Mene ne hukuncin haɗiye yawu ga mai azumi?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam. Mene ne hukuncin hadiye yawu, ga mai azumi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Yawu baya cutar da azumi, don haka in aka hadiye shi babu komai, kamar yadda idan aka tofar da shi babu komai. Amma kaki da ke fitowa daga ƙirji ko daga hanci, wanda larabawa ke kira (nukhamah), ko kuma (nukha'ah) wanda shi kuma shi ne kaki mai kauri da ke fitowa daga ƙirji ko kuma daga kai, irin Waɗannan wajibi ne ga mutum namiji ko mace tofar da shi, da fitar da shi, da rashin hadiye shi.

    Yayin da shi kuma yawu na al'ada babu matsala akansa, kuma baya cutar da mai azumi; namiji ne ko mace.

    MAJMU'U FATAWA WA MAƘAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 313).

    ALLAH NE MAFI SANI.

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.