Mace ce aka yi mata aiki (operation) a wuya, sai likita ya hana ta yin azumin watan Ramadan. Shin ramuwa za ta yi ko za ta iya ciyarwa?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mace ce aka yi mata aiki (operation) a wuya, sai likita ya hana ta yin azumin watan Ramadan. Shin ramuwa za ta yi ko za ta iya ciyarwa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Ya zama wajibi a kanta, ta rama adadin kwanakin da ta sha azumi a cikin su.

    Allah Ta’ala Ya ce: “Duk wanda ya kasance mara lafiya ko matafiyi daga cikin ku, to ya rama a wasu kwanaki na daban”. Suratul Bakara aya ta 185.

    Kuma wannan ta sha azumi ne sanadiyar rashin lafiya, don haka ramuwa za ta yi.

     Allahu Ta’ala.

    AMSAWA: Sheikh Salih Bn Fauzan, Rahimahullah

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GhLY39kRlZEIdcZUmGchEm

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ************************************** 

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.