Hukuncin Kwana Da Ƙawayen Amarya Suke Yi A Ranar Da Aka Ɗaura Mata Aure

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuhu, Sabahul Khair, Ina tambaya, mene ne hukuncin kwana da ƙawayen amarya suke yi a ranar da aka ɗaura mata Aure a addinin Musulunci.

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Waalaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

    "Kowace al'umma akwai irin nata al'adun waɗanda suke ta'ammuli dasu, wasu sun saɓawa addinin Musulunci wasu kuma ba su saɓa ba"

    "Al'adun da suka saɓawa shari'ar addinin musulunci, to haƙiƙa haramun ne yin aiki dasu, waɗanda kuma basuci karo kuma sun saɓawa musuluncin ba, to lallai wannan ba haramun ba ne matuƙar akwai maslahar yin hakan"

    "A batun aure akwai wasu abubuwa da dama da ake aikatawa, wasu haramun ne, wasu kuma ba haramun ba ne al'ada ce kawai ta mutanen yanki kaza"

    "Kwana da ƙawayen amarya a ranar aurenta indai haka al'adar garin take, to wannan inshaa Allahu babu wata matsala, tun da daman ai shi kansa mijin yasan da irin wannan batun al'adar, kun ga ai ba zai ce an yi masa ba-zata ba, idan kuwa babu wannan al'adar a garin, to haƙiƙa aikata hakan babu kyau, domin kuwa ai za su iya tauyewa mijin haƙƙinsa na mararin son ganin amaryarsa"

    "Batu dai wanda ya fi daidai shi ne ranar auren mace ko yar ƙaramar yarinya bai dace a ce ta je su kwana tare ba balle kuma wasu ƙawayenta, domin hakan baya daga cikin aikin magaba ta na ƙwarai"

    WALLAHU A'ALAM.

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BD0aB20SWTB9hgHahFHb9M

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.