Ticker

Matan Aure Da 'Yan Mata

Da yawa 'yan mata da matan aure na halakar da kansu, suna zama mushrikai ta hanyar bin malamai masu yi musu sihiri da manufar taimako.

Mata na zuwa gurin malamai domin neman mallake miji ko uwar miji ko ɗauke hankalin mijinsu daga kan abokiyar zamanta dadai sauransu, sai dai kuma shi sihiri kafurci ne.

Waɗannan da kuke ganinsu kamar malamai sun tara Alƙur'anai ga manyar carbi da yawansu ga tarin ƙasa suna duba a kanta suɗin ba malamai ba ne bokaye ne.

Da yawan 'yan mata suna rasa imaninsu, suna shirka ta dalilin zuwa gurin malamai da niyyar meman taimako a kan wani saurayi daga ƙarshe sai ki zama mushrika baki sani ba.

Duk malamin da kikaje gurinsa dan neman taimako a kan mijinki ko saurayinki ya ce miki za ai miki aiki to boka ne, ki tashi ki bashi guri.

Domin babu wani aiki da zai miki daya wuce ya baki rubutu ko wani garin magani ko laya ko ya sa kiyi yanka daga nan kuma sai ki zama mushtika, da ke da shi duk ku shiga wuta.

 Duk malamin da ki kaji ya ce miki za ai miki addu'a amma da sharaɗi, za'ayi yanka, to boka ne, kitashi ki bashi guri, babu wata addu'a da take da sharaɗi sai anmata yanka sannan ALLAH zai karɓa.

Duk malamin da ki kaje gurinsa neman shawara a kan mijinki ya ce to ki kawo kuɗi kaza ko za ki biya kuɗi kaza to ba malamin ALLAH ba ne ki tashi ki bashi guri, ɗan damfara ne.

 

 Malaman sunnah ba sa karɓar kuɗin kowa, saidai su ɗoraki a kan hanyar da zakibi ki samo kan mijinki bisa hanyar koyarwar Manzon ALLAH {s.a.w}, ki sami lada kuma ki sami aljanah kuma ku zauna lafiya da mijinki.

Babu wata addu'a da take da sharaɗin sai an yi yanka, shi yanka idan kina so, bayan kin roƙi ALLAH da kanki a kan wata buƙata taki ko a kan mijin naki, koma wacce irin bukata ce, to idan kina da halin da za ki iya yanka duk abin da ALLAH ya azurtaki da shi na halal sai ki yanka.

Sannan ki dafa abinki ki ci a cikinki yaranki ma suci, ki aikawa maƙobta suma da niyyar ALLAH ya biya miki dukkan buƙatunki, wannan kaɗai ya isar miki a gurin ALLAH {S.W.T}.

Amma kada ki yarda wani malami ya ce a yi yanka kuma ki yarda, amma a kan kanki ya halatta kiyi babu wanda ya saki ke kika ga dama kikayi a binki don ALLAH.

Saboda haka ki dafa kowa ya ci da mijinki da 'ya'yanki suci su yi farin ciki ALLAH zai biya miki buƙatarki saboda dalilin farin cikin da kika saka mijinki da yaranki.

Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

Sadakar da tafi falala ita ce sadakar da aka bada ita ga ɗan uwa tana da lada biyu, ga ladan sadaka ga ladan zumunci.

Sannan ki tashi cikin dare ki kyautata alwala, kiyi sallah raka'a biyu ki roƙi ALLAH dukkan buƙatunki, musamman a cikin sujadarki ta sallah, sannan ki yanka duk abin da ALLAH ya hore miki, ki dafa ku ci keda mijinki da 'ya'yanki da niyyar sadaka.

Ko kuma ki sayi alawa ki rabawa yara sadaka don neman yayewar dukkan damuwarki insha ALLAHU TA'ALAH za ki sami biyan buƙatarki daga ALLAH amma basai kinje wani malami yana cinye miki kuɗi kuma ya jefaki ga aikata shirka ba.

Sannan ya zo cewa duk wanda ya karanta LA'ILAHA ILLAH ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ-ZALIMIN sau 40 to ALLAH zai yaye miki dukkan damuwarki, duk sanda wani abu ya dameki kawai ki zauna ki karanta ta ki miƙa al'amarinki wa ALLAH zakiga biyan buƙata.

Don haka yaku mata ku ji tsoron ALLAH ku kiya yi bin malaman tsubbu, malaman-nan ba malamai ba ne bokaye ne, kawai neman kuɗi sukeyi da ayoyin ALLAH.

Da yawansu sun kafurce, za su iya aikata komai a kan kuɗi, wasu daga cikinsu suna neman matan mutane suce sai ya kwanta da ke sannan za ki sami biyan buƙata, ko kuma ya yi rubutu a jikin azzakarinsa ya kwanta da ke wannan ai ba ƙaramin kafurci ba ne.

 

 Akwai matan da sunje gurin irin waɗannan mutanen, sun san komai, sun san yadda malaman suke, basu da kunya ko kaɗan, babu tsoron ALLAH a tattare dasu, ko mutum kike so a kashe miki zai iya kashewa a kan kuɗi.

Akwai masu luwaɗi da maza, idan namiji yaje neman taimako sai suce sai an yi luwadi da shi sannan zai sami biyan buƙata.

Wasu kuma sai suce suje su rinƙa neman matansu ta dubura, ba ta farji ba, wannan shi ma umarnin aljanu ne, kuma ALLAH ya tsinewa wanda ya yi jima'i da matarsa ta dubura da wanda ya kwant da matarsa tana haila.

Don haka ku rinƙa neman shawara gurin malaman sunnah su sanar daku hanyoyin da zakubi, ku sami mallakar mazajenku cikin sauƙi ta hanyar neman yardar ALLAH, kuma ba tareda kin kashe ko sisi ba.

 Ku sani waɗannan malaman da yawansu 'yan damfara ne, ku kula sosai, kada su damfare muku imaninku, su kuma damfare muku kuɗa-ɗenku.

Kuma ki je ki yi wa mijin naki sihiri idan ALLAH ya sa mai kula da sallah ne a kan lokacinta wani da ya yi alwala nan take sai sihirin ya rage ƙarfi koma ya karye.

Idan kuwa ya yi sallah sihirin ya karye, haka dai zakita yawo kiyita bin bokaye, kinayi yana karyewa harsai kin mutu kina aikata shirka, kuma ki je ki shiga wuta.

Wasu kuwa suna zuwa sunawa abokan zamansu (kishiya) sihiri saboda mijinsu ya daina kwana ɗakin kishiyarta, ko kuma ya daina jin daɗin kwanciya da ita, ko kuma ya tsaneta ma gaba ɗaya.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments