Matsalar Jinkirin Aure Ta Dalilin Shafar Aljanu

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum wa,rahmatullah. Mlm nidalibar kuce a group Hausa Islamic Pictures nakaranta Faɗakarwa nan ta jinkirin aure Mlm kamar muda Allah ya sa muka samu jinkirin aure ta dalilin aljanu waca shawara za ka bamu saboda mukaucewa fadawa shirka wajan neman Magani wlh mlm da irin mu da yawa a Group dinku na matane. Dan Allah Mlm ina so kayiman Faɗakarwa a kan yanda za mu samu solution ba tare da mun kauce hanya ba wlh mlm matsalar tana damuna gagore Goren yan'uwa da yan unguwa kuma muma bamu da wan buri feyada muganmu adakin mijin mu amma duk Wanda ya zo ba zai dawoba. Dan Allahah Mlm kai mana karatu a kan wannan matsalar agroup Allah ubangiji yasaka muku da alkairi abun da kuke mana👏

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Waalaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

    Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, tsira da amincinsa su ƙara tabbata ga annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallama, bayan haka:

    "Haƙiƙa mutane da yawa suna fama da irin wannan matsalar, wasu daga cikin mata wasu kuma daga cikin maza, amma hakan ya fi kasancewa daga mata, wanda kuma hakan baya rasa nasaba da waɗansu abubuwa na musamman da matan ke aikatawa sai aljanun su sami damar shiga jikinsu harma su aure su kuma su hana su auren mutane yan'uwansu"

    Zaka sami mace ta daɗe a gidan iyayenta ba ta yi aure ba, wata kuma ta yi auren amma ya mutu duk ta dalilin wannan matsalar ta aljanun, wani lokaci sukan shiga jikin mace don kawai ta burge su, wasu kuma don kawai mugunta, wasu kuma sukan shiga jikin mace idan ta aikata waɗannan abubuwan:

    👉Yawan bayyanar da tsaraici.

    👉Yawan zubar da ruwan zafi musamman a ban-ɗaki ko makwararar ruwan kwata.

    👉Yawan sauraren kaɗe-kaɗe da ƙaurace wa Alƙur'ani.

    👉Rashin nutsuwa da kuma rashin kamun kai.

    👉Yawan barin gashin kai a buɗe.

    "Haƙiƙa waɗannan kaɗan ne daga cikin dalilan da suke sawa aljanu su afkawa bil-adama su aure shi ko su aure ta su kuma hana ta auren jinsin mutum"

    "To akwai magunguna na musamman da musulunci ya tana da wanda ba sa kaiwa izuwa ga shirka, musamman irin karanta ayoyin alƙur'ani, da kuma wasu addu'oin da suka zo a ingantaccen hadisan Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama"

    "Yawan karanta alƙur'ani mai girma yakan kori aljanu daga cikin gidan mutum, musamman idan yana yawan yin ta'ammuli da Suratul-Baƙarah, haƙiƙa yawaita karanta ta zai kore aljanu daga cikin gidajenku harma daga jikin ku matuƙar kun bayar da cikakken yaƙini a bisa hakan"

    "Kada ku yarda a ce sai kunyi yanka sannan aljanu za su fita daga jikin marasa lafiyan ku, wannan yana bayuwa izuwa ga shirka, sannan kuma kada ku yarda a ce sai kun ɗaura laya sannan aljanu za su fita daga jikin ku, wannan shi ma yana bayuwa zuwa ga shirka, SubhanAllah"

    "Matuƙar kuna son ƙauracewa shirka da Allah a wajen nemawa marasa lafiyanku maganin aljanu, to haƙiƙa sai kun gujewa waɗannan abubuwan masu zuwa:

    👉Yanka domin wanin Allah.

    👉Ɗaura guru ko laya.

    👉Binne wani abu a ƙasa.

    👉Rataya wani abu a ƙofar gida.

    👉Nesantar zuwa gurin bokaye.

    Ya ubangiji! Waɗanda suke fama da irin wannan cuta/rashin lafiyar aljanu, Ya Allah ka warkar dasu, sannan kuma ka basu abokanan aure nagari, ka basu haƙuri da ladan jinkirin da suka samu na wannan cuta, kasa hakan ya zamto silar shigar su aljannah, Ameen.

    WALLAHU A’ALAM

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/F1YV6JhrD89EfJddPLvƘ32

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.