Ticker

    Loading......

Bacci Ɗan Uwan Mutuwa Ne, Yan Aljanna Ba Sa Bacci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah Allah ya kara wa mallam hirsi da taƙawa mallam. Ina buƙatan sharhin wannan hadisin ne

قال: رسول الله صلى الله عليه وسلم، "النوم أخو الموت وأهل الجنة لا ينامون"

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce "barci ɗan'uwan mutuwa ne, alhali yan aljanna ba su yin barci".

Ma'anar wannan hadisi a sarari take, sai dai ƙarin bayani a kan wannan hadisi, shi ne, hadisin na tabbatar da dangantaka mai ƙarfi tsakanin barci da mutuwa, domin maɓuɓɓagar su ɗaya, ma'ana duk mai barci gawa ne, har sai ya tashi, ma'ana matacce ne, sai dai idan ajalin shi bai zo ba, sai Allah ya maido masa da ran shi, kamar yadda ya zo a alƙur'ani, inda Allah ya ce

(ٱللَّهُ یَتَوَفَّى ٱلۡأَنفُسَ حِینَ مَوۡتِهَا وَٱلَّتِی لَمۡ تَمُتۡ فِی مَنَامِهَاۖ فَیُمۡسِكُ ٱلَّتِی قَضَىٰ عَلَیۡهَا ٱلۡمَوۡتَ وَیُرۡسِلُ ٱلۡأُخۡرَىٰۤ إِلَىٰۤ أَجَلࣲ مُّسَمًّىۚ إِنَّ فِی ذَ ٰ⁠لِكَ لَـَٔایَـٰتࣲ لِّقَوۡمࣲ یَتَفَكَّرُونَ)

[Surah Az-Zumar 42]

Ke nan daga wannan aya da hadisin, za mu fahimci cewa duk mai barci matacce ne, sai wanda Allah ya maido masa rayin sa. Toh idan haka ne, yaya yan aljanna za su yi barci? Da sun yi barci, toh sun ɗanɗana mutuwa alhali Allah ya ƙaddara masu rashin mutuwa kamar yadda ya zo a wani hadisin, za a ƙaddara ma kowanen su rayuwar da babu mutuwa, ma'ana ta har abada, bayan an zo da mutuwa an yanka ta gaban idon yan wuta da yan aljanna sai a ce da yan aljanna ku dauwama babu mutuwa, haka kuma za a ce da yan wuta.

فإذا أدخل الله أهل الجنة الجنة وأهل النار النار أتي بالموت ملببا فيوقف على السور الذي بين أهل الجنة وأهل النار ثم يقال: يا أهل الجنة! فيطلعون خائفين ثم يقال: يا أهل النار! فيطلعون مستبشرين يرجون الشفاعة فيقال لأهل الجنة وأهل النار: هل تعرفون هذا؟ فيقول هؤلاء وهؤلاء: قد عرفناه هو الموت الذي وكل بنا فيضجع فيذبح ذبحا على السور ثم يقال: يا أهل الجنة! خلود لا موت ويا أهل النار! خلود لا موت".

(صحيح) [ت] عن أبي هريرة. شرح الطحاوية 576.

 

Don haka babu barci a aljanna, tun da shi ɗan'uwan mutuwa ne, sai shagali kawai, babu tsufa, babu gajiya, babu baƙin ciki, ɓacin rai ko takaici, babu tsananin zafi ko tsananin sanyi, babu yunwa ko ƙishi, babu kashi ko fitsari, kuma za a ci za a sha kayan daɗi, babu al'ada, majina, maziyyi ko duk wani nau'in ƙazanta.

Amma wani zai iya cewa, me za ka ce da wannan ayar da alƙur'ani ya ce yan aljanna za su yi ƙailula?

(أَصۡحَـٰبُ ٱلۡجَنَّةِ یَوۡمَىِٕذٍ خَیۡرࣱ مُّسۡتَقَرࣰّا وَأَحۡسَنُ مَقِیلࣰا)

[Surah Al-Furƙan 24]

Sai mu ce da shi, ƙailula a yaren larabci, ba ta nufin dole yin barci da rana, kamar yadda kalmar baituta, ba ta lazimta yin barci da dare. A'a, abin da ƙailula ke nufi shi ne ko da zama ka yi na ba tare da ka yi wani kai komo ba, ana kiran shi da suna ƙailula, hutawa ka yi ko barci ko kuma sararawa ka yi, duk ana kiran shi da sunan haka.

Wallahu ta'aala a'lam.

Amsawa:

Malam Aliyu Abubakar Masanawa

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments