Hukuncin Canza Wuri Bayan Sallar Farilla Kafin Sallar Nafila

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne asali ko dalili idan mutum ya idar da salla zai yi nafila sai naga ya ɗan matsa baya ko gaba daga inda ya yi sallarsa, akwai hadisi ne a kan haka?

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    To dan'uwa Akwai hadisin da yake nuna haka, sai dai wasu malaman hadisin sun raunana shi kamar Bukhari a sahihinsa, a hadisi mai lamba: 848, amma Albani ya inganta shi saboda yawan hanyoyin sa, a cikin littafin Sahihu sunani abi-dawud 3\178

    Sai dai malamai suna cewa : ana so a yi hakan saboda gurare da yawa su yi ma mutum shaida,

    Amma abin da ya fi ga liman shi ne canza wuri, saboda abin da aka rawaito daga Aliyu - Allah ya kara masa yarda- yana cewa : "Yana daga cikin sunna, liman ya canza wuri idan zai yi sallar nafila" wannan ya sa Imamu Ahmad ya karhantawa liman ya yi nafila a inda ya yi sallar farilla, don kar a zaci sallar ba ta kare ba . Fathul-bary 2\335

    ALLAH NE MAFI SANI

    Dr Jamilu Zarewa

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/CFp8AF5lYJt7v6HZ3i6mjf

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.