Ticker

6/recent/ticker-posts

Haramun Ne Ɗanka Wanda Ka Same Shi Ta Hanyar Zina Ya Auri 'Yarka Wadda Ka Same Ta Ta Hanyar Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Da gaske ne wai idan mutum yana da ɗa (ɗan shige) sai daga baya ya zo ya yi aure ya haifi yarinya. Toh wai akwai aure a tsakanin su, Yaron da yarinyan?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Toh a kan wannan matsalar babu shakka akwai saɓanin malamai, amma jamhur na malamai sun tafi a kan cewa Haramunne Ɗanka na wanda ka same shi ta hanyar zina ya auri 'yarka wadda ka same ta ta hanyar aure Mafi yawan Malamai sun ce yin hakan haramunne kuma wannan shi ne abun da Shekhul Islam ya faɗa a cikin fatawarsa. Amma akwai wasu malamai da suke ganin ze iya aurenta Kamar Imamush Shaukani a cikin Nailul Audar can cikin Babin Alwaladu lil firash shi ma yadan goyi bayan wannan ra'ayin. Hakama akwai wata fatawarda ake jinginawa Shafi'i a kan halascin haka din. Amma dai mafi ingancin magana shi ne maganar malamanda suka ce be halasta ba ɗin domin akwai haramci na alfarma kamar yadda su malaman suka fada.

Allah ya sa mu dace

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments