Hukunce-Hukuncen Idda Da Takaba

    IDDA: Ita ce lokacin da musulunci ya sanya bayan rabuwa tsakanin mata da miji, saboda saki ko mutuwa ko abu mai kama da su, wadda ya zama dole mace ta yi shi kafin ta sake aure.

    HUKUNCIN TA

    Iddah dole ce a kan mace a lokacin da aka samu sababin ta, saki ko mutuwa ko abu mai kama da su.

    IRE-IREN IDDA

    1• Iddar wacce aka saka ko mijin ta ya rasu kafin ya sadu da ita.

     Idan sakinta yayi kafin ya sadu da ita, babu idda akanta.

     Idan mutuwa yayi kafin ya sadu da ita, zatayi idda wata huÉ—u da kwana goma.

    2• Iddar wacce aka saka bayan an sadu da ita.

     Idan har tana yin jini, iddar ta ita ce jini uku, jinin haila kenan.

     Idan ba ta jini saboda yawan shekaru ko Æ™arancin su (tsufa ko yarin ta), iddarta ita ce wata uku.

    * Iddar wacce mijinta ya rasu, idan ba ta da ciki iddarta ita ce wata huÉ—u da kwana goma.

     Idan tana da ciki kuma iddar ta tana Æ™arewa ne a lokacin da ta haihu, koda kuwa bayan ya mutu da kwanaki ne, ko banbancin wasu mintuna.

     Misali da zai mutum da safe sai ita kuma ta haihu da rana, to haihuwarta ta fitar da ita daga iddah.

    * Iddar wacce jinin hailar ta ya daina zuwa.

    Idan aka saki mace sannan sai jinin hailar ta ya daina zuwa ba tare da ta san dalili ba, to iddarta ita ce shekara É—aya.

     Amma banda wacce ta yi planning kamar tasa roba ko Allura ko wani abu, ana magane ne a kan wscce hailarta ta É—auke haka kaeai batadsn dalili ba.

    TAMBAYOYI DA AMSOSHIN SU

    TAMBAYA:

     Mace ce mijinta ya sake ta sakin kome É—aya ko biyu, sai ya rasu tana cikin idda ya zatayi?

    AMSA:

    Za ta bar yin iddar saki, ta yi iddar mutuwa wata huÉ—u da kwana goma, daga lokacin da ya rasu, kamar yadda za ta ci gadon sa, saboda ya mutu tana matsayin matarsa.

    ALLAH shi ne mafi sani.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki É—ayanmu Ameen.

    ************************************** 

    Wannan É—aya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Æ˜ur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waÉ—anda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta Æ™arin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.