaya wanne irin aikin alkari mutum ya kamata ya yi a cikin watan Ramadan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh. Alhamdu
lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa
sahbihi ajma'in.
Aiyukan da ya kamata mutum ya yi a watan na Ramadan,
kuma ya basu kulawa, su ne aiyukan alkhairi da kuma nisanta da kamewa daga
aiyukan sharri. Daga cikin su akwai jaddada imani, ta yawaita zikirin laa
ilaaha illa Allahu
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم،
جددوا إيمانكم قالوا كيف نجدد إيماننا يا رسول الله؟ قال أكثروا قول لا إله إلا الله
Yawaita ambaton Allah da Ɗa'a gare Shi, sannan nisanta daga shirka, Bid'ah da saɓon Allah. Girmama iyaye, yi
masu biyayya, ihsani, lazimtar su da yawaita yi masu addu'ar gafara da rahama.
Kyautata mu'amala da bayin Allah gaba ɗaya da kuma makusanta.
Karatun alƙur'ani, hardar shi, koyon
iya karatun shi da fassarar shi. Yawaita ƙiyamul laili da sauran
nafilfili da yawaita sadaka, kyauta da yafe bashi, rabin shi ko kuma duka.
Taimakon marayu, gajiyayyu, talakawa, zawarawa, da ziyarar marasa lafiya, tare
da siya masu magani, da yan prison da basu abinci da
tufafi da yi masu nasiha.
Girman ladar sadaka na banbanta daga lokaci zuwa wani
lokaci, daga mutum zuwa wani mutum, daga yanayi zuwa yanayi. Haka Ikhlasi yana
hauhawar da ladar sadaka komin yadda abin sadakar ya zamo ƙanƙani. Babban abin lura ga mai
sadaka, ba yawa ko kaɗan ba ne na abin da zai bayar ba, a'a, Ikhlasi ya fi girma,
sai lada ta fi girma insha Allahu
(إِنَّمَا نُطۡعِمُكُمۡ لِوَجۡهِ ٱللَّهِ لَا نُرِیدُ مِنكُمۡ جَزَاۤءࣰ وَلَا شُكُورًا إِنَّا نَخَافُ مِن رَّبِّنَا یَوۡمًا عَبُوسࣰا قَمۡطَرِیرࣰا)
[Surah Al-Insan 9 - 10]
Don haka babu wata sadaka ɗaya da za a ce tafi sauran,
domin wata karuwa ta shayar da kare ruwa, kuma wannan sadakar ta sama mata
aljanna a wurin Allah.
Amma ko shakka babu duk abin da muka amba ta a sama
nau'ukan ne na sadaka, sai ka ɗauki kowane kake so kuma za
ka iya, Allah ya taimake ka. Abin lura game da sadaka, shi ne wanene ya fi bukata,
a dangin ka, sannan a wajen su? Bayan haka ana fifita sadakar da za ta amfanar
mai yin ta da wanda aka yiwa, a kan wacce kawai mai yin ta zai amfana, misali,
azumi, zikirin Allah, karatun alƙur'ani duk sadaka ne, amma
suna amfani ga mai yin su ne kaɗai, amma ciyarwa, shayarwa,
taimakon gajiyayyu, marayu, zawarawa da fursunoni, misali, suna taimakawa ɓangaren biyu ne. Allah yana
bayar da aljanna a kan hakan, Allah ya ce
(وَیُطۡعِمُونَ ٱلطَّعَامَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ مِسۡكِینࣰا وَیَتِیمࣰا وَأَسِیرًا)
[Surah Al-Insan 8]
Ga sakamakon
(فَوَقَىٰهُمُ ٱللَّهُ شَرَّ ذَ ٰلِكَ ٱلۡیَوۡمِ وَلَقَّىٰهُمۡ نَضۡرَةࣰ وَسُرُورࣰا وَجَزَىٰهُم بِمَا صَبَرُوا۟ جَنَّةࣰ وَحَرِیرࣰا مُّتَّكِـِٔینَ فِیهَا عَلَى ٱلۡأَرَاۤىِٕكِۖ لَا یَرَوۡنَ فِیهَا شَمۡسࣰا وَلَا زَمۡهَرِیرࣰا وَدَانِیَةً عَلَیۡهِمۡ ظِلَـٰلُهَا وَذُلِّلَتۡ قُطُوفُهَا تَذۡلِیلࣰا وَیُطَافُ عَلَیۡهِم بِـَٔانِیَةࣲ مِّن فِضَّةࣲ وَأَكۡوَابࣲ كَانَتۡ قَوَارِیرَا۠ قَوَارِیرَا۟ مِن فِضَّةࣲ قَدَّرُوهَا تَقۡدِیرࣰا وَیُسۡقَوۡنَ فِیهَا كَأۡسࣰا كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِیلًا عَیۡنࣰا فِیهَا تُسَمَّىٰ سَلۡسَبِیلࣰا ۞ وَیَطُوفُ عَلَیۡهِمۡ وِلۡدَ ٰنࣱ مُّخَلَّدُونَ إِذَا رَأَیۡتَهُمۡ حَسِبۡتَهُمۡ لُؤۡلُؤࣰا مَّنثُورࣰا وَإِذَا رَأَیۡتَ ثَمَّ رَأَیۡتَ نَعِیمࣰا وَمُلۡكࣰا كَبِیرًا عَـٰلِیَهُمۡ ثِیَابُ سُندُسٍ خُضۡرࣱ وَإِسۡتَبۡرَقࣱۖ وَحُلُّوۤا۟ أَسَاوِرَ مِن فِضَّةࣲ وَسَقَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡ شَرَابࣰا طَهُورًا إِنَّ هَـٰذَا كَانَ لَكُمۡ جَزَاۤءࣰ وَكَانَ سَعۡیُكُم مَّشۡكُورًا)
[Surah Al-Insan 11 - 22]
WALLAHU TA'AALA A'ALAM
Amsawa :
Malam Aliyu Abubakar Masanawa
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Eub2uLrV18T4vHJcƙRDkPZ
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.