Hukuncin Gina Toilet Ta Fuskanci Al-Ƙibla

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam mutunne yagina sabon gida saida akagama aikin komai sai yalura ansa toilet yana kallon gabas sai ya ce acire ajuya a musulunce babu kyau Asa gado ko toilet suna kallon gabas dan Allah malam mene ne hukuncin haka na gode

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Wa'alaykumussalam.

    Hadisi ya inganta daga Abu ayubal Ansari a cikin Bukhari da Muslim cewa manzon Allah ya hana a kalli alƙibla ko a ba ta baya wajen biyan bukata...

    Amma jamhurun malamai cikin su akwai Imam malik, Shafi'i da Ahmad Bin Hambal sun ce wannan hanin ya shafi wanda zai biya bukatar sa ne a fili inda babu wani shamaki tsakanin sa da alƙibla, amma idan akwai shamaki ko cikin irin bayukan mu toh babu komai...

    Sauran Malaman kamar su Imam Abu hanifah sun ce hanin ya shafi fili da kuma cikin bayi, wannan shi ne ra'ayin shehul Islam Ibn Taymiyya, (Aduba Al'Mugny 1\107)..

    An tambayi malaman Lajna sun ba da fatawar babu laifi idan har akwai shamaki wato wani gini ko makamancin sa aduba Fatawa lajna 5\97.

    Don haka idan har ka riga ka gina bayin toh babu komai a kan ka ba sai ka rusa ba, in kuma kafin ka gina ne to za ka iya gyara tsarin ta yadda za ka kaucewa kallon ka'aba don gujewa duk wata shubuha.

    Amma tun da kace ka gyara shi ke nan muna fatar Allah ya baka ladar nesantar hanin manzon Allah .

     

    Zancen saka gado ya kalli gabas ban san wani dalili daya hana haka ba, abin da na sani shi ne a kwanta a gefen dama kafin a yi bacci a kuma kaucewa kifa ciki.

    WALLAHU A'ALAM.

    Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.