Hukuncin Auren Ɗan Ball

    Malamai sun kasa ƙwallo gıda uku:

    1• Ƙwallon da ake yi saboda motsa jiki, kamar mutum biyusu haɗu, su yi ball don su tsinka jinin jikinsu, wannan ta hallata mutuƙar ba ta kautar da masu yinta daga ambatonALLAH ba, ko kuma ta hana su yin sallah idan lokacinta ya shiga ba, kuma ba a bayyana tsiraici a cikitaba.

    2• Ƙwallon da ƙungiyoyi biyu ko sama da haka za su haɗa kudi su sayı kofi wanda a ƙarshe ƙungiya ɗaya za ta ɗauka, wannan kam bai halatta ba,

     Saboda daidai yakeda caca, kuma yana sabbaba gaba da ƙiyayya a tsakanin 'yan ƙwallo.

    3• Idan ya zama wanine daban zai sanya Kofin, shimamalamai sun ce haramun ne saboda asali musabaƙa dawasan tsere haramun ne, in ba abin da dalili na shari'aya halatta ba, irin wannan ƙwallon kuma ba ta cikin abin da aka shar'anta.

     

     Sannan akwai ɓarna mai yawa a cikinta, domin zai yi wuya a tashi irin wannan ƙwallon wani bai ji ciwo ko ya karye ba, ga kuma haushi daƙulewa da yake samun wanda aka kayar, wasu lokutanhar da doke-doke tsakanin ƙungiyoyin guda biyu.

     Idan ya zama mijin da za ki aura yana yın nau'i na biyu kona uku, to ya wajaba kiyi masa nasiha idan kuma yaƙiji, to auransa akwai hadari saboda zai ciyar da ke da haramun.

     Don neman ƙarin bayani duba Fatawa Al-lajna Adda'imah 3/238.

     Ko kuma Fatawa Muhammadbn Ibrahim 8/116.

    ALLAH shi ne mafi sani.

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.