Mene ne matsayin mutumin da ya yi zina a watan Ramadan bayan an sha ruwa?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne matsayin mutumin da ya yi zina a watan ramadan bayan an sha ruwa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

    Zina dai haramun ne, kuma zunubi daga cikin manyan zunubbai, mazinaci ɗan wuta ne, hukuncinsa ya bar zina kuma ya tuba zuwa ga Allah. Kar ya kuskura ya mutu a matsayin mazinace.

    Zina Lafi ne mai girma, Allah Ya ce “ Kar ku kusanci Zina, domin ita Alfasha ne kuma mummunar tafarki ne” (Suratul Isra’i Aya ta 32).

    Bukhari da Muslim sun ruwato ce annabin tsira (SAW) ya ce: Mazinace bai da imani a lokacin da yake zina. Idan shari’a ta kamashi da laifin zina, to, hukuncin sa shi ne a yi masa BULALA ƊARI, IN BAI TAƁA AURE BA KO A JEFE SA IN YA TAƁA AURE (suratun- Nur aya ta 2). Amma in Allah ya rufama sa asiri, to, ya yi saurin tuba ga Allah.

    Babu shakka a cikin girma da Alfarman watan Ramadan, watane da ake nisantan muyagun laifuka manya da kanana, kuma ake rige-rige cikin ayyukan kwarai, irin tsayuwar dare, sadaka, ciyarwa.

    Amma ka ga zina a cikin Ramadana tafi tsananin zunubi da girman ukuba fiye da zina a cikin watan da ba shi ba, don zunubin saɓo yana kara girma da muni idan aka aikata shi a wani wuri ko lokaci na musamman. Kamar yadda aikin kwarai yake kara lada da daraja a lokuta da gurare na musamman.

    Wajibi ne ga wanda ya fada cikin wannan hadari ya yi gaggawan tuba, ya yawaita Istigifari, ya yawaita aiyukan alhairi, domin kyawawan aiyuka suna kankari munana, kuma mai yawan tuba kamar mara zunubi ne. Allah mai yawan gafara ne kuma mai karban tuba.

    WALLAHU A'ALAM

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/ECƘsg2ycfS0FUI3fHfIdjƙ

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.