𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam tambayata ita ce: mene ne hukuncin Wanda ya sha Azumi da gangan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikum Salaam:- Karya Azumi da Gangan Haramun Ne, Kuma Yana Daga Cikin Manya-Manyan Laifuka a Wajen Allahu Subhanahu Wata'ala. Don Haka Duk Wanda Ya Karya Azumin Na Rana Ɗaya tak ba tare da Wani Uzuri Mai Karfi Wanda Shari'ar Musulunci Ya Yarda Da shi ba, Kuma bai Tuba ba, toh Babu Abin da Wannan Mutumin Zai Yi Ya isar Masa da Azumin Sa, Koda Kuwa ya yi Azumin Zamani Guda Gabaɗayanta toh bai Taɓa isar masa da Wannan Azumin guda ɗaya Tak da Ya Karya Shi da Gangan Nan.
Saboda Faɗin Annabi Muhammad Mai Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, (( Duk Wanda Ya Karya Azumi Rana ɗaya daga Cikin Ramadan, Ba a AKan Wani Rangwame da Allah ya yi Masa ba, toh Azumin Zamani gabaɗaya ba Zai iya Rama Masa Wannan Azumin nasa guda Ɗayan Nan ba. Duba Cikin Dawud))
Mutum ya yi Asara Babba Wallahi, Azabar🔥 Allah Ya Tabbata ga Wanda Ya Karya Azumin sa da Gangan, Azaba mai Girma. An Karɓo Hadisi Daga Abu Umaimata Al-Bahili Allah Ya Kara Yarda Gare Shi, ya ce Na Ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam Yana Cewa, Ina Cikin Barci, Sai Wasu Mutane Ɓiyu Suka Zo Min, Sannan Suka Tafi da Ni, Sai Kawai Na ga Wasu Mutane An Rataye Su ta AgararSu, Muqamuqansu a Tsatsassage, Jini Yana ta Ƙwarara. Sai Ya Ce, Na Ce Shin Su Wanene Waɗannan?Sai Ya Ce, Waɗannan Waɗanda Suke Karya Azumin Su ne Tun Gabanin Lokacin Shan Ruwa Yayi)) Duba Cikin (Ibn Hibban)
Muna Kira Zuwa ga Matasa da Yan Mata Wallahi Ku ji Tsoron Allah Ku Sani Cewa Mutuwa zata Zo mu Ku a Lokacin da Ba ku Shirya mata Zuwa ba. Wallahi Kada Budurcin Ki, Balagar ki Kuruciyar ki, Ya Kai ki ga Saɓawa Allah Wanda za a Miki Azaba Mai Raɗaɗi a Ranan Alkiyama Musamman na Qin yin Azumin Watan Ramadan.
Abin Mamaki ne wai Ana yin Azumi Ana Neman Gafaran
Allah, Amma Wasu Yan Matan Biyawa Kansu Bukata
Suke yi gurin Kallon Alfasha Tsiraicin Arna, har Sai ta Fitar da Maniyyi ko
Maziyyi da Ranan Allah Kuma Ana Azumi. Haka nan Maza Samari Wani Budurwa Yake Ɗaukowa Yana Zina da Ita da Rana a Cikin Watan Azumi Kuma
Dukkan Su Musulmai ne😭 Inna illahi Wa'inna illahin
Rajee'um Subhanallah.
Wanne Irin Masifa ce Wannan?Wanne Irin Bala'i Ce Wannan?Ke Kina Son Biyawa Kanki Bukata Mene ne Zai Hanaki Yin Aure Koda Babu Kayan Lefe da Sauran su?Kin Sa Buri a Ranki Samari Sun Ki Zuwa Ga Sha'awa na Tayar ki Kin ga Gara Bin Umurnin Allah da Manzon Allah ﷺ Kin qi Yin Aure Yaya Ba Za ki Rika Saɓawa Allah ba?Daga Karshe Allah ya ɗauki Ranki ba ki Shiryawa Mutuwa me Za ki gayawa Ubangijin ki😭? Wallahi Ku Ji Tsoron Allah Yan Mata da Samari har da Matan Aure Masu Irin Waɗannan Ayyukan, Ba Zaku Taɓa Tsira a Gaban Allah ba a Ranan Alkiyama😭. Allah Ya Tsare ya Shirya.
WALLAHU A'ALAM.
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Fadakarwaa Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.