𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum warahmatullah..Malam mene hukuncin saka eyelashes da 'yan mata suke yi ko amare a lokacin biki in an gama biki su cire, wasu sukan cire a ranar wasu kuma suna barin sa ya yi kwanaki, ya hukuncin alwala, saboda da gum ake sa shi kuma ina kyautata zaton ruwa ba ya taba wurin, shin sanyawar kansa ba matsala, ko kuma idan za a cire lokacin da za'ayi alwala za a iya sakawa? Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa'alaikumus Salámu Wa Rahmatullahi Wa Barakátuhu.
Ga 'yan uwana maza da ba su san ko mene ne eyelashes
ba shi ne ƙirƙirarren gashin ido da mata suke ƙarawa a lokacin bukukuwa da manufar nuna ado.
Kafin in ba da amsar tambayar nan, na tuntuɓi mata a Zaurukan Saƙon Annabta sashen mata zalla da kuma wajen zauren a game da
matsayin eyelashes, shin ruwan alwala yana tsuma gam (gum) ɗin da ake manne gashin da
shi har ya kai ga fatar ido ko ba ya tsuma shi? Mafi yawan su sun tabbatar min
da cewa ruwa ba ya ratsa gam ɗin da ake amfani da shi har
ya iske fatar ido, ga biyu daga cikin amsoshin da suka ba ni:
"Assalamu alaikum malam barka da ƙoƙari. A gaskiya ruwa ba ya taɓa fatar matar da ta sa
eyelashes. Kuma shi ma tamkar canza halittar Allah ne, don da zarar an sanya
shi sai mace ta canja. Wallahu A'alam."
"Assalamu Alaikum, malam barka da warhaka, to a
gaskiya ruwa ba zai taɓa ratsa wurin da aka Sanya Shi ba. Saboda gum ne ake
Sanya shi a jikin gashin idon da za a kara, to ka ga duk inda aka manna to fa
zai lulluɓe wurin ne, ka ga ruwa ba zai ratsa shi ba, duba da
idan ka zuba gum a wurin idan ka zuba ruwa a wurin ba zai ratsa gum din ya
sauka karkashin sa ba, ka ga faruwar haka zai haifar da lam'a a cikin alwala,
Allah ya kara wa malam lafiya."
A bisa lura da amsoshin nan nasu, duk da cewa akwai masu
amsa akasin nasu, sai ya zama bai halasta mace ta yi alwala da eyelashes har ta
yi sallah da shi idan har ya tabbata da gaske ruwa ba ya tsuma gam ɗin da ake manne shi da shi
har ya kai ga fatar ido ba, saboda in hakan ya tabbata, to zai sa a sami lum'a
a fatar ido a lokacin alwala.
Idan aka faɗaɗa ma'anar hadisin haramcin ƙarin gashi, to za a iya cewa la'anar da Manzon Allah ﷺ ya yi a kan mai ƙarin gashi da wadda ta nemi a ƙara mata a hadisin Muslim
(2122), wannan la'ana ta haɗa da har mai ƙara gashi a ido, wato eyelashes, saboda duk cikin su ƙarin gashi ne a bisa gashin asali.
Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CFp8AF5lYJt7v6HZ3i6mjf
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.