Hukuncin Shiga Bayi Da Wayar Dake Ɗauke Da Alkur'ani

     Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

    Mene ne hukuncin shiga bayi da na’ura ko wayar da ke ɗauke da Al-Kur’ani?

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    وعليكم السلام ورحمه الله وبركاته

    Matsalar shiga bayi da na’ura ko wayar da ke ɗauke da Al-Kur’ani ta kasu gida biyu:

    1 – Makaruhi ne a shiga da wayar ko na’urar da ke dauke da Al-Kur’ani idan gilashin na’urar/wayar na buɗe da Al-Kur’anin kuma ana ganinsa a

    gilashin (screen).

     

    Malamai sunce yin hakan kamar shiga da Al-Kur’ani ne bayi. Kuma haka ya saɓawa shari’ah, hasilima wasu malam sun haramta kai tsaye, domin rashin dacewarsa.

     

    2 – Kauli na biyu shi ne halacci (Halal) idan gilashin wayar baya nuna (displaying the text of Ƙur’an) ayoyin Al-Kur’ani a fili. Ko kuma wayar na kashe (swich off), ko ta yi lumm da duhu ba a ganin komai na Al-Kur’ani a gilashinta. To, idan gilashin wayar bai nuna Al-Kur’ani ba, babu komai.

     

    Sharadi ne sai mai tsarki zai ɗauki Al-Kur’ani, to shin tsarki sharadi ne game da Al-Kur’anin na’ura (kamar waya)?

    Mafi yawan malamai na ganin cewa bai dace musulmi ya buɗe Al-Kur’anin wayarsa ba sai yanada tsarki (ma’ana babu haila ko janaba), domin hakan kamar daukar Al-Kur’ani ne cikkake. Amma wasu malamai suna ganin babu komai matukar mutum ba zai taɓa gilashin (screen) da ke nuna rubutun ba.

     

    WALLAHU A'ALAM

     

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/EPG7wVPlgxRFR4R9CdR8xY

     

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.