Ba Na So Na Sha Azumi, Ko Zan Iya Shan Maganin Hana Haila?

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, Allah ya gafarta malam, azumi ya zo ni kuma ba na son na sha ko azumi ɗaya, to shi ne na sayi maganin da zai hanani yin al'ada na sha, bayan mun Haɗu da kawata, sai take ce min wai babu kyau, shi ne na ce mata ban yarda ba, zan tambayi malamai, don Allah malam a kara min haske?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaykumussalam, To 'yar'uwa amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, Idan ya zama ba zai cutar ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda faɗin Allah “kar ku jefa kawunanku a cikin halaka” suratu Albakarah aya ta 195.

    Saidai duk da cewa hakan ya halatta da sharudan da suka gabata, amma barinsa shi ya fi, sai idan bukatar hakan ta taso, saboda mutum ya zauna akan yadda yake ya fi masa kwanciyar hankali akan ya yi abin da zai canza dabi’arsa, musamman ma wasu daga cikin kwayoyin na zamani suna dagula kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana gare mu, sai a kiyaye.Don neman karin bayani, duba : Dima'uddabi'iyya shafi na : 54 .

    Allah ne mafi sani.

    Amsawa: Dr. Jamilu Zarewa

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/EPG7wVPlgxRFR4R9CdR8xY

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.