Ticker

6/recent/ticker-posts

Bafulatani Da Farfesa

 Wani farfesa ya rena hankalin wani Bafulatani. Profesa ya ce idan na yi maka tambaya ba ka amsa ba za ka ba ni 5000. Idan kuma ka yi min tambaya ban sani ba zan ba ka 20000. Professor ya tambayi Bafulatani "nawa ne nisan sama zuwa ƙasa?" Bafulatani ya ce bai sani ba.

Bafulatani ya ba da 5000. 

Bafulatani yace saura ni."Wace dabba ce idan tana kasa tana da kafa 4 idan ta soma tashi tana da kafa 3 idan tayi sama sai ta koma kafa 2 idan ta tashi saukowa sai ta sauko da kafa 1?"

Profesa ya zaro 20000 ya bayar dan bai sani ba. Bafulatani zai tafi sai profesa ya ce

"mene ne ansar?". Sai Bafulatani ya zaro

5000 ya kara wa profesa ya ce: "Ni ma ban sani ba."

Bafulatani Da Farfesa


Post a Comment

0 Comments