Ticker

Littafin Azumi [ 04 ] – Rukunnan Azumi

RUKUNAN AZUMI

Rukunan Azumi guda biyu ne:

1• Niyya:

Rukuni na farko Azumi baya yiwuwa idan babu niyya.

Dukkanin ayyuka ba sa yiwuwa sai da niyya.

[Bukhari da Muslim].

2• Kamewa ga barin ci da sha.

Rukuni na biyu daga cikin rukunan Azumi shi ne kamewa ga barin duk wani abinci ko abin sha ko jima’i.

 ALLAH TA'ALAH ya ce:

Ku ci ku sha har izuwa ku bambance tsakanin farin zare da baƙin zare daga hasken alfijir, sannan ku cika Azumi izuwa dare.

[Suratul Baƙara: ayata:187].

 SUNNONIN AZUMI DA LADUBBANSA

Azumi yana da sunnoni da mustahabbai, su ne kamar haka:

1• Sahur: Shi mustahabi ne a gamuwar malamai, wanda baiyi shi ba, ba shida laifi, sai dai wanda ya yi sahur ya fishi yawan lada.

 Domin Annabi {s.a.w} ya yi umarni da a yi Sahur.

 Daga Anas Ɗan Malik (R.A) ya ce:

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

 ku yi sahur haƙiƙa, akwai albarka a cikin yin sahur.

 [Bukhari da Muslim].

2• Gaggauta yin buɗa baki da jinkirta sahur,

Saboda faɗin Annabi {s.a.w} ya ce:

Mutane ba za su gushe suna cikin alkhairi ba, muddin suna gaggauta buɗa baki kuma suna jinkirta sahur.

 [Bukhari da Muslim].

3• Yin buɗa baki da dabino:

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

Idan ɗayanku zai yi buɗa baki ya yi buɗa baki da dabino, idan bai samu dabino ba, ya yi da ruwa, don tsarki ne ko tsarkakakke ne.

[Abu Dawud da Tirmizi].

4• Addu’a ya yin buɗa baki:

عَنْ عَبْدِ اللهِ ابْنِ عُمَرُو بْنِ الْعَاص: أَنَّ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "إِنَّ لِلصَّائِمِ عِنْدَ فِطْرِهِ دَعَوَةٌ مَا تُرَد." (رواه ابن ماجه).

 Abdullahi Ɗan Amru Ɗan As (R.A) ya ce:

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

Haƙiƙa, mai Azumi idan ya yi addua lokacin buɗa baki ba a mayar da addu’arsa (ana amsawa).

[ Ibn Majah ne ya rawaito]

Annabi {s.a.w} ya kasance idan zai yi buɗa baki yana cewa:

Ya UBANGIJI dominka mukayi Azumi, kuma da arzikinka muke buɗa baki, ka karɓa daga garemu, lallai kai mai jine masani.

[Abu Dawuda ne ya rawaito].

 Dama wasu addu'o'in da dama.

5• Asuwaki: Anso ga mai Azumi ya yi asuwaki lokacin azuminsa.

Saboda Manzon ALLAH {s.a.w} ya kasance yana yin asuwaki lokacin da yake Azumi.

Haka nan yana daga ladubban Azumi a nisanci shaidar zur, ƙarya, giba, rad'ɗa, rigingimu, da dai sauran ayyukan saɓo.

ALLAH shi ne mafi sani.

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments