Mene Ne Khul'i A Musulunci?

     Wannan É—aya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waÉ—anda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta Æ™arin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    Ma'anar Khul'i shi ne mace ta fanshi kanta daga gurin mijinta, ta ba shi sadakinsa da ya biya a lokacin da ya aure ta.

     Kamar yadda hakan ya zo a hadisi wanda hakan ya taÉ“a faruwa a tsakanin É—aya daga cikin Sahababan Manzon ALLAH {s.a.w} da matarsa.

     Ya halatta a musulunci mace ta biya mijinta sadakinsa daya ba ta a lokacin daya aureta idan har bazata iya zama da shi ba, ko ba ta sonshi, ko yana mata wasu abubuwa da bataso anyi sulhun anyi sulhu amma bai daina ba, to ya halatta ta yi masa Khul'i kamar yadda ya zo a cikin Suratul Bakarah ayata 229.

     Sannan khul'i yana daukar hukuncin saki É—aya ne tak, sannan kuma idan anyishi ba'ayin kome sai dai tsohon mijin nata ya sake biyan sabon sadaki sannan sai a É—aura musu sabon aure.

    ALLAH shi ne mafi sani.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki É—ayanmu Ameen.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.